Labarin yadda mata ke rayuwa a ƙasurgumin gidan yari na Iran

    • Marubuci, BBC 100 Women
  • Lokacin karatu: Minti 4

Zaune ita kaɗai a dandariyar ƙasa cikin wani ƙaramin ɗaki maras taga, Nasim kan ji alamun ana azabtar da wasu fursunonin.

Mai gadin kan doki ƙofar ɗakin nata kuma ya tambaye ta: "Kina jin dukan da ake yi a can? Ki shirya, ke ce gaba."

Akan yi mata "tambayoyi har tsawon awa 10 zuwa 12 duk rana" kuma aka dinga yi mata barazana.

Kurkukun wanda bai wuce girman mita biyu ba, ba shi da gado ko banɗaki. Wata huɗu da ta yi a ciki shi ne karon farko da mai shekara 36 ɗin ta taɓa sanin gidan yarin Evin da ya yi ƙaurin suna.

Mutanen da kawai take gani su ne masu gadinta. Ta yi tunanin za ta "mutu ba tare da wani ya sani ba".

Mun tattara labarin daga majiyoyi na ƙwarai domin sanin abin da ya faru da Nsim da wasu matan, waɗanda yanzu haka ke tsare a gidan yarin na Evin.

Da yawansu na cikin dubban mutanen da aka kama da hannu a zanga-zangar yaƙi da saka ɗankwali, wadda ta biyo bayan mutuwar Mahsa Amini mai shekara 22 a hannun 'yan Hisbar ƙasar a watan Satumban 2022.

Yayin da tsofaffin fursunoni ke faɗar halin da suka shiga a gidan yarin Evrin, da wuya a iya samun labaran yayin da suke cikinsa.

Abin da muka ji ba rashin imani kawai yake nunawa ba, wasu sun ci gaba da yekuwar 'yancin mata ta hanyar karya dokokin da aka ƙaƙaba musu.

Akwai kuma wasu al'amura na ban mamaki. Akwai wata fursuna da ake bari wani zubin ta dinga ganawa da mijinta, har ma ta samu ciki.

Nasim da ke ƙaunar kaɗe-kaɗen rap, an kama ta ne a watan Afrilun 2023 bayan ta shiga zanga-zangar tare da ƙwayenta, har aka kashe ɗaya daga cikinsu ma yayin arangama da 'yansanda.

Mutanen da suka ga Nasim bayan ta fito daga gidan yarin na cewa sun ga ciwuka, da tabbuna a jikinta.

An kama Rezvaneh ma tare da mijinta saboda zanga-zangar a 2023. Duka an kai su Evin, wanda ke da ɓangaren mata daban da na maza.

Bayan tsarewa da tuhuma da wulakantawa, an mayar da Nasim ɓangaren mata, inda ake da mutum 70, cikinsu har da Rezvaneh, waɗanda aka kama mafi yawansu saboda laifukan siyasa.

Akasarin matan da ke wurin na zaman hukuncin shiga harkokin kare haƙƙi ne, da laifukan yaɗa farfaganda, da ɗaukar makamai don yaƙar gwamnati, da kuma yi wa tsaron ƙasa barazana.

Suna zaune cikin ɗakuna huɗu masu dandazon jama'a, inda mutum 20 ke cikin kowanne, sai kuma gado masu hawa uku.

A lokacin sanyi, "kowa na shiga rawar ɗari", amma matan "kan yi ta yawo da ruwan zafi a kwalaba" domin ɗumama jikinsu. A lokacin zafi kuma, suna jin jiki cikin zafi.

Akwai wani ƙaramin ɗakin girki mai 'yan risho. Idan suna da kuɗin sayen abinci a kantin gidan yarin, sukan yi girki don rage wa kansu yunwa saboda ƙarancin abincin gidan.

Sukan saka tufafinsu kuma ba a hana su zagayawa a yankinsu da ke da banɗaki biyu. Sukan yi layi duk yamma domin shiga banɗakunan.

A nan ne kuma suka haɗu da Rezvaneh, kuma bayan sun zauna tsawon kusan wata huɗu Rezvaneh ɗin ta gano Nasim na da ciki.

Ta sha faman neman samun ciki tsawon shekaru, har ma ta haƙura. Amma dokokin Evin, ita da mijinta - wanda shi ma fursuna ne a ɓangaren maza - akan ƙyale su su dinga haɗuwa lokaci-lokaci, kuma irin wannan lokacin ne ta samu cikin.

Lokacin da ta lura tana da cikin, "ta sha kuka tsawon kwanaki".

Daga baya aka ƙyale ta ta yi hoton cikin bayan wata huɗu, kuma likitoci suka faɗa mata mace za ta haifa.

Vida 'yarjarida ce da ke son zane-zane. Takan yi amfani da zanin gado da kuma fenti ta zana hotunan wasu matan.

An yiyo safarar ɗaya daga cikin zanen daga gidan yarin Evin - na wata mace Bakurɗiya mai suna Pakhshan Azizi wadda ta dinga shiga yankunan Iraƙi da Syria don taimaka wa mutanen da ƙungiyar Islamic State ta zalinta.

An yanke wa Pakhshan hukuncin kisa bayan tuhumar ta da ɗaukar matakamai, kuma ana fargabar nan gaba kaɗan za a aiwatar da hukuncin.

Samun kulawar likitoci abu ne mai wuya ga fursunonin. Ɗaya daga cikinsu, wata mai fafutikar kare haƙƙi kuma wadda ta lashe kyautar Nobel Peace Prize ta zamn lafiya - Narges Mohammadi - ta gamu da larurar huhu mai tsanani.

Sai da ta shafe lokaci mai tsawo tana fafutikar neman ganin likita. 'Yan'uwanta sun ce hukumomi sun sha hana a yi mata aiki saboda ta ƙi yarda ta saka ɗankwali zuwa wajen likitan. Har sai da sauran fursunonin suka shiga yajin aikin cin abinci sannan hukumomin suka ƙyale ta ta ga likitan.

An saki Narges tsawon kwana 21 a farkon watan Disamba saboda dalilai na rashin lafiyarta.

Ita da sauran sun sha gudanar da zanga-zangar a cikin gidan yarin. Duk da cewa doka ta tilasta musu saka hijabi ko kuma ɗankwali, da yawansu ba su sakawa. Bayan sun daɗe suna fafutika, da kyar aka ƙyale su suka kafa labule a gefen gadonsu domin su samu sirri daga kyamarorin tsaro.