Yadda kisan wata matashiya ya fito da ƙiyayyar da ake nuna wa mata a intanet

Asalin hoton, Getty Images
Kisan wata matashiya ƴar ƙasar Kenya a wani gidan da aka yi haya na gajeren lokaci, ya fusata mutane tare da fito da irin muzgunawa da ƙiyayyar da ake nuna wa mata a shafukan intanet na ƙasar.
An daddatsa gawar matashiyar, aka kuma zuba a cikin wata jakar leda, a cewar wani rahoton ƴansanda da BBC ta gani.
Ƴansanda na ci-gaba da bincike, amma wanda ake zargin ba a san inda yake ba.
Lamarin ya "ɗimautar da kuma fusata" shugaban kungiyar Amnesty International a Kenya, Irungu Houghton.
"Wata matashiya kuma mai shekara 20 da ba za ta kai ga lokacin da za ta kai shekara 40 ba!" In ji shi.
Mako biyu gabannin hakan an kashe wata ƴar ƙwalisa a wani gidan da aka yi haya na gajeren lokaci a birnin Nairobi.
Kashe-kashen da aka fi sani da kisan 'Airbnb: (wani kamfanin Amurka mai bayar da hayan gidaje na gajere da dogon lokaci ta intanet)' a Kenya.
Sai dai kamfanin ya shaida wa BBC ya gudanar da bincike kuma ya gano cewa ba matan ba ne suka karɓi hayar gidajen ta shafinsa na intanet.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Cin zarafi mai nasaba da jinsi wata babbar matsala ce a ƙasar.
A shekarar 2022 an samu akalla kashi 34 cikin dari na mata sun ce sun fuskanci cin zarafi na zahiri, a cewar wani binciken da aka yi na ƙasa.
Kisan baya-bayan nan ya ƙara fito da mummunan bangare na shafukan sada zumunta a ƙasar ta Kenya, wanda ake bayyanawa a matsayin "matattara" inda mafiya yawan tsokacin da ake wallafawa suna ɗora laifin kisan ne a kan matan.
"Matattara" ta haɗa dandalin sada zumunta da ke ɗaukaka maza tare da nuna ƙasƙancin mata.
Wani mutumin Kenya a shafinsa na X, wadda a baya ake kiran shafin Twitter, ya ce: "A haƙiƙanin gaskiya ina ganin babu wata fafutukar da za ta iya kawo ƙarshen kisan da ake yi wa mata."
Ya kara da cewa "ya rage ga matan su zama masu kula da kare kansu," yana mai ikirarin cewa "hakan ne kawai zabin da suke da shi."
Masu fafutuka da dama sun mayar da martani da cewa tsokacin mazan a shafukan intanet ba wani sabon abu ba ne.
A wani mataki na mayar da martani kan kashe-kashen da ake samu, "KU DAINA KISAN MATA" ya zama abun da aka fi magana akai a shafin X a Kenya.
Wata mata a shafin X ta ce: "Abun na bani mamaki ace har yanzu maganar da ake yi ita ce ta abun da mata za su yi, ko wanda bai kamata su yi ba, maimakon a fara mayar da hankali kan maza su daina kisan mata, "abu ne mai sauƙi."
Wata ƴar majalisar dokokin Kenya, Esther Passaris ta shaida wa BBC cewa bata yi mamakin ɗora laifin da ake yi a kan matan da aka kashe ba, a alumma irin ta Kenya da maza ke amfani da karfinsu wajen nuna son kansu, kuma suke kallon mata da ƙasƙanci.
Ta ce a matsayinta na mace, ana mata kallon wulaƙanci, kuma an sha kiranta "karuwa."
Mista Houghton ya gaya wa BBC cewa waɗannan maganganun ba wai ɗaiɗaikun mata kawai ake yi wa ba, abun ya fi ƙarfin hakan domin wata al'ada ce ta nuna wa "mata ƙiyayya".
"Dandalin sada zumunta da saƙon kar- ta-kwana sun zamo mahadar al'umma. Inda ake muhawarori kan batutuwa. Kuma kan al'ummar ƙasar ya rabu kan dalilan da ke janyo cin zarafin da ke da nasaba da jinsi.
"Ga wasu yadda ake ɗora laifin kan waɗanda abin ya shafa, ga wasu kuma yadda ake wa maza kuɗin goro wajen yin tur, na daga cikin abubuwan da ake jayayya a kai". Inji Houghton.
Wani ɗan fafutuka, Onyango Otieno, mai shekara 35 a duniya, wadda ya ƙalubalanci al'adar da ke matsin lamba ga maza su nuna cewa su maza ne idan ba haka ba al'umma ta kalle su a matsayin ragwaye, ya shaida wa BBC cewa maza suna yi wa mata kalamai na ƙasƙanci ne saboda an cire "wani tsani" wanda yasa mata ke neman daidaito da mazan.
Ya ce mazan Kenya sun taso da fahimtar cewa suna sama da mata, amma ƙaruwar kare haƙƙin mata da nuna daidaitonsu ga maza ya sanya wasu mazan na jin cewa an rage musu matsayi ko kuma sun rasa na yi.
"Maza da yawa ba a koya musu yadda za su rayu kafaɗa-da-kafaɗa da mata a matsayin ƴan adam da ke daidai da juna ba," In ji Mista Otieno.
Ya ƙara da cewa maza da yawa sun kasa fuskantar wannan al'ari na zahiri.
"Matattara" ta zamo musu wata hanyar da za su samu fifikon da "aka yi musu alƙawari".
"Duniya ta sauya ta ɓangarori da dama, amma maza ba su sauya ba," yana mai ƙarfafawa.











