Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hanyoyin da ɗumamar yanayi ke shafar Najeriya
Yayin da wakilan gwamnatocin ƙasashe da kamfanoni da 'yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki suka hallara a birnin Belém, na Brazil, a taron kwana 11 na duniya na sauyin yanayi, na wannan shekara ta 2025, wanda aka yi wa laƙabi da COP30.
BBC ta yi nazari kan wannan gagarumar matsala da ta addabi duniya a yanzu musamman kan yadda ta shafi ƙasashe masu tasowa, kamar Najeriya da kuma yadda za a iya rage illolinta.
Taron na duniya na shekara-shekara na bana, wanda aka fara daga ranar Litinin 10 ga watan Nuwamba zuwa 21 ga watan na Nuwamba, na gudana ne bayan shekara 10 da yarjejeniyar yanayi ta Paris.
A lokacin ne ƙasashe suka yi alƙawarin rage zafin da yake ɗumama duniya zuwa maki 1.5 a ma'aunin Selshiyas.
Mence ce ɗumamar yanayi?
Ɗumamar yanayi kamar yadda kalmar take na nufin yanayi ne na duniya da yake sauyawa ya zama ya ƙara zafi a sanadiyyar hayaƙin da yake fita daga makamashin da ɗan'Adam ke amfani da shi, kamar na man fetur da dangoginsa.
Wannan hayaƙi ne da ke tafiya sama ya yi wa duniya rumfa ko bargo, to wannan bargo da hayaƙi ke yi wa duniya shi ne ke haddasa ɗumamayar yanayi, kamar yadda Dakta Sani Mu'azu, babban darektan shirin haɓaka makamashin haidurojin (Hydregen) na Najeriya ya bayyana wa BBC.
''Yanayin zafi a duniya yana ƙaruwa, ƙaruwar da yake yi shi ne, yakan haura yadda aka san shi a baya kamar shekara 30,'' in ji masanin.
Ya ƙara da cewa : ''To wannan kuma ƙaruwar da akan samu ita ke jirkirta abubuwa da yawa, kamar yanayin ruwan sama da ake samu, yanayin fari, da yanayin ambaliyar ruwa ko yanayin ƙanƙara a arewacin duniya ka ga ta fara narkewa.
''Dalilin da kuma ke haddasa hakan shi ne in hayaƙin da ke ɗumawa yanayin ya fita shi ne sai ya yi wa duniya bargo, wanda idan hasken rana ya zo duniya ya doki ƙasa, misali ruwa ko dutse to yakan koma sararin samaniya,'' in ji Dakta Sani.
Yadda ɗumamar yanayi ke shafar Najeriya
Ita matsalar ɗumamar yanayi aba ce da ta addabi kusan duniya gabaɗaya ba ta ware wani sashe, ta bar wani ba, illa dai a ce wasu ƙasashe da suka fi cigaba suna iya ɗaukar matakan rage tasirinta fiye da wasu da ba su kai su cigaba ba.
Saboda haka idan aka yi dubi da ƙasashe irin su Najeriya za a ga cewa wasu abubuwan da ke faruwa a sanadiyyar sauyin yanayin, ba su bambanta da na wasu ƙasashen sa'o'inta, in ji Dakta Sani Mu'azu, kamar yadda ya sheda wa BBC.
Ƙaruwar zafi:
''Matsalar ɗumamar yanayi kamar gama-gari ce , idan aka samu ɗumamaw yanayi ana samun jirkitar abubuwa da yawa.
''Idan muka dawo Najeriya, daga shekara 30, baya zuwa yanzu an samu canji na zafi, in ka shiga birane kamar su, Abuja, da Kano, da Legas za ka ga yanayin yadda ake samun zafi a lokacin zafi za ka ga ya ƙaru matuƙa.''
Ƙaruwar ambaliya:
Dakta Sani ya ce: ''Yawan ambaliya shekara 30 baya da yanzu ya ƙaru matuƙa, musamman a jihohin arewa da kuma na kudancin Najeriya, kuma hakan na faruwa ne ta hanyar abu biyu.
1-''Ƙarfin ruwa da ake samu a rana ɗaya ya ƙaru nesa ba kusa ba a kan yadda ake samu a da. Misali a baya za ka ga a can kudanci za ka ga ana samun ruwa tsawon kwanaki 200 zuwa 250, ko kuma mu a arewa misali akan samu adadin kwanaki 150 zuwa da 160 a Najeriya to amma yanzu abin ya ɗan fara canzawa zuwa baya.''
Dakta Sani, ya ƙara bayani da cewa, illar hakan ita ce wasu tsirrai (shuka) na buƙatar
cikakkun watannin da ake yin ruwa domin su yi yabanya sosai amma idan ruwan ya ragu ba za ta yi yabanya ba yadda aka saba gani, saboda haka babu abinci kenan idan kuma babu abinci to za a samu yunwa kenan.
Tazarar kwanakin da ake samu na ruwa sama:
A cikin damuna ita kanta akwai kawankin da ake samu na ɗaukewar ruwa, to a dalilin sauyin yanayi nazarin ya nuna daga shekara 30 baya zuwa yanzu wannan tazara ta ƙaru.
Kuma hakan na shafar noma, saboda idan ana samun fari na kwana 10 a yanzu ya zama kusan na kwana 15 ko 20,kuma hakan shi ma yana kawo matsala ga yawan yabanyar abinci, kamar yadda masanin ya yi bayani.
Waɗannan hanyoyi uku kusan su ne suka fi yawaita daga matsalolin da suka jiɓanci sauyi ko ɗumawar yanayi inda, musamman ambaliya kan haifar da asarar dukiya da rayuwa masu yawa, kamar yadda aka gani a 2024 a jihar Borno, kuma a bana an yi kusan irin wannan mummunar ambaliya a jihar Naija, in ji masanin.
Hanyoyin rage matsalar sauyin yanayi
Akan yaƙi wannan matsala ta sauyin yanayi ta hanyoyi biyu, kamar yadda Dakta Sani ya bayyana wa BBC.
''Tun da wannan hayaƙi shi ne yake haddasa sauyin yanauin to rage yawan fitar da shi to hakan zai sa a yaƙe shi ta haka, ka ga idan aka daina fitar da hayƙin zuwa sama to hakan zai ragu.
''Kuma ta yaya za a yi hakan, misali a canza yadda ake amfani da makamashi mai gurɓata muhalli, kamar yanzu a Najeriya, ɗaya daga cikin matakan da gwamnati ta ɗauka shi ne, yadda ta assasa amfani da makamashi na iskar gas a motoci da sauran injina maimakon fetur da man dizil.
''Ta wata fuskar bishiyoyi ma na taimakawa sosai wajen rage wannan matsala, kasancewar su bishiyoyi na buƙatar wannan ɗumi wajen rayuwa - saboda hakan yawan shuka bishiyoyi ko hana sare su na taimakawa.
''Sai kuma hanya ta biyu inda za a yi ƙoƙarin rayuwa da matsalar illa dai mutane za su iya ƙokarin sauya yadda suke wasu abubuwan saboda matsalar ta riga ta zama jiki.
''Misali saboda ƙaruwar kwanakin da ake yin fari ko ɗaukewar ruwan sama to sai manoma su riƙa amfani da iri mai yi da wuri da kuma juriyar rashin ruwa.
''Sannan ta ɓangaren ambaliya bincike kan yanayi da hasashe domin ankarar da jama'a kan abin da zai iya faruwa na taimakawa wajen magance wannan matsala ko kauce wa illolinta.