Yadda aka kashe limamin Musulunci 'ɗan luwaɗi na farko a duniya'

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Todah Opeyemi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
Muhsin Hendricks, wanda ake ganin shi ne limamin Musulunci na farko da ya fito ya bayyana kansa a matsayin ɗan luwaɗi, an kashe shi ta hanyar harbi a Afirka ta Kudu.
Mutumin ɗan shekara 57 ya kasance jagoran wani masallaci a birnin Cape Town, inda ya zamo tamkar mafaka ga masu alaƙar jinsi ɗaya da kuma wasu Musulmai da ke ganin ana tauye su.
An kashe shi ne a ranar Asabar yayin da wasu mutane suka yi wa motar da yake ciki kwantar-ɓauna a kusa da birnin Gqeberha da ke kudancin ƙasar Afirka ta Kudu.
"Wasu mutum biyu ne da suka rufe fuskokinsu suka sauka daga cikin mota inda suka buɗe wuta kan motar da yake ciki," in ji rahoton ƴansanda.
Kisan Hendricks ya girgiza ƴan ƙungiyar LGBTQ+ da ma wasu da dama, lamarin da ya janyo sharhi daban-daban a faɗin duniya.
Julia Ehrt, shugabar ƙungiyar ƴan luwaɗi da maɗigo da waɗanda suka sauya jinsinsu na asali, da sauransu, ta duniya (Ilga), ta buƙaci hukumomi su yi kyakkyawan bincike kan lamarin wanda ake yi wa kallon "aikin nuna ƙyama".
"Ya tallafa tare da bai wa mutane da dama shawarwari a Afirka ta Kudu da ma duniya domin nuna musu hanyar da za su yi rayuwarsu duk da addinin da suke bi, kuma rayuwarsa shaida ce ta natuswar da haɗin kai zai iya samarwa a rayuwar al'umma," in ji ta.
Rahotanni sun bayyana cewa an kashe Hendricks ne bayan ya kammala ɗaura auren wasu ƴan luwaɗi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Labarin kisan nasa ya bazu ne bayan ɓullar bidiyon na yadda aka kai masa harin a shafukan sada zumunta.
Bidiyon ya nuna yadda wata mota ta sha gaban motar da Hendricks ke ciki. Ƴansanda sun ce a lokacin malamin na zaune ne a bayan motar.
Bidiyon kyamarar tsaro ta CCTV ta nuna yadda wani mutum ya fito daga cikin mota ya garzaya zuwa wurin motar da Hendricks ke ciki sannan ya buɗe wuta a ɓangaren kujerar baya.
Gidauniyar Al-Ghurbaah, wadda Hendricks ya kafa, wadda kuma take tafiyar da lamurran masallacin da ake kira Masjidul Ghurbah da ke yankin Wynberg da ke kusa da birnin Cape Town ta tabbatar da kisan malamin a wani abu da ta bayyana a matsayin 'kisan cune'.
Sai dai shugaban kwamitin gudanarwar gidauniyar, Abdulmugheeth Peterson, a cikin zauren WhatsApp na ƙungiyar ya buƙaci mabiya malamin su yi haƙuri, sannan ya jaddada buƙatar ganin an martaba sirrin iyalin marigayin.
Ayyukan Hendricks sun yi hannun riga da koyarwar musulunci da aka saba da su, inda ya riƙa hanƙoron ganin addini ya karɓi mutane daban-daban.
Kundin tsarin mulkin Afirka ta kudu bayan mulkin wariyar launin fata ne na farko a duniya da ya bayar da kariya ga mutane daga nuna bambanci saboda ɗabi'arsu ta luwaɗi, kuma a shekarar 2006, su ka zama ƙasa ta farko a Nahiyar Afirka da ta halasta auren jinsi.
Amma duk da ƙaruwar da ƴan ƙungiyar LGBT ke yi a ƙasar, har yanzu ƴan luwaɗi na fuskantar wariya da kuma cin zarafi.
Kasar kuma na da ɗaya daga cikin adadi mafi yawa na kisa a duniya.
Hendricks ya bayyana kansa a matsayin ɗan luwaɗi a shekarar 1996, lamarin da ya girgiza alummar musulman Cape Town da sauran wurare.
A wannan shekarar, ya kafa ƙungiyar '' The Inner Circle'', wata ƙungiya da ke bayar da goyon baya ga Musulmai ƴan luwaɗi da ke neman samun daidaito tsakanin addininsu da ɗabi'arsu ta luwaɗi, kafin daga bisani ya kafa massalacin Masjidul Ghurbaah.
A kan shi akayi wani gajeren shiri a shekarar 2022 mai suna The Radical, wanda a ciki ya yi magana kan barazanar da ya ke fuskanta : '' Buƙatar kasancewa yadda na ke ya fi karfin tsoron mutuwa.''
A lokuta da dama Hendricks na magana kan muhimmancin tattaunawa tsakanin addinai da kuma buƙatar magance matsalolin lafiyar kwakwalwa da kuma damuwa da ƴan ƙungiyar LGBTQ+ ke fuskanta a cikin allummar addinai.
A wani taron duniya na Ilga a Cape Town a bara, ya ce : ''Abu mai muhimmanci ne mu daina kallon addini a matsayin abokin gaba.''
Reverend Jide Macaulay, sannanen ɗa luwaɗi kuma malamin addinin kirista, ya bayyana mutuwar Hendricks a matsayin mai '' matuƙar karya zuciya''
Mai fafutukar kare haƙƙin ƴan ƙungiyar LGBT ɗan Birtaniya ɗan asalin Najeriya da ke jagoratar House of Rainbow, wata ƙungiya da ke baiwa ƴan luwaɗi goyon baya a Najeriya inda aka haramta tarayya tsakanin jinsi, ya aika saƙon jaje game da jarumtakar Hendricks.
Sadiq Lawal, musulmi ɗan luwaɗi da ke zama a Najeriya ya shaidawa BBC cewa Hendricks ya yi tasiri sosai a rayuwarsa saboda ya mayar da 'abin da bazai yiwu ba ya yiwu'' ta hanyar faɗin kalaman : '' Ni limami ne ɗan luwaɗi.''
Shi abin koyo ne ga Musulmai ƴan luwaɗi a Afirka musamman a Najeriya saboda tsattsaurar ra'ayin addini'' in ji shi.
'' Har yanzu a gigice na ke kuma na kaɗu sosai.''











