Bindigogi 7 da ƴan fashin daji suka fi amfani da su a arewacin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan Najeriya sun daɗe suna tambayar ina ƴanbindiga da sauran masu tayar da ƙayar baya a ƙasar suke samun makamansu, lamarin da ya sa wasu suke zargin akwai lauje cikin naɗi.
An sha ganin manyan makamai a hannun ƴanbindigar, musamman a baya-bayan nan inda suke holen makamansu a kafofin sada zumunta domin bayyana wa duniya irin ƙarfin da suke da shi.
Baya ga samun irin wadannan makamai ta hanyar masu safarar su ta barauniyar hanya, lokaci zuwa lokaci wadannan ‘yan bindiga kan kai hari kan jami’an tsaro, kuma idan suka yi nasara sukan kwashe makamansu, waɗanda ake zargin suke amfani da su wajen ci gaba da kai hare-hare.
To amma wadanne bindigogi ne wadannan ‘yan bindiga ke amfani da su wajen kaddamar da hare-hare kan al’umma, musamman a arewacin Najeriya?
Wannan ya sa muka tuntubi Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, wanda masani ne kuma mai bincike kan harkokin tsaro a Najeriya da yankin Sahel, wanda ya lissafa mana wasu bindigogi da ƴanbinda suka fi amfani da su.
AK 47
Bindiga ƙirar AK-47 ita ce ta fi fice a hannun ƴanbindiga a Najeriya, kamar yadda ta kasance wadda ta fi karɓuwa a yanzu a ƙasashen duniya.
Bindiga ce da aka fara amfani da ita a Rasha a zamanin mulkin Tarayyar Soviet, inda wani mai suna Mikhail Timofeyevich Kalashnikov ya kasance wanda ya ƙirƙiro ta. AK ɗin da ke cikin sunan na nufin Avtomat Kalashnikova, wanda ke nufin bindiga mai tashi da kanta, wato mai fitar da harsasai da yawa a tare.
A shekarar 1947 ne Kalashnikov ya kammala tsarawa da haɗa bindigar, sannan aka amince a fara amfani da ita.
Harsashin bindigar na iya yin tafiya mai nisan mita tsakanin 300 zuwa 400, sanan za ta iya fitar da harsasai kusan 700 a cikin minti ɗaya, wanda hakan ya sa take cikin makamai waɗanda suka fi hatsari a duniya.
Akwai kuma bindiga ƙirar AK-49 wadda ita ma kamar ƙirar AK-47 ce aka sabunta tare da ƙara wasu abubuwa.
A game da wannan, Kabiru Adamu ya ce ƴanbindiga irin su Bello Turji da sauransu, duk sun fi amfani da irin wannan.
Type 59
Akwai na'ukan makamai da dama da ake kira da Type 59, amma ana kiran bindiga ƙirar pistol ta ƙasar China da Type 59.
Bindiga ce da take da kama da ƙirar Makarov ta Tarayyar Soviet, wadda kuma ake kira da Red Star.
An fara ƙirƙirar bindigar ce a kamfanin Factory 636 da ke garin Bei'an a lardin Heilongjiang da ke China.
An amince da ita ne a matsayin bindigar da za ta maye gurbin ƙirar Type 52 da Type 54.
An ƙirƙiri ta soji ce a tsakanin shekarar 1959 zuwa 1963 a kamfanin na Factory 626, sannan akwai nau'in da fararen hula ke amfani da ita.
G3 Heckler & Koch

Asalin hoton, Getty Images
Bindiga ƙirar G3 da ake kira da Gewehr bindiga ce da kamfanin Jamus Heckler & Koch da ke Jamus ya ƙirƙira a tsankanin shekarun 1950 domin amfanin sojojin ƙungiyar ƙasashen Nato.
Rahotanni sun ce ana fitar da bindigar G3 zuwa aƙalla ƙasashe 70 a faɗin duniya, sannan an bayar da lasisin haɗa ta a aƙalla ƙasashe daban-daban har kusan guda 15.
Idan aka harba ta, tana iya tafiya mai nisan mita 600, sannan tana iya fitar da harsashi tsakanin 500 zuwa 600 a cikin minti ɗaya.
MAT 49

Asalin hoton, Getty Images
MAT 49, bindiga ce da sojojin Faransa suka fara amfani da ita daga shekarar 1950 zuwa tsakankanin shekarun 1980.
An sace bindigar ne daga wata motar sojojin Faransa a ƙasar Cyprus a ranar 23 ga watan Satumban 1956 a lokacin rikicin Suez.
A tsankanin shekarun 1960 ne kamfanin d'armes de Saint-Étienne plant (MAS) ya karɓi ragamar haɗa bindigar, sannan suka dakata da yin bindigar a shekarar 1979, inda bindigar FAMAS ta maye gurbinta.
Bindigar na ɗaukar harsashi mai nauyin 23 cm tsakanin 20 zuwa 32.
Haka kuma tana iya fitar da harsashi 600 a minti ɗaya, sannan tana tafiya mai nisan mita 100.
PKM

Asalin hoton, Getty Images
PKM babbar bindiga ce (machin gun) da ta samo asali daga sojojin Tarayyar Soviet da wasu mutane a ƙarƙashin jagorancin M T Kalashnikov suka yi aiki a tare domin ƙirƙirowa.
A shekarar 1961 ne aka fara amfani da ita lokacin da sojojin USSR ke neman ƙirar bindiga ko makamai manya da za su maye gurbin ƙananan da matsakaitan makaman da suka daɗe suna amfani da su.
Ita kuma tana cin zangon mita 1200, sannan tana iya fitar da harsasai guda 650 zuwa 750 a minti ɗaya.
Harba ka ruga

Asalin hoton, Getty Images
Harba ka ruga ita ce bindigar da ta fi yawa a hannun mutane kasancewar doka ta amince a mallake ta bayan samun lasisi, wanda hakan ya sa ƴan sa-kai da ɗaiɗaikun mutane ma suke iya mallakarta ko dai domin kariya ko domin farauta.
Akwai na'ukan bindigar harbi ka ruga daban-daban, amma yawanci ba ta harba harsasai da yawa, sannan harsashinta ba ya yin tafiya mai nisan dogon zango.
RPG

Asalin hoton, Getty Images
RPG bindiga ce ta harba makaman roka wadda sojojin Tarayyar Soviet suka fara amfani da ita a shekarar 1962.
Farko RPG-2 aka fara haɗawa, sannan daga bisani aka samu cigaba aka mata garambawul ta koma RPG-7.
Asali ana harba ta ne kan tankokin yaƙi, amma ana iya jefa bama-bamai da ita, kuma sojojin ƙasasshe masu tasowa da dama suna amfani da ita.
Ana amfani da ita wajen tarwatsa gidaje da motoci da wasu abubuwa, sannan akan jefa ta a cikin taro domin tarwatsa mutane.
Sai dai wani abu da Kabiru Adamu ya bayyana shi ne ba kasafai wadannan bindigogi ke shiga kai tsaye hannun ‘yan fashin saji daga kasashen da ake kera su ba.
Yawanci suna bi ne ta hannun masu safarar makamai ta barauniyar hanya.
Rashin isasshen tsaro a kan iyakokin Najeriya sun saukaka yadda wadannan makamai ke kwarara zuwa Najeriya, inda suke karewa a hannun ‘yan fashin daji wadanda suka addabi al’umma.










