Sanata Natasha ta kai ƙarar Akpabio zuwa Majalisar Ɗinkin Duniya

Lokacin karatu: Minti 4

Sanata Natasha Akpoti-Uguaghan ta yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta hukunta majalisar dattawan Najeriya game da dakatarwar da aka yi mata na tsawon wata shida.

Majalisar dattawan ta dakatar da sanata Natasha ne kan zargin yunurin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalisar, Godswill Akpabio.

Da take magana a taron mata na ƴanmajalisar ƙasashen duniya na Majalisar Ɗinkin Duniya da aka yi a birnin New York, Akpoti-Uduaghan ta ce tana fuskantar "tsangwama a siyasa da kuma barazana" saboda ta nemi a yi bincike na gaskiya kan zarge-zargen cin zarafi ta hanyar lalata da ta yi wa Akpabio.

Ta ƙara da cewa ta yi kiran ne don "kada duniya ta zura ido a yi shiru yayin da dimokraɗiyya da haƙƙoƙin mata ke cikin tasku a Najeriya".

Tun farko dai Sanata Natasha ta fito ta bayyana zarge-zargen ne bayan da a wani zaman majalisa aka ga yadda take ɗaga murya tana nuna fushinta game da yadda aka sauya mata wajen zama a majalisar ba tare da wani dalili ba, a cewarta.

A ranar 6 ga watan Maris ne aka dakatar da ita bisa zargin "saɓa dokokin majalisar dattawa" da kuma "take ƙa'idojin majalisar dattawa na 2023 da aka yi wa gyaran fuska", abubuwan da aka bayyana a matsayin zubar wa da shugabancin majalisar da gaba ɗaya majalisar ƙima".

A yanzu dai an garƙame ofishinta an kuma tsayar da albashinta da alawus-alawus ɗin da take samu tare da janye mata jami'an da ke ba ta tsaro sannan kuma an haramta mana bayyana kanta a matsayin sanata ga ƴanjarida.

Ana sa ran ƴarmajalisar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a yankin Arewa ta Tsakiya za ta miƙa takardar neman yafiya kafin ta koma majalisar - wani abu da ta ce ba za ta yi ba.

An dai gudanar da zanga-zanga a Abuja, babban birnin Najeriya - wasu na nuna goyon baya ga Sanata Akpoti-Uduaghan, wasu kuma na nuna goyon baya ga shugaban Majalisar Dattawa Akpabio.

An gudanar da zanga-zanga ta baya-bayan nan a ranar Talata inda aka ga wasu matasa daga wata jam'iyyar hamayya tare da ƴarmajalisar duk da kasancewarta ba ƴar jam'iyyarsu ba.

Mene ne martanin majalisar?

Bayan ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta gabatar, Shugabar ƙungiyar ƴanmajalisar ƙasashen duniya, IPU, Tulia Ackson, ta mayar da martani inda ta ce za su ɗauki matakan da suka kamata ne bayan sun saurari ɓangarorin biyu game dakatarwar da aka yi wa ƴarmajalisar.

A cewarta, "Ya ku abokan aikina, kafin na rufe taron, akwai wani batu da ya taso a taron farko da muka yi da safe, abokiyar aikinmu daga Najeriya, Sanata Natasha ce ta taso da batun. Dukkanmu mun ji abin da ta ce, mun ji kokenta amma kasancewar mun ji daga ɓangare ɗaya ne, IPU a matsayin ƙungiya, za mu bai wa ɗaya ɓangaren dama. Za mu ɗauki matakan da suka dace."

Mece ce Ƙungiyar ƴanmajalisar ƙasashen duniya ta IPU?

Wannan ƙungiya dai an kafa ta ne tun shekarar 1889 inda ta soma a matsayin ƙaramar ƙungiya domin bunƙasa zaman lafiya ta hanyar amfani da diflomasiyya da tattaunawa na majalisa wanda kuma a yanzu take da mambobi 181 da wasu mambobi 15 marasa cikakken iko.

Ƙungiyar IPU na bai wa majalisa da ƴanmajalisa dama ta samar da zaman lafiya da bunƙasa dimokraɗiyya da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a sassan duniya.

Burin ƙungiyar da ke da mazauni a Geneva na ƙasar Switzerland, shi ne yin aiki tare da majalisu da ƴanmajalisa wajen biyan bukatun al'umma.

Tana kuma da ofisoshi a New York da ke Amurka da Vienna a Austriya.

Ayyukan ƙungiyar IPU

Ɗaya daga cikin muhimman ayyukan IPU shi ne bai wa ƴanmajalisar ƙasashen duniya kariya da kuma tabbatar da haƙƙoƙinsu.

Kungiyar ta kafa kwamiti kan kare haƙƙoƙin ƴanmajalisa da ke nazari tare da bincike kan ƙorafe-ƙorafe da suka shafi wannan ɓangare.

IPU tana amfani da wata dabara wajen kare haƙƙoƙin ƴanmajalisa a faɗin duniya waɗanda ke fuskantar cin zarafi ko barazanar kisa ko tsangwama saboda kawai suna gudanar da ayyukansu.

Tana kuma samar wa ƴanmajalisa bayanai da ilimi tare da ba su horo kan yadda za su kare haƙƙoƙin mutanen da suke wakilta musamman mata da yara da tsiraru.

Galibi IPU tana bayyana matsayarta game da ƙararrakin da suka shafi take haƙƙoƙin bil'adama ga duniya. Ana gabatar da matakan da aka ɗauka a tarukan kwamitin da ake yi sau biyu a shekara ga hukumar gudanarwar majalisar domin amincewar jama'a.

Zuwa yanzu dai kwamitin ƙungiyar IPU kan kare haƙƙoƙin ƴanmajalisa ya saurari ƙorafe-ƙorafe 943 a ƙoƙarinsa na kare haƙƙoƙin yanmajalisa a faɗin duniya sai dai abin da ba a sani ba shi ne ko ƙorafin da Natasha Akpoti ta gabatar a baya-bayan nan zai shiga jerin ƙararrakin da za a yi duba a kai.

Abin da ya janyo tankiya tsakanin Natasha da Akpabio

A ranar 20 ga watan Fabrairu ne dai tankiya ta ɓarke a zauren majalisar dattawan tsakanin shugaban majalisar, Godswill Akpabio da sanata Natasha Uduaghan da ke wakiltar tsakiyar jihar Kogi.

Rikicin ya samo asali ne lokacin da mai tsawatarwa na majalisar, sanata Mohammed Munguno ya shaida wa ƴan majalisar cewa sanata Natasha ta ƙi amince wa ta koma sabuwar kujerar da aka ware mata.

Al'amarin dai ya janyo har shugaban majalisar, Akpabio ya umarci ɗaya daga cikin masu yi wa sandan majalisar hidima da ta fitar da sanata Natasha daga zauren majalisar.

Hakan ne ya janyo ƙungiyoyi da mutane da dama yin kiraye-kirayen a yi bincike wani abu da ya sa majalisar dattawan ta nemi da Natasha ta je ta bayar da bahasi.