Mutumin da ya kashe tarin baƙaƙen fata a Afirka ta Kudu ya mutu

Ɗaya daga cikin fitattun waɗanda suka kashe mutane da yawa a Afirka ta Kudu ya mutu.
Louis van Schoor ya hallaka aƙalla bakar fata 39 manya maza da yara a tsakanin shekara ta 1986 da 1989.
Jerin kisan da Louis van Schoor, wanda aka fi sani da laƙabin, The Apartheid Killer, ya yi sun kasance ne a birnin East London na kasar ta Afirka ta Kudu, inda a lokacin yake aiki a matsayin mai gadi wanda ba na hukuma ko gwamnati ba.
A 1991 an kama Van Choor, aka gurfanar da shi gaban shari'a, inda aka same shi da laifin kisan kai bakwai kawai, aka kuma ɗaure shi, to amma daga baya an sake shi bisa dalilai na nuna halayya ta gari, bayan shekara 12 a gidan kaso.
Har yanzu kisa aƙalla 32 da ya yi a wajen hukumomin ‘yansanda na ƙasar ya yi su ne bisa dacewa da doka.
To amma wani rahoto da BBC ta yi ya nuna tababa sosai a kan abin da hukumomin ‘yansandan suka ayyana a matsayin dacewa na waɗannan kashe-kashe da ya yi ta hanyar harbe mutanen.
Rahoton na BBC ya ƙunshi doguwar tattaunawa da aka yi da shi Van Schoor, inda ya bayyana abin da ya yi a matsayin mai ban sha’awa, a wani lokacin kuma yake bayyana abin da farauta, inda kuma ya yi zargi da dama a kan sanya hannun ‘yansanda a abubuwan da ya yi a shekarun na 1989.
Haka kuma BBC ta yi nazarin takardun hukuma da dama da aka ma manta da su da daɗewa, waɗanda suka haɗa da bayanai na shedun mutane da dama da suka tsira daga harbin na Van Schoor, waɗanda suka bayar da bayanai masu tayar da hankali na yadda ya harbe su duk da cewa sun miƙa wuya gareshi
A lokacin rayuwarsa Van Schoor na iƙirarin cewa dukkanin mutanen da ya harbe ko waɗanda ya raunata masu laifi ne da ya kama ƙarara suna aikata laifi.
Ya dai dogara ne wajen aikata ta’asar a kan dokokin lokacin mulkin wariyar launin fata na kasar ta Afirka ta Kudu, inda dokokin suka ba shi damar amfani da makami a kan duk wasu masu kutse.
Van Schoor mai shekara 72, ya kasance a asibiti yana jinyar wani ciwo a ƙafarsa, inda ‘yarsa ta gaya wa BBC cewa ya rasu ne ranar Alhamis.
Mutumin ya mutu ne kasa da mako daya bayan da BBC ta ƙaddamar da bincike a kan abubuwan da ya aikata a baya, binciken da ya bankado, sababbin bayanai kan kashe-kashen mutane da ya yi a karshe-karshen shekarun 1980, wato wajejen shekarun ƙarshe na mulkin wariyar launin fata.
'yar uwar ɗaya daga cikin waɗanda ya harbe, ta gaya wa BBC cewa tana fatan 'yan sanda za su sake buɗe bincike kan abubuwan da Van Schoor ya aikata duk da cewa ya mutu.











