Ɗan wasan da ya tserewa yaƙin basasa ya kai ga gasar Olympics da NBA

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Kelvin Kimathi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
- Lokacin karatu: Minti 6
Zai yi matuƙar wahala mutumin da ya ke da tsayin 7ft ya iya ɓuya a rububi amma lamarin na iya ƙara wahala ga Khaman Maluach cikin watanni 12 masu zuwa.
Ana sa ran ɗan wasan ƙwallon kwandon mai shekaru 17, wanda ke wakiltar Sudan ta Kudu a gasar Olympics, zai kasance ɗaya daga cikin ƴan wasa da za su yi kasuwa a gasar ƙwallon kwando ta Amurka (NBA) na shekara mai zuwa, inda tuni aka ce ƙungiyoyi da dama na ta rububin ganin sun samu nasarar ɗaukarsa.
Maluach ya ci gaba da nuna ƙwarewa a wasansa, amma bajintarsa a fagen wasa ba shi ne kaɗai abin mamaki a labarin matashin ɗan wasan ba.
“Kwallon kwando ba ƙaramin abu ba ne a gare ni. Na yi imani cewa wata baiwa ce da Allah ya yi mun domin in yi tasiri a rayuwar wasu kuma in sauya rayuwar dangina," ya shaida wa BBC Sport Africa.
"Wannan ƙwallon mai launin lemu ya yai matuƙar tasiri a rayuwata."
An haife shi a shekara ta 2006, danginsa sun tsere zuwa ƙasar Uganda da ke makwabtaka da su domin gujewa rikicin da aka dade ana fama da shi wanda a karshe ya kai ga Sudan ta Kudu ta sami ƴancin kai daga Sudan a shekara ta 2011.
Maluach ya tashi ne a Kawempe, wani gari da ke wajen Kampala babban birnin Uganda wanda ke da al'ummomi marasa galihu da dama.
Ya kasance lokutansa tare da mahaifiyarsa da ƴan uwansa giuda shida da danginsa daga bangaren mahaifiyarsa da ya ke a lokacin mahaifinsa ya fi zama a Sudan ta Kudu.
Ya fara samun ƙwarin gwiwar buga wasan ƙwallon kwando bayan wani kicibis da ya yi da wani a bakin hanya a lokacin da ya ke dawowa daga makaranta.
''Wani mutum yana tafiya a kan babur, sai ya tsaya a gaba na'' In ji Maluach
''Sai ya ce mun 'ya kamata ka fara buga wasan ƙwallon kwando. Zan iya taimaka maka da takalma, zan kuma iay samo maka ƙwallon' idan har na fara buga wasan nan take
Maye babban gurbi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Filin wasa mafi kusa da Maluach na da nisan tafiyar sa'a guda daga gidansu, kuma kusan kullum a cike ya ke.
Amma nisan ba shi ne kadai abin da ke kawo masa cikas a wasansa ba. Ƙarancin ƙwallaye da kuma rashin takalman wasan ba ƙaramin matsala ba ne - Inda Maluach ke sanya takalmi mai lamba 14 a lokacin da ya ke da shekara 13 kacal.
An tilasta masa buga wasansa na farko sanye da takalma nau'in 'Crocs' amma ya taka rawar ganin da ya burge masu horo na cikin gida, Wal Deng da Aketch Garang.
"A lokacin da na fara ganin Khaman, na yi la'akarida bajintarsa," Deng ya shaida wa BBC Sport Africa.
"Na san zai bunƙasa kuma ya zama ƙwararren ɗan wasa. Yana daukar darusa da wuri. Na gaya wa Aketch cewa nan gaba wannan yaron zai zama babban ɗan wasa. "
A shekara ta 2021, shekara guda bayan ya fara buga wasan ƙwallon kwando, Maluach ya sami gayyata daga NBA Africa Academy don yin gwaji da su.
Maluach had taught himself several moves by watching YouTube videos, learning from two-time NBA MVP Giannis Antetokounmpo and 2023 MVP Joel Embiid.
Maluach ya koya ma kansa abubuwa da dama ta hanyar kallon bidiyo a shafin Youtube, inda ya ke koyan abubuwa daga ɗan wasan da ya lashe kyautar ɗan wasa mafi bajinta a gasar NBA karo biyu Giannis Antetokounmpo da kuma wanda ya lashe kyautar a shekara 2023 Joel Embiid.
Kasancewar waɗannan ƴan wasan ƴan asalin nahiyar Afrika ne ya ƙara ƙarfafawa matashin gwiwar duƙufa wurin neman ƙwarewa
Maluach ya ce: “Ni da ɗan’uwana mukan yi wani abin da mu ke kir ‘aikin dare’.
“Idan ya kai karfe 12 na dare kamfanin sadarwa, suna ba ku da damar shiga intanet (data na wayar hannu) a farashi mai rahusa. Nakan yi amfani da tsawon wannan lokacin, Ina kallon waɗannan mutanen.
"A lokacin na ga yadda Giannis ke abin da ake kira 'jab step' , a wurin Joel kuma na koyi yadda ake 'shimmy'. Idan har za su iya taka rawar gani a can, tabbas ni ma zan iya . "
Komawa Afrika ta yamma

Asalin hoton, Getty Images
Ƙwazon da ya nuna ya haifar masa da nasara, kuma koci Deng yana cikin waɗanda suka shawo kansa wurin neman gurbin karatu a Kwalejin Afirka ta NBA da ke Dakar, Senegal, duk da cewa matakin na nufin sai ya sadaukar da abubuwa da dama.
Maluach ya kwashe shekara biyu bai ga danginsa a Kawempe ba yayin da yake mai da hankali kan haɓaka wasansa da kuma karatunsa.
''Makarantar ta taimaka mun sosai, a fannponi daban-daban''. In ji Maluach
''Fafatwa da da ƙwararru daga bangarori daban-daban na nahiyar Afrika ya taimaka mun wurin ƙara zaƙewa in inganta salon wasana a kodayaushe.
''Ɗaya daga cikin abubuwan da ya sa na yanke shawarar ci gaba da wasan ƙwallon kwando a mataki na gaba shi ne domin in samu ingantaccen ilimi. Akwai lokacin da na yi zango biyu ba tare da na je makaranta ba a Uganda''
Ɗan uwansa Majok ya ci gaba da yin 'aikin dare' domin isa ido kan yadda wasan ɗan uwansa ke bunƙasa
''Ina jin dadin ganinsa a Sahfin Youtube, saboda idan na kalle shi a talabijin, hankali na yakan tashi.''
Shekara uku bayan haka yanzu ana tunanin Maluach zai kasance zaɓi na uku a bikin zaɓen ƴan wasa na gasar NBA na shekara ta 2025, bayan ya samu cacncanta a lokacin da ya amince zai buga wasa a matakin matasa a kwalejin Duke.
Harin shiga zauren bajintar gasar NBA

Asalin hoton, Getty Images
Yin wasa a gasar ƙwallon kwando ta Afirka (BAL) shima ya ci gaban matashin.yi matuƙar taimakawa ci gaban matashin
Hakan ya ba shi damar buga wasa da manyan haziƙai daga ko'ina cikin nahiyar a cikin yanayi daban-daban tun lokacin da ya fara buga wasansa na farko, yana da shekaru 15 kacal, a kungiyar wasan Cobra na Sudan ta Kudu a shekara ta 2022.
A shekarar da ta biyo baya ya kai wasan ƙarshe da ƙungiyar AS Douanes ta Senegal, yayin da a farkon wannan shekarar ya buga wa City Oilers ta Uganda.
Baya daga gasar BAL, ya lashe kyautar ɗan wasa mafi hazaƙa a gasar 'Basketball Without Borders' ta 2023 a Johannesburg inda ya sami horo daga ɗan wasan ƙungiyar Miami Heat Bam Adebayo.
"Ina so in shiga zauren bajintar gasar NBA," in ji shi.
“Wannan shine ɗaya daga cikin burina na. Yin wasa a filin wasa ɗaya da Giannis da kuma Joel Embiid. "
Karfafawa matasan Afrika gwiwa

Asalin hoton, Getty Images
Wani mutum mai mahimmanci ga ci gaban Maluach ya zama ɗan wasa na duniya shine Luol Deng, tsohon ɗan wasan Chicago Bulls da Birtaniya.
Shugaban hukumar ƙwallon kwando ta Sudan ta Kudu tun daga shekarar 2019, tsohon ɗan wasan mai shekara 39 ya gamsu da kwarjinin ƙwararru da jajircewa da Maluach ya nuna.
"Ina ganin bajinta irin tawa a tattare da Khaman," kamar yadda ya shaida wa BBC Sport Africa.
“Na kasance a kusa da ƴan wasa da yawa kuma wani lokaci wasu abubuwa kan ɗauke masu hankali kuma ta hana su daga samun ci gaban da ya kamata.
“A dai na shi ɓangaren, abu ne da ya ke so. Ya san abin da ake bukata don cimma wannan burin, kuma abin da ya sa ya zama daban daga cikin kowa.”
A bara Maluach, wanda a lokacin yake da shekaru 16 da haihuwa, ya taimakawa Sudan ta Kudu samun gurbin shiga gasar Olympics a karon farko ta hanyar gasar cin kofin duniya ta Fiba.
Yana fatan bajintar tawagar Bright Stars a Paris 2024 zai iya zaburar da wasu a Nahiyar Afirka su cimma nasu burin.
"Burina na dogon zango shi ne sanya Afirka a idon duniya, da samar da damammaki da yawa ga yara masu tasowa saboda Afirka na da haziƙai da dama da ba a gano ba," in ji shi.
“Abin da suke buƙata shine damar nuna kansu.
"Na yi imanin yaran da ke kasata suna da ƙwarin gwiwa kuma wannan gasar ta Olympics zata haɗa kawunan mu."











