Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda zarge-zargen fyaɗe da rashin kula suka dabaibaye masana'antar fim a Indiya
- Marubuci, Geeta Pandey & Meryl Sebastian
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Marubuci, Imran Qureshi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hindi, Bengaluru
- Lokacin karatu: Minti 5
Wani rahoto ya bankaɗo yadda mata ƴan fim ke fuskantar matsala a masana'antar Malayalam, wato ɗaya daga cikin masana'antar fim mafi girma a Indiya.
Binciken da wasu mutane uku suka gudanar na da matuƙar tayar da hankali.
Rahoton mai shafi 290, na ɗauke da bayanan waɗanda lamarin ya shafa da kuma waɗanda suka aikata laifin, koda yake an sakaya sunayensu, inda rahoton ya ce akwai gawurtattun maza waɗanda suke abin da suka ga dama a masana'antar.
"Shi ya sa cin zarafin lalata ya zama ruwan dare ga mata."
Kwamitin da tsohuwar alƙalan alƙalai ta babbar kotun Kerala ta jagoranta, wanda gwamnati ta naɗa tun 2017, ya yi bayanin yanayin da ƴan fim ke samun kansu a lokacin da ake ɗaukar fim.
Akwai rashin banɗakuna da kuma ɗakunan sauya kaya ga taurari masu tasoswa, da kuma rashin ruwa da Abinci, ga rashin biyan su kuɗin aiki da zirga-zirga.
"Babu banɗakuna,saboda haka mata sai dai su je bayan gari ko cikin itatuwa. A lokacin al'adarsu, ba su samaun damar sauya ƙunzugunsu na tsawon lokaci, tare da riƙe fitsari na tsawon lokaci da ke haifar masu da matsalar da har sai sun je asibiti," cewar rahoton.
Rahoton wanda aka gabatar ga gwamnati a watan Disambar 2019, an fitar da shi ne a cikin wannan makon bayan kwashe shekaru biyar ke nan.
An kafa kwamitin binciken ne saboda taƙaddamar da ta kunno kai kan mummunan cin zarafin wata babbar jaruma a masana'antar.
Bhavana Menon, ta jagoranci fim sama da 80 a gabashin Indiya, ta kuma lashe manyan kambun girmamawa, wadda ayarin wasu maza suka ci zarafinta a kan hanyarta daga Thrissur zuwa Kochi a watan Fabrairun 2017.
Jaridu da dama sun yi labarin faruwar lamarin, musamman bayan da aka ambaci sunan ɗaya daga cikin manyan jarumai na masana'antar a matsayin wanda ake zargi, wato Dileep, inda aka kama shi tare da gurfanar da shi gaban kotu, an kuma tuhume shi da laifin haɗin baki.
Sai dai ya musanta zargin, amman an tsare shi gidan gyaran hali na tsawon wata uku kafin daga bisani aka bayar da belin shi tare da ci gaba da sauraron shari'ar a kotu.
A dokar Indiya fitar da sunan wadanda aka ci zarafi ya saɓa ƙa'ida, sai dai tun da farkon an san cewa Menon ce aka ci zarafi. A 2022, ta bayyana kanta ta hanyar saƙon da ta wallafa a shafinta na Instagram da kuma a wata hira da aka yi da ita a BBC.
Bayan wasu ƴan watanni da afka wa Menon, wasu abokan aikinta mata sun kafa wata ƙungiya a masana'antar, inda suka buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki kan faruwar lamarin.
A cikin rahoton, mai shari'a Hema ta ce ƙungiyar ta matan masana'antar sun shaida mata cewa "ana hana su magana saboda ana nuna masu akwai buƙatar a kare ƙimar masana'antar".
Kwamitin ya tattauna da gomman mata da maza, da suka haɗa da jarumai da masu shiryawa da bayar da umarni da masu rubuta labari da masu kwalliya da masu sutura da sauran mutanen da ke cikin masana'antar.
"Mun tattara shaida ta hanyar naɗar bidiyo da muryoyi da kuma sakonnin dandalin WhatsApp."
Rahoton ya bayyana yadda cin zarafi ta hanyar lalata ga mata a masana'antar da mummunan yanayi mai tayar da hankali da ke faruwa kusan kullum kuma ba tare da an yi wani abu ba.
"Wasu maza, jarumai da masu shiryawa da bayar da umarni da masu sayarwa waɗanda suka samu ɗaukaka da kuɗi a masana'antar ne ke juya kowa."
"A bayyane maza ke neman kwanciya da mata babu shakka ko tsoro, lamarin da ya sanya matan ba su da wani zaɓin da ya wuce su amince da buƙatar su, saboda ƙin amincewar na sanyawa a hana su cimma burinsu na zama jarumai."
"Da yawan matan sun fuskanci wani mummunan yanayi mai tayar da hankali da ba su iya bayyana halin da suke ciki ga iyalansu na kusa."
"Yawancin waɗanda kwamitin ya tuntuɓa sun ji tsoron yin magana saboda kada su rasa aikinsu."
"Da farko mun ɗauki fargabar ta su wani iri, amman daga bisani mun fahimci dalilinsu. Mun damu da tsaron lafiyarsu da ta iyalansu.
A cikin rahoton, ƙungiyar matan da ke masana'antar (WCC) ta ce "Mun kwashe shekaru muna faɗin akwai matsaloli, wanda cin zarafin lalata na ɗaya daga cikinsu. Wannan rahoton ya tabbatar da hakan," cewar Beena Paul ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar WCC, kamar yadda ta shaida wa BBC.
"Duk lokacin da muka kawo irin wannan ƙorafin ana ce mana ba mu son zaman lafiya, amman wannan binciken ya ƙara fito da cewa lamarin ya wuce yadda muka ɗauke shi."
Mambobin ƙungiyar matan masana'antar WCC sun ce suna shan wahala tun lokacin da suka nemi samar da yanayin aiki mai kyau a lokacin da ake ɗaukar fim.
"Mutane da dama ba su so muna yin tambayoyi ko bincike, shi ya sa wasu mambobinmu suke shan wahala suke kuma shiga mawuyacin hali," cewar Ms Paul.
Babbar ƙungiyar masana'antar fim ta Malayalam [AMMA] wadda ke da manyan jarumai a cikinta da suka hada da Mohanlal da Mamooty a cikin mabobinta, ta musanta zarge-zargen.
Sakataren ƙungiyar AMMA, Siddique ya musanta batun cewa wasu tsirarun gawurtattun maza ne ke juya masana'antar.
Ya kuma musanta cewa cin zarafin lalata ya zama ruwan dare a masana'antar, inda ya ce yawancin ƙorafin da suke samu shi ne na jinkirin biyan kuɗin aiki ko kuma rashin biyan kuɗin.
Ya kuma ce an inganta yanayin aiki ga mata a cikin shekara biyar da suka gabata ta hanyar samar masu dukkan abubuwan da suke buƙata.
Rahoton ya janyo cece-ku-ce a jihar, inda masu raji da manyan jagororin adawa suka nemi da gwamnati ta ɗauki mataki kan lamarin.
Shugaban gwamnati Pinarayi Vijayan ya ce idan har matan da suka bayar da shaida a gaban kwamitin za su fito su shigar da ƙorafi to lokacin ne gwamnati za ta ɗauki mataki," kan duk wanda ya aikata laifi komai girmansa."
Kotu ta buƙaci gwamnati ta gabatar da rahoton domin duba yiyuwar ɗaukar mataki kan lamarin.
Zarge-zargen cin zarafi ba sabon abu ba ne a masana'antar fim a Indiya, inda ko a 2018, an samu irin haka a masana'antar fim ta Bollywood bayan da jaruma Tanushree Dutta ta zargi jarumi Nana Patekar da nuna wasu ɗabi'u marasa kyau a kan ta a yayin da suke ɗaukar fim a 2008. Zargin da Pateker ya musanta.
Dutta wadda ta ce an hana ta yin aiki, ta bayyana rahoton na Hema da "marar amfani", inda ta ce rahotannin da aka gabatar a baya ba su yi tasiri ba.
Sai dai Parvathy Thiruvothu, ɗaya daga cikin mai faɗa a ji a ƙungiyar WCC ta bayyana rahoton a matsayin gagarumar nasara.
"Rahoton zai taimaka wajen kawo sauye-sauye a masana'antar," cewar Parvathy Thiruvothu.
Jeo Baby, darakta na Great Indian Kitchen, ya shaida wa BBC cewa wannan ne lokacin da ya dace wajen kawo sauye-sauyen da ake buƙata.
Rahoton ya bayar da shawarwari na hanyoyin da za a bi wajen samar da kyakkyawan yanayin aiki ga mata, " Ana fatan masana'antar fim za ta samar da yanayi mai tsafta da iyaye za su iya tura yaransu domin su yi aiki a cikin ta."