APC ta nada Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugabanta

Nentawe Yilwatda

Asalin hoton, X/Nentawe Yilwatda

Bayanan hoto, Nentawe Yilwatda
Lokacin karatu: Minti 3

Kwamitin zartarwa na Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, ya amince da nadin Farfesa Nentawe Yilwalda daga jihar Filato a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na ƙasa.

An cimma matsayar ne yayin taron kwamitin zartarwar na kasa da ya gudana a Abuja.

Taron wanda ke gudana a fadar shugaban ƙasar, ya samu halartar Shugaba Bola Tinubu da kuma gwamnonin jam'iyyar ta APC

Wane ne Farfesa Nentawe Yilwalda?

Kafin zaɓensa a matsayin sabon shugaban jam'iyyar APC na riƙon ƙwarya, Farfesa Nentawe Yilwatda ya kasance ministan jin-ƙai na Najeriya.

Sunan Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ɓulla a baya-bayan a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda ake kyautata zaton za su maye gurbin Ganduje.

Tsohon malamin jami'ar ya fito ne daga jihar Filato, kuma ya koyar ne a Jami'ar ayyukan noma da ke Makurdi kafin tsunduma cikin harkokin siyasa.

Haka nan ya taɓa zama kwamishinan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya tsakanin shekarun 2017 da 2021 a jihohin Benue da Anambra da Osun da Rivers da kuma Cross River.

Masu lura da al'amura na ganin sabon shugaban jam'iyyar na riƙon ƙwarya, Farfesa Nentawe Yilwalda ka iya zama cikakken shugaban jam'iyyar ko da bayan babban taronta na watan Disamba.

A watan Disamba ne jam'iyyar mai mulki za ta yi babban taronta na ƙasa domin zaɓen shugaban jam'iyyar mai cikakken iko.

Abokan takarar Farfesa Yilwalda

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Zaɓen Farfesa Nentawe Yilwalda a ranar Alhamis ɗaya ne daga cikin manyan abubuwan da ake sa ran taron ya cimma matsaya a kai.

Hakan ya biyo bayan saukan ba-zato ba tsammani da tsohon shugaban jam'iyyar, Abdullahi Ganduje ya yi a watan Yuni.

Abdullahi Ganduje ya ce ya sauka ne bisa dalilai na ƙashin kai, musamman domin kula da lafiya.

Jim kaɗan bayan haka ne aka naɗa Ali Bukar Dalori, ɗan asalin jihar Borno a matsayin mai riƙon muƙamin.

Sai dai saukar Ganduje daga muƙamin ta zo ne bayan tsawon lokaci da mutanen arewa ta tsakiyar ƙasar suka kwashe suna neman a mayar da muƙamin zuwa yankin.

Hasali ma batun ya yi ta tayar da ƙura tun kafin miƙa wa tsohon gwamnan na Kano muƙamin da kuma bayan ya hau kujerar.

Hakan kuwa ya faru ne kasancewar tun asali muƙamin na hannun ɗan asalin yankin na arewa ta tsakiya ne, wato tsohon gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Adamu.

Kafin zaɓen Farfesa Yilwalda, tsohon gwamnan jihar Nasarawa Tanko Almakura na daga cikin na gaba-gaba da ake kawowa a matsayin wanda zai iya zama sabon shugaban jam'iyyar na ƙasa.

Ana kallon Almakura a matsayin daɗaɗɗen mai biyayya ga jam'iyyar ta APC kuma mai ɗimbin gogewa a harkar siyasa, bugu da ƙari shi ɗan asalin jam'iyyar CPC ne wadda ta kasance ƙashin bayan haɗakar da ta samar da jam'iyyar APC.

Tsohon gwamnan na jihar Nasarawa na daga cikin ƴansiyasa da ake girmamawa a yankin na arewa ta tsakiya.

Sannan a baya-bayan nan ya fito fili ya nuna mubaya'a ga gwamnatin shugaban Najeriya, Bola Tinubu a lokacin da ake raɗe-raɗin cewa ƴan asalin tsohuwar jam'iyyar APC ba su aminta da salon mulkin ƙasar ba.

Tanko Amkaura ya yi gwamnan jihar Nasarawa ne daga shekarar 2011 zuwa 2019, inda aka fara zaɓen shi a jam'iyyar CPC, sai kuma karo na biyu a jam'iyyar APC.