Abu bakwai da Muhammadu Sanusi II ya faɗa lokacin karɓar takardar mulki

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Asalin hoton, KANO STATE GOVT

Bayanan hoto, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

A ranar Juma'a 24 ga watan Mayu, 2024 Sarki Muhammdu Sanusi II ya karɓi takardar kama aiki a matsayin sarkin Kano na 16.

Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ne ya miƙa masa takardar a gidan gwamnatin jihar, lokacin wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar.

Sarkin ya koma kan karaga ne bayan soke dokar masarautun Kano ta 2019, wadda ta samar da masarautu biyar.

A ranar 9 ga watan Maris ne aka sauke Muhammadu Sanusi II daga sarautar sarkin Kano na 14 bayan gwamnati ta zarge shi almundahana da kuɗin masarauta.

Bayan sauke shi daga kan muƙamin an kai shi ƙauyen Loko da ke jihar Nasarawa a yankin tsakiyar Najeriya.

Haka nan an zarge shi da rashin biyayya ga gwamnati ta hanyar ƙin halartar tarukan da gwamna ya kira.

Sai dai dokar masarautar Kano ta 2024, wadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya wa hannu a ranar Alhamis ta rushe masarautu da sarakuna biyar da dokar 2019 ta tanada.

Sannan dokar ta mayar da Muhammdu Sanusi II kan karaga a matsayin sarki na 16.

Ga wasu abubuwan da sarkin ya faɗa a lokacin jawabinsa na karɓar aiki:

'Shekara 10 tsakanin kama aikina na farko da na biyu'

A farkon jawabinsa, Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa ya koma kan karagar sarautar Kano ne bayan shekara goma da karɓar takardar kama aikin mulkin masarautar a karon farko.

Ya ce "A shekara ta 2014, a nan wajen, mai girma gwamnan na wancan lokacin, Rabiu Musa Kwankwaso ya miƙa min takardar naɗi a matsayin sarki.

"Yau bayan shekara 10, kwanaki ne suka rage ta cika, Allah ya ƙaddara mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf shi ma zai ba ni wannan takardar".

A ranar 8 ga watan Yuni, 2014 ne aka naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 14 a karon farko.

'Ana lalata tsarin sarauta a arewacin Najeriya'

...

Asalin hoton, KANO STATE GOVERNMENT

Sarkin ya yi tsokaci kan cewa siyasa ta shiga cikin harkar sarauta, kuma ƴan siyasa na rarraba masarautu yadda suke so.

Ya ce "Mun gani a jihohi daban-daban, ƙasashe na manyan sarakuna ƴan siyasa sun zo sun kacaccala su".

"Wannan abin da aka ɗauko a Kano, da an bar shi ya ɗore, wata rana sai mun ji ana sarkin Kumbotso, sarkin Ƙunchi, sarkin Fagge, sai an yi sarakuna 44".

Ya ƙara da cewa "abin da gwamnati ta yi toshe hanya ce ga ɓarnar da ta fi wannan (rarraba masarauta)".

Shugabanni sun so su raba al'ummar Kano

Sarkin na Kano ya kuma yi tsokaci kan haɗin kan al'ummar jihar, inda ya bayyana cewa kan al'ummar a haɗe yake.

Ya ce: "Al'ummar Kano kanta a haɗe yake, babu wani ɓangare na al'ummar Kano da yake faɗa da wani ɓangare".

Ya ƙara da cewa "Allah ne ya haɗa mu da shugabanni waɗanda suka nemi su raba kanmu, kuma Allah ya kawo mana shugabanni da suka haɗa kan al'umma".

Duk zuri'ar Dabo na da hakki kan sarautar Kano

Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa gidan sarautar Kano guda ɗaya ne, tare da kore batutuwan da ke nuna cewa akwai gidajen sarauta daban-daban a masarautar ta Kano.

A cewarsa: "Sarautar Kano gidan sarki Ibrahim Dabo ne, babu wani wanda yake da gida, babu wani wanda ya yi yaƙi ya kafa Kano bayan Ibrahim Dabo.

"Duk wanda ya hau (sarauta) haifar sa aka yi a gidan ya gada kuma duk zuri'ar Dabo suna da hakki wanda yake daidai ne da kowanne".

'Addu'ar mutane ce ta yi tasiri'

Wani batu da sarkin na Kano ya taɓo kuma shi ne yadda a cewar sa 'addu'ar mutane ta yi tasiri' wajen komowarsa kan karaga.

Ya ce "Wannan abin, babu abin da ya yi shi sai addu'a, addu'ar mutanen Kano, addu'ar mutanen Najeriya, addu'ar mutane ko ina a duniya, Nijar, Kamaru, Senegal...babu inda al'umma ba su yi addu'a Allah Ya dawo da Kano yadda take ba".

'Abba ka cika gwarzo'

...

Asalin hoton, KANO STATE GOVERNMENT

A lokacin da yake gab da kammala jawabin nasa, Muhammadu Sanusi II ya yaba wa gwamnan jihar da kuma ƴan majalisar dokokin jihar waɗanda ya ce sun yi ƙoƙari wajen gyara dokar da ta sake haɗa masarautar Kano zuwa ɗaya.

Ya ce "Yau muna zaune sai na ji wata gaskiya, an ce Abba ka cika Gwarzo.

"Idan har a duniya...mutumin da zai yi ɓarna, mutumin da zai lalata abu mai kyau zai bugi ƙirjinsa ya yi da'awar shi gwarzo ne, wanda ya zo ya warware ɓarna, ya gyara, shi ya fi cancanta da a ce wa gwarzo".

'...darajarsu ba ta kai a ɗaga ido a kalle su ba'

A ƙarshen jawabin nasa ya yi fatan cewa darasin da ya samu a cikin 'waɗannan' shekaru za su amfane shi.

Ya ce: "iyakacin abin da mutum zai iya maka shi ne ya yi abin da Allah ya yi maka, ba zai yi maka abin da Allah bai ƙaddara maka ba".

"Sai mu fuskanci gaba, abu ne ya faru maras daɗi, a wuce shi kamar ba a yi shi ba saboda waɗanda suka yi...darajarsu ba ta kai a ɗaga ido a kalle su ba, balle a yi magana a kansu, kuma ba za a yi ba.

Wanna ne karo na biyu a tarihin masarautar Kano na baya-bayan nan da aka sauke sarki sannan ya sake komawa kan karaga.

A shekarar 1652 an kori sarkin Kano Muhammad Kukuna tare da naɗa sarki Soyaki.

Amma Kukuna ya sake komawa a kan karagar mulkin bayan samun galaba a kan sarki Soyaki, inda ya yi mulki har zuwa shekara ta 1660.