Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yadda na yi rayuwa tare da shugaban ISIS, al-Baghdadi'
- Marubuci, Feras Kilani
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
- Aiko rahoto daga, Baghdad
Cikin wata na musamman daga gidan yari, matar marigayi shugaban ƙungiyar Islamic State ta ba da labarin rayuwarta. Umm Hudaifa ce matar Abu Bakr al-Baghdadi ta farko kuma ta shaida lokacin da ya mulki ɓangarorin Syriya da Iraƙi a matsayin daular Musulunci. Yanzu tana tsare a wani gidan yarin Iraƙi inda ake tuhumar ta da laifukan ta'addanci.
A bazarar shekarar 2014, Umm Hudaifa na zaune a birnin Raqqa, garin Syriya kenan da IS ta fi ƙarfi a lokacin, tare da mijinta.
Yayin da jagoran da ake nema ruwa a jallo ke ɓoye-ɓoye a wirare daban-daban, a wannan lokacin ne ya tura dakaru su kwaso 'ya'yanta biyu ƙanana. "Ya faɗa min cewa zai kai yaran ne don koya musu ninƙaya a ruwa," in ji Umma Hudaifa.
Akwai ɓoyayyar talabijin da take amfani da ita a asirce.
"Ina kunna ta idan ba ya gidan," a cewarta ya zaci ba ta aiki. Ta ƙara da cewa an keɓance ta daga sauran duniya ta hanyar hana ta amfani da duk wata na'ura kamar waya da kuma kallon talabijin tun daga shekarar 2007.
'Yan kwanaki bayan ɗaukar yaran, ta ce ta sha mamaki da ta kunna talabijin ɗin. Ta ga mijinta na yi wa jama'a jawabi a babban masallacin al-Nuri da ke birnin Mosul na Iraƙi ya na bayyana kansa karon farko a matsayin shugaban daular Musulunci.
An ga bidiyon al-Baghdadi yana neman haɗin kan Musulmai a matsayin shugabansu a duka faɗin duniya sanye da baƙaƙen kaya, wanda shi ne lokaci mafi girma a rayuwar ƙungiyar IS yayin da ta mamaye wasu yankunan Iraƙi da Syriya.
Umm Hudaifa ta ce ta kaɗu da gano cewa 'ya'yanta suna Mosul tare da shi - ba wajen koyon ninƙaya ba.
Mun samu wuri a wani ɗakin karatu inda muka yi magana tsawon awa biyu. Yayin tattaunawar ta nuna cewa ita aka zalinta bayan ta yi yunƙurin guduwa daga hannun mijin nata kuma ta musanta hannu a duk wasu ayyukan IS na rashin imani.
Hakan ya saɓa sosai da yadda aka bayyana ta a takardun kotu da aka shigar da ƙarar da al'ummar Yazidi suka shigar, waɗanda 'yan IS suka yi garkuwa da su kuma suka yi musu fyaɗe - sun zarge ta da haɗa baki wajen mayar da su bayi.
Ba ta ɗaga kanta ba yayin hirar, ko sau ɗaya. Tana sanye da baƙaƙen kaya kuma wani ɓangare na fuskarta kawai ake gani, daga hancinta zuwa ƙasa.
An haifi Umm Hudaifa a 1976 a Iraƙi kuma ta auri Ibrahim Awad al-Badri, wanda daga baya aka sani da Abu Bakr al-Baghdadi a shekarar 1999.
Ya karanci fannin harkokin Shari'ar Musulunci a Jami'ar Baghdad kuma ta ce a lokacin yana da bin addini amma ba mai tsattsauran ra'ayi ba ne.
Sai kuma a 2004, shekara ɗaya bayan Amurka ta jagoranci mamaye Iraƙi, dakarun Amurka suka tsare al-Baghdadi a sansanin Bucca da ke kudancin ƙasar tare da wasu mazajen, waɗanda daga baya suka zama jagororin IS.
Bayan sakinsa, ya yi iƙirarin cewa ya sauya: "Ya koma maras fushi kuma ya daina yi wa mutane tsawa cikin fushi."
Wasu da suka san shi sun ce ya fara hulɗa da al-Ƙa'ida ne kafin ya je sansanin Bucca, amma a cewarta daga wannan lokacin ne ya koma mai tsattsauran ra'ayi.
"Ya fara samun matsala a tunaninsa," in ji ta. Da aka tambaye ta dalili, sai ta ce "ya ga wasu abubuwa da ba za ku gane ba".
Tana ganin duk da bai faɗa mata ba, amma "lokacin da ake tsare da shi an ci zarafinsa ta hanyar lalata". Wasu hotuna da suka ɓulla na gidan yarin da Amurka ke jagoranta a Iraƙi mai suna Abu Ghraib sun nuna yadda ake tilasta wa fursunoni tayar wa da mutane sha'awa da kuma saka su yin wasu abubuwa na ƙasƙanci.
Mun faɗa wa Ma'aikatar Tsaro ta Amurka zarge-zargen da ta yi amma ba ta ba da wata amsa ba.
Ta ce ta fara mamakin ko ya shiga wata ƙungiyar gwagwarmaya ne. "Na sha caje kayansa idan ya dawo gida, ko idan yana wanka ko kuma idan yana barci.
"Har jikinsa nake dubawa ko zan ga wani rauni...na yi mamaki," a cewarta, amma ba ta ga komai ba.
"Na faɗa masa cewa, 'Ka shiga hanyar ɓata'...abin ya ɓata masa rai."
Ta faɗi yadda suke yawan sauya gidan zama, da yadda suka samu takardun boge na ƙarya, da yadda ya auri mace ta biyu. Umm Hudaifa ta ce ta nemi ya sake ta amma kuma ba zata iya yarda da sharaɗin da ya ke gindaya mata ba, na cewar sai dai ta bar masa 'ya'yanta, wanda hakan yasa dole ta ci gaba da zama da shi a hakan.
Yayin da Iraƙi ta faɗa rikicin ƙungiyoyi da ya kai har 2008, ta san cewa lallai akwai hannunsa a ɓangaren ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi na Sunni. A 2010 ya zama shugaban ƙungiyar Islamic State ta Iraƙi - bayan kafa ta a 2006, wata gamayya ce ta ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi a Iraƙi.
"Mun koma Idlib a Syria a watan Janairun 2012, kuma a nan ne na fahimci cewa shi ne Khalifa," in ji Umm Hudaifa.
Ƙungiyar Islamic State ta Iraƙi ta haɗe daga baya don kafa babbar Islamic State.
A lokacin, ta ce sai ya fara saka irin tufafin 'yan Afghanistan, ya tara gemmu kuma ya fara ɗaukar ƙaramar bindiga.
Bayan lamarin tsaro ya taɓarɓare a arewa maso yammacin Syriya, sai suka koma birnin Raƙƙa, wanda daga baya IS ta mayar da shi babban birnin daularta.
Tuni aka san irin rashin imanin ƙungiyoyin da suka haɗu suka zama IS, amma a 2014 da 2015 abin ya ƙara fitowa fili.
Wata tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya ta gano cewa IS ta aikata kisan ƙare-dangi a kan al'ummar Yazidi marasa rinjaye.
IS kan yaɗa rashin imaninta ta bidiyo. Ta kashe kusan mutum 1,700 wanda akasarinsu dakarun 'yan Shia ne, yayin da suke dawowa daga wani sansani a arewacin Bagadaza.
Sauran sun ƙunshi ƙona wani matuƙin jirgin sama ɗan ƙasar Jordan.
Wasu matan da suka zauna 'yan IS yanzu na cewa ba su san yadda abin yake ba a lokacin, shi ya sa na matsa wa Umm Hudaifa kan ra'ayinta game da lokacin - ta ce ko a lokacin ba ta iya kallon hotunan rashin imanin saboda "zubar da jini haka kawai rashin imani ne kuma yin hakan keta alfarmar ɗan'adam ne".
Umm Hudaifa ta ce ta ƙalubalanci mijinta game da "jinin mutanen da babu ruwansu" da ya zubar kuma ta faɗa masa "akwai abubuwan da za su iya yi kamar yadda Shari'ar Musuluncin ta tanada, kamar ɗora su kan hanyar tuba".
Ta ce yakan ɓoye kwamfutarsa a cikin wata jaka. "Na yi ƙoƙarin shiga na ga abin da ke faruwa amma ba ni da ilimin kimiyya kuma ko da yaushe sai ta tambaye ni kalmomin sirri."
Ta ce ta yi ƙoƙarin guduwa amma wasu mazaje ɗauke da bindigogi suka hana ta wucewa kuma suka mayar da ita gidan.
Game da faɗa kuma, ta ce a iya saninta "bai taɓa shiga wani yaƙi ba", ta na mai cewa yana Raƙƙa lokacin da IS ta karɓe iko da Mosul - daga baya ya je Mosul ya yi wannan jawabin.
Jim kaɗan bayan wannan jawabin, al-Baghdadi ya aurar da 'yarsu mai shekara 12, Umaima, ga wani abokinsa mai suna Mansour, wanda aka damƙa wa amanar kula da iyalin. Umm Hudaifa ta ce ta yi ƙoƙarin hanawa amma ba a saurare ta ba.
Wata majiya a ɓangaren tsaro a Iraƙi ta faɗa mana an taɓa aurar da Umaima tun tana shekara takwas ga wani kakakin IS. Amma ya ce an shirya auren ne kawai saboda mutumin ya dinga shiga gidan idan al-Baghdadi ba shi nan, amma bai taɓa saduwa da ita ba.
Sai kuma a 2014, Umm Hudaifa ta haifi wata yarinyar mai suna Nasiba, wadda ke da matsalar zuciya. Wannan ya yi daidai da lokacin da Mansour ya kai 'yan matan Yazidi tara zuwa gidan. Shekarunsu sun fara daga tara zuwa 30.
Suna cikin dubban matan Yazidi da IS ta bautar da su - kuma aka kashe wasu dubbai.
Umm Hudaifa ta ce ta kaɗu kuma "ta ji kunya da lamarin".
Na bi diddigin mahaifin Samar mai suna Hamid, wanda cikin hawaye ya tuna loakcin da aka ɗauke ta.
Ya ce yana da mata biyu waɗanda aka yi garkuwa da su tare da wasu matan 26, cikinsu har da 'yan'uwansa biyu da iyalansu daga garin Khansour da ke Sinjar. An kai su cikin wasu tsaunika da ke kusa.
Har yanzu ba a san inda 'ya'yansa shida suke ba har da Samar. Wasu sun koma bayan an biya kuɗin fansa, yayin da wasu kuma sai bayan an ƙwace garuruwa daga hannun IS.
Ɗaya yarinyar mai suna Zena 'yar ɗn'uwansa ce da ta maƙale a arewacin Syriya. 'Yar'uwar Zena mai suna Soad ba ta haɗu da Umm Hudaifa ba, amma an bautar da ita, aka yi mata fyaɗe, kuma aka sayar da ita har sau bakwai.
Hamid da Soad sun shigar da Umm Hudaifa ƙara saboda haɗa baki da ita wajen sace su da kuma bautar da 'yan matan Yazidi. Ba su yarda cewa ita ma an zalince ta ba kuma suna neman a yanke mata hukuncin kisa.
"Ita ce ta kitsa komai da komai. Ita ce ta yi zaɓa - wannan ce za ta yi mata aiki ko kuma wannan ce za ta yi wa mijinta aiki...kuma 'yar'uwata na cikinsu," in ji Soad.
"Matar ɗan'daba Abu Bakr al'Baghdadi ce, kuma ita ma mai laifi ce kamar shi."
Mun kunna wa Umm Hudaifa hirar da muka yi da Soad kuma ta ce: "Ba na musanta cewa mijina mai laifi ne," amma ta ƙara da cewa tana "neman afuwa game da abin da ya faru da su", kuma ta ƙaryata zarge-zargen da aka yi mata.
Umm Hudaifa ta faɗa daga baya a Janairun 2015 cewa ta haɗu da 'yar Amurka da aka yi garkuwa da ita Kayla Mualler, wadda aka tsare wata 18 kuma ta mutu a tsaren.
An kai Umm Hudaifa wani gida a Raƙƙa inda ta ji wata murya daga kan bene kuma ta je ta ga abin da ke faruwa. Cikin daƙin sai ta ga Kayla. "Kamar tana cikin farin ciki...ta faɗa min cewa ta zama matar sheikh ɗin...sai na gano cewa tana nufin mijina.
Ta ce Kyala ta yabe shi "cikin ƙauna" wanda hakan ya sa ta ji kishi da kuma fushi a lokacin da take ƙoƙarin ceton ran 'yarta Nasiba, wadda ta rasu daga baya.
Sai dai wannan labarin ya sha bamban sosai da wanda waɗanda aka tsare tare da Kyala suka bayar. Bayan mutuwar Kayla, mahaifiyarta Marsha ta ce abin da wata fursunan ta faɗa ya nuna "ba ta auri mutumin nan ba, kawai al-Baghdadi ya ɗauke ta ne da ƙarfin tsiya, ya yi mata fyaɗe, ya ci zarafinta, kuma duk lokacin da ta fito daga ɗakinsa tana kuka".
Kuma wani ƙwararre da ya yi aiki da 'yan sanda ya yi bayani cewa Kayla ta yi abin da Umm Hudaifa ta bayyana, babu mamaki ta yi ne don ta tsira.
Har yanzu ba a san abin da ya kashe Kayla - IS ta ce wani harin rundunar sojin Joradan ne ya kashe ta, amma Amurka ta sha musanta hakan kuma yanzu wata majiya a rundunar tsaron tsaron Iraƙi ta faɗa mana cewa IS ce ta kashe ta.
A 2019, dakarun Amurka sun binciki wurin da al-Baghdadi yake ɓuya a arewacin Syriya tare da iyalinsa. Baghdadi ya tashi wani bam da ke jikinsa lokacin da aka tarfa shi a cikin wata hanya, inda ya kashe kansa da kuma yara biyu, yayin da kuma aka kashe mtansa biyu cikin huɗu a harbe-harbe.
Sai dai Umm Hudaifa ba ta wurin - tana zaune a Turkiyya bisa sunan ƙarya kafin a kama ta a 2018. An mayar da Iraƙi a watan Fabrairun shekarar nan, inda aka jefa ta a gidan yari tun daga lokacin yayin da ake ci gaba da binciken rawar da ta taka a IS.
Babbar 'yarta Umaima na tare da ita a gidan yari, ita kuma Fatima mai shekara 12 ke tsare a sansanin tsare yara. An kashe ɗaya daga cikin 'ya'yanta maza yayin wani hari da Rasha ta kai a Syriya a kusa da garin Homs, ɗayan kuma ya mutu ne tare da mahaifinsa a cikin hanyar ƙarƙashin ƙasa, sai kuma ƙaramin da ke gidan marayu.
Bayan mun kammala hirar, ta ɗaga kanta kuma a nan ne na ga fuskarta. Ta nemi ƙarin bayani game da 'ya'yanta ƙanana. Yanzu kuma da ta koma gidan yari, dole ne ta jira kafin ta san ko za a tuhume ta da aikata laifi.