Ko kun san yadda aka kashe Sarki Faisal na Saudiyya shekara 50 baya?

    • Marubuci, Louise Hidalgo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5

A ranar 25 ga Maris, 1975 ne aka kashe Sarki Faisal bin Abdulaziz Al Saud na Saudiyya a babban birnin ƙasar, Riyadh. Wani ɗan uwansa ne ya harbe shi.

Ministan mai na ƙasar, Ahmed Zaki Yamani, yana tsaye a gefen sarkin lokacin da aka harbe shi.

A shekara ta 2017, 'yarsa, Dr. Mai Yamani, ta shaida wa BBC cewa:

"Ba zan taɓa mantawa da wannan rana ba. Har yanzu ina jin zafin abin da mahaifina ya gani. Ka yi tunanin mutum yana tsaye kusa da ubangidansa, malaminsa, abokinsa sannan kwatsam aka harbe shi."

An harbi Sarki Faisal sau uku a jere lokacin da ya durƙusa don ya gaishe da ɗan'uwansa.

Mahaifin Dr. Yamani, wanda ya kasance amintaccen ministan sarkin na tsawon shekara 15, yana kusa da shi ne saboda yana masa bayani a lokacin.

Cikin gaggawa aka garzaya da Sarki Faisal - wanda shi ne sarki na uku tun bayan kafuwar masarautar Saudiyya, kuma ɗa na uku ga wanda ya kafa ƙasar - asibiti, amma bai jima ba ya rasu.

Mai Yamani mai shekara 18 a lokacin tana jiran dawowar mahaifinta a wani wuri da ke da nisan ƴan milimitoci daga cikin birnin.

"Ina zaune a cikin ɗakin mahaifina, wanda ke cike da littattafansa. Sai ya shigo da wani yanayi mai ban tausayi a fuskarsa. Ya nufi ɗakin cin abinci kai tsaye, kawai sai na ji ihunsa inda ya faɗi kalma ɗaya kawai – 'masifa'."

Wannan ba halinsa ba ne, domin shi mutum ne mai nutsuwa da kamun kai. Sai ya gaya mini abin da ya faru.

"A lokacin da aka yi harbin, wata tawagar man fetur daga Kuwait ta je don ganawa da Sarki Faisal da ƙarfe 10 a fadarsa, kuma mahaifina, kasancewarsa ministan mai, ya shiga don ya yi wa sarkin bayani," in ji ta.

"Ɗan uwan sarkin da ya harbe shi wanda shi ma yarima ne, kuma shi ma sunansa Faisal Ibn Musaed, ya shiga cikin tawagar da suka kai wa sarkin ziyara daga Kuwait. A lokacin da Sarki Faisal ya buɗe hannayensa don rungumar ɗan'uwansa ne ɗan'uwan ya fito da ƙaramar bindiga daga aljihunsa, ya harbe shi har sau uku a kai. Mahaifina yana tsaye kusa da su sosai."

A cewar wasu rahotanni a lokacin, wanda ya harbe sarkin ya faɗa wa 'yan sanda cewa ministan mai na tsaye kusa da su su sosai lokacin harbin har ya yi tunanin ya kashe shi ma.

Daga nan sai ministan ya garzaya da Sarki Faisal zuwa asibiti, inda aka tabbatar da rasuwarsa.

"Bayan haka, komai da ko ina ya yi shiru. Titunan Riyadh suka zama babu kowa.

Sarki mai sauye-sauye

An naɗa Faisal a matsayin Sarkin Saudiyya a shekara ta 1964 inda ya mulki ƙasa mai faɗin hamada kwatankwacin girman Yammacin Turai.

A wancan lokaci, an yaba masa a Ingila a matsayin "sabon abokin Turawa," kuma aikin da aka ɗora masa shi ne ya kawo ci gaba ga ƙasar da aka ɗauka tana baya ta ɓangaren cigaba a Gabas ta Tsakiya.

Amma tambayar a lokacin ita ce, shin zai iya yin hakan ba tare da rasa mulkinsa ba?

Yayan Faisal a lokacin na daga cikin manyan 'ya'yan Abdulaziz Al Saud kuma shi ne ya halarci yaƙin da mahaifinsa ya jagoranta na haɗa yankunan Larabawa, wanda daga bisani ya haifar da kafa Masarautar Saudiyya shekaru 30 kafin nan.

Daga baya Faisal ya zama Firaminista a ƙarƙashin yayansa da ya hau karagar mulki bayan rasuwar mahaifinsu.

Lokacin da Faisal ya zama sarki, ya riga ya shahara a matsayin ɗan siyasa mai basira da mai ibada kuma mai aiki tukuru, sannan mai son gyara. Mutum ne da ya saba da hulɗa da shugabanni a ƙasashen waje.

An san shi a matsayin sarki mai hangen nesa, wanda yake son amfani da arziƙin mai da ƙasarsa ta samu domin kawo ci gaba musamman a fannin ilimi da lafiya da tsarin shari'a.

Sai dai wasu daga cikin masu ra'ayin mazan jiya, waɗanda danginsa ke da alaƙa da su, ba su yi farin ciki da waɗannan sauye-sauyen ba.

A tsakiyar shekarun 1960, lokacin da Faisal ya buɗe tashar talabijin ta farko a Saudiyya, wasu suka kai hari kan ginin, ƙarƙashin jagorancin ɗan'uwan mutumin da daga baya shi ne ya kashe sarkin.

Sarkin Faisal kuma ya gabatar da ilimi ga mata.

Dr. Yamani ta ce: "Sarauniya Iffat, matarsa ta biyu ce ta fara ilimin mata a Saudiyya. Ina alfahari da cewa ni ɗaya ce daga cikin dalibai mata tara na farko a makarantarta. Sarkin Faisal ne ya lallaɓa malamai masu ilimin addini da cewa idan aka ba mata ilimi, za su zama iyaye nagari. Sunan makarantar a lokacin Dar Al Hanan."

Yamani ya fara aiki da Sarki Faisal a shekarar 1960.

Wannan abin mamaki ne domin shi ba ɗan sarki ba ne, duk da dai mutum ne mai ilimi sosai kuma lauya, amma ba daga gidan sarauta na Saudiyya ba.

Sarki Faisal ya karanta wasu labarai da Yamani ya rubuta, kuma waɗannan ne suka ja hankalinsa.

"Babana ya buɗe ofishin lauya na farko, sannan ya ci gaba da rubuta labarai masu ta da hankali suna kiran dimokiradiyya da kyakkyawan shugabanci. Don haka ne Faisal, wanda a lokacin yana matsayin sarkin gado, ya ce: 'Wane ne wannan mutum?' Domin yana neman mai ba shi shawara kan shari'a."

Daga baya, Sarki Faisal ya nada shi a matsayin ministan man fetur.

Kuma tare, sarki da Yamani suka tsara wata manufar da ta bai wa Saudiyya cikakken iko da manyan kadarorin man fetur ɗin ƙasar, wanda ya sa ƙasar ta zama mai karfi a duniyar Larabawa da kuma a matakin duniya.

Sabon naɗi

A shekara ta 1973, bayan yakin Isra'ila da kasashen Larabawa, Saudiyya, wadda ta zama mafi yawan mai a duniya, ta yi amfani da man fetur a matsayin makamin siyasa.

An rage isar da man fetur zuwa ƙasashen da ke goyon bayan Isra'ila a lokacin abin da ya sa farashin man a duniya ya tashi sosai.

Sheikh Yamani ne aka tura don isar da sakon da ya haɗa da "Muna so sojojin Isra'ila su fice daga ƙasashen Larabawa da suka mamaye, ko kuma za mu rage sayar muku da man fetur."

Hakan ya canza tsarin ikon duniya tsakanin ƙasashe masu arzikin mai da na masana'antu.

A shekara ta 1974, an zaɓi sarki Faisal "Gwarzon Shekara" na mujallar Times.

Dr Mai Yamani, ta ƙara da cewa; "Ba mu san dalilin kashe sarkin ba, amma kuma wanda ya kashe sarkin ya kasance mutum mai matsala, na ji zafin mutuwarsa sosai."

Yamani ya ci gaba da zama ministan mai na Saudiyya har zuwa 1986.

Dr Mai Yamani ta samu digirinta na uku wato PhD daga Jami'ar Oxford, ta rubuta littattafai kan asalin Larabawa, kuma ta yi aiki a matsayin mashawarciyar bankuna da kamfanonin mai.