Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd na son karɓo aron Gallagher, Endrick zai koma Lyon
Manchester United ta zayyana yanwasan tsakiya bakwai da take son ɗaukowa, yayin da take son ɗauko aron ɗanwasan tsakiya na Atletico Madrid da Ingila mai shekara 25 Conor Gallagher a Janairu. (Talksport).
Tottenham ta jingine neman da take yi wa ɗanwasan gaba na Bournemouth da Ghana Antoine Semenyo, amma Manchester City da Manchester United na son ɗanwasan mai shekara 25, kuma Liverpool ma na sha'war ɗanwasan bayan raunin da Alexander Isak's ya samu. (Sky Sports)
Semenyo, wanda darajarsa ta kai fam miliyan 60.5, zai yanke shawara kan makomarsa a ranar Litinin. (Mail)
Aston Villa na tuntubi wakilan kan ɗanwasan Tottenham da Wales mai shekara 24 Brennan wanda Crystal Palace ta nuna buƙatarsa. (Teamtalk)
Chelsea na shirin ba AC Milan ɗanwasan baya na Faransa Axel Disasi, mai shekara a watan Janairu. (Football Italia)
Chelsea da Manchester City na hamayya kan matashin ɗanwasan Ingila Jeremy Monga, mai shekara 16. (Teamtalk)
Roma ta taya ɗanwasan gaba na Manchester United da Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekara 24, kan yuro miliyan 5 a Janairu da kuma yuro miliyan 30 a Yuni domin kammala cinikinsa. (Il Messaggero - in Italian)
Manchester United da Newcastle United sun saka ɗanwasan tsakiya na Portugal Ruben Neves, mai shekara 28, cikin yanwasan da suke farauta. (Caught Offside)
Ɗanwasan gaba na Real Madrid da Brazil mai shekara 19 Endrick na shirin komawa taka leda a Lyon a matsayin ɗanwasan aro na tsawon wata shida. (ESPN)
Bayer Leverkusen na diba yiyuwar ɗauko ɗanwasan gaba na Brighton da Ingila mai shekara 17 Harry Howell, yayin da wasu ƙungiyoyin Jamus ke ribibin ɗanwasan. (Florian Plettenberg)
Chelsea ta nace kan ɗanwasan tsakiya na Lille mai shekara 18 Ayyoub Bouaddi. (Caught Offside)