Masana na son a riƙa bai wa sauro maganin maleriya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, James Gallagher and Philippa Roxby
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health and science correspondent
- Lokacin karatu: Minti 3
Ya kamata a bai wa sauro maganin cutar maleriya domin kawar da cutar da ke cikinsu, ta yadda ba za su iya yaɗa cutar ba.
Cutar maleriya na kashe kimanin mutum 600,000 a kowace shekara, musamman yara - macen sauro ne ke yaɗa cutar a lokacin da suke shan jinin bil'adama.
Duk ƙoƙarin da ake yi yanzu na yaƙi da cutar shi ne kashe sauron da maganin ƙwari a maimakon kashe cutar da ke jikinsu.
To amma a yanzu wata tawagar masana a jami'ar Hardvard ta gano wasu ƙwayoyin magani wadanda za su iya kashe maleriyar da ke cikin sauro idan maganin ya shiga ta tafin ƙafarsu.
Yanzu abin da ake ƙoƙarin yi shi ne barbaɗa wa gidan sauro/sange maganin.
Kwana a gidan sauro na daga cikin nagartattun hanyoyin kare kai daga kamuwa da maleriya yayin da sauro ya fito farauta da daddare.
Haka nan akan sahwarci mutane su yi amfani da rigakafin cutar a wuraren da maganin ya kai.
Gidan sauro kan hana sauron isa jikin mutum sannan kuma yakan kashe sauron da ya sauaka a kansa.
Sai dai a ƙasashe da dama sauro kan bijire wa magungunan ƙwari da ake amfani da su wajen ƙoƙarin kashe su.
"Ba mu taɓa yunƙurin kashe ƙwayoyin cutar maleriya tun daga cikin sauro ba kafin yanzu, domin mun mayar da hankali ne wajen kashe sauron," in ji Dakta Alexandra Probst, wadda ke aiki a Jami'ar Harvard.
Sai dai, ta ce da alama waccan dabara ta baya "ba ta aiki a yanzu."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masanan sun yi nazari kan halittar ƙwayoyin cutar maleriya domin gano ɓangarorin da ke da rauni a cikinsu.
Daga nan sai aka gwada bai wa matan sauro maganin, inda aka gano wasu magunguna biyu da ake ganin suna aiki sosai, waɗanda suka kashe ƙwayoyin cutar maleriyar ɗari bisa ɗari.
Daga nan ne aka gwada magungunan a jikin wata raga mai kama da gidan sauro.
"Ko da sauron ta tsira da ranta bayan sauka a kan gidan sauron, to ƙwayoyin cutar zazzaɓin da ke cikinta za su mutu, saboda haka ba za ta iya zuba ma wani zazzaɓin ba," in ji Dakta Probst.
"Ina ganin wannan hanya ce mai ban sha'awa kasancewa sabuwar hanya ce fil ta magance matsalar sauro."
Maganin zai iya ci gaba da aiki a jikin ragar sauro har tsawon shekara ɗaya, wanda hakan ke nufin tsarin na da rahusa kuma ya fi sauƙi a kan yin amfani da maganin kashe ƙwari, in ji masana.
An tabbatar da ingancin wannan tsari a ɗakunan bincike. Yanzu mataki na gaba shi ne za a gwada tsarin a ƙasar Ethiopia domin ganin yadda zai yi aiki a zahiri.
Za a kwashe shekara bakwai ana gwajin tsarin kafin tabbatar da ingancinsa.
Amma abin da ake shirin yi shi ne za a sanya wa gidan sauron maganin ƙwari da kuma maganin kashe ƙwayar cutar maleriya, saboda idan ɗaya dabarar ba ta yi aiki ba, ɗayan za ta yi.











