Me aka cimma a taron NEC na PDP da aka yi bayan kai ruwa rana?

Lokacin karatu: Minti 3

Bayan shafe tsawon yinin yau Litinin ana kai ruwa rana tsakanin mambobin babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya, jam'iyyar ta gudanar da taronta na kwamitin zartaswa wato NEC karo na 100.

Taron na zuwa ne bayan wani taron sirri da gwamnonin jam'iyyar suka gudanar a gidan gwamnatin jihar Bauchi da ke unguwar Asokoro a Abuja.

Shugaban jam'iyyar na riƙo, Amb. Iliya Damgum ya shaida wa manema cewa taron ya mayar da hankali kan abu guda ɗaya, kodayake bai bayyana batun ba.

Taron na zuwa ne bayan shafe tsawon yinin ranar Litinin ana dambarwa tsakanin ƴan jam'iyyar game da taron.

Tun da farko tun da safe aka shirya gudanar da taron kwamitin zartwarwar jam'iyyar NEC a harabar ofishin jam'iyyar da ke Wadata Plaza.

Abin da aka cimma a taron

Bayan kammala taron , kwamitin ya amince da wasu abubuwa har guda uku kamar haka:

Matsayin sakataren jam'iyya: Taron ya amince Samuel Anyanwu ya ci gaba da riƙe muƙamin sakataren jam'iyyar na kasa har zuwa lokacin da za a gudanar da babban taron jam'iyyar na ƙasa.

Batun babban taron jam'iyyar: Haka ma taron ya amince da saka ranar 23 ga watan gobe na Yuli domin sake wani taron an mkwamitin zartaswa, wanda a shi ne za a tattauna tare da saka ranar gudanar da babban taron jam'iyyar na ƙasa.

'Taruka biyu aka yi gabanin taron na NEC'

Gabanin taron kwmaitin zartaswar jagororin jam'iyyar sun gudanar da taruka biy mabambanta a wurare daban-daban, duk dai da nufin samun daidaito takanin ƴaƴan jam'iyyar.

Taro na farko shi ne na kwamitin amintattun jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Sanata Adolphus Wabara, wanda ka gudanar a babban ɗakin tao na Ƴar'adua Center da ke Abuja.

Taro na biyu shi en wanda gwanonin jam'iyyar da ƴan majalisar dattawa da na wakilai da aka gudanar da a gidan gwamnatin jihar Bauchi da ke unguwar Asokoro a birnin na Abuja.

Wakilin BBC da ke wurin ya ce an gudanar da duka tarukan biyu ne da nufin lalubo bakin zaren yadda za a gudanar da babban taron kwamitin zartarwar jam'iyyar (NEC) .

Tun da farko dai kwamitin Amintattun Jam'iyyar ya shirya gudanar da taron ne a ofishin jam'iyyar da ke Wadata Plaza da misaƙalin ƙarsfe 10:00 na safe amma hakan bai samu ba.

Da gaske ƴansanda sun hana rufe Wadata Plaza?

Tun da safiya an samu rahotonnin da ke cewa ƴansanda ɗauke da makamai sun mamaye Wadata Plaza, hedikwatar jam'iyyar PDP da ke Abuja, yayin da tashin hankali ke ƙara ƙaruwa dangane da taron kwamitin zartaswa na Kasa (NEC).

Rahotannin sun bayyana cewa 'yan sanda sun hana Maina Chiroma, ɗaya daga cikin mambobin Kwamitin Amintattu na Jam'iyyar, shiga cikin harabar hedikwatar.

Duk da cewa an bar wasu ma'aikatan jam'iyyar sun shiga cikin harabar da farko ba tare da wani cikas ba, daga bisani sai aka tilasta musu fita daga ciki.

Haka kuma, 'yan jarida da ke wajen sun samu umarnin barin harabar hedikwatar jam'iyyar.

An hango wasu daga cikin 'yansanda suna toshe titin Dalaba Street, wanda ke kai wa kai tsaye zuwa Wadata Plaza.

Cikin wani saƙo da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na X, ta zargi ƴansandan da ƙoƙarin dakatar da taron nata.

To sai dai daga baya ƴansandan sun musanta batun hana gudanar da taron.

Rundunar ƴansandan birnin Abuja ta ce "babu gaskiya a rahotonnin sannan ba haka al'amarin yake ba. An kai jami'an ƴansandan ne zuwa wurin taron domin wanzar da doka da oda kamar yadda tsarin mulki ya tanada.

A wata sanarwa, rundunar ta ce "babu wani lokaci da jami'an ƴansanda suka kulle sakateriyar jam'iyyar ta PDP."

A sanarwar, kwamishinan ƴan sanda na Abujar ya buƙaci kafafen watsa labarai da su yi kaffa-kaffa wajen tantance labarai kafin su wallafa shi.

Mene ne asalin rikicin PDP?

Jam'iyyar PDP wadda ita ce babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya - ta faɗa cikin rikici ne tun gabanin babban zaɓen 2023.

Wani abu da masana ke ganin ya taimaka wajen rashin nasarar jam'iyyara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda ta zo na biyu a zaɓen.

An yi tunanin bayan zaɓen jam'iyyar za ta haɗa kan ƴaƴanta tare da ɗinke ɓarakar jam'iyyar, to amma da alama har yanzu tsugune ba ta ƙare ba.

A ranar 28 ga watan Maris din 2023 ne aka naɗa Amb. Umar Iliya Damagum a matsayin shugabanta na riƙo bayan dakatar da Iyorchia Ayu, da nufin magance matsalolin da suka kunno kai cikin jam'iyyar a wancan lokaci.

To sai dai bayan an kasa magance matsalolin jam'iyyar, lamarin da ya sa wasu suka fara zarginsa da zama yaron Ministan Abuja, Nyesom Wike, wanda ya shiga gwamnatin APC.

Zargin da Damagum ya sha musantawa, ko a wata hira da ya yi da BBC Hausa a baya-bayan nan ya ce tsakaninsa da masu yi masa wanzan zargi ''sai dai Allah ya isa''.