Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa muka amince da ɓangaren Wike na PDP - INEC
Hukumar zaɓen Najeriya ta bayyana dalilin da ya sa ta amince da shugabancin riƙon ƙwarya da ɓangare Nyesom Wike ya samar a jam'iyyar PDP.
INEC ta ce tana biyayya ne ga doka da hukuncin kotu kan duk wani mataki da ta ke ɗauka, ko dai a kan jam'iyyun siyasa ko ƴan takara ko kuma rikicin cikin gida na jam'iyyun Najeriya, kamar yadda kundin mulkin ƙasa ya yi tanadi.
Bayanin hukumar INEC na zuwa ne bayan sabon rikicin shugabanci da ya kunno kai a cikin jam'iyyar PDP, inda ake jayayya tsakanin shugabanci ƙarƙarshin Kabiru Tanimu Turaki, da kuma shugabancin riƙon ƙwarya ƙarƙashin Mohammed Abdulrahman, mai samun goyon bayan ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike
PDP ta zaɓi Tanimu Turaki a matsayin shugabanta na ƙasa ne a wajen babban taron da ta yi cikin watan Nuwamban bara a birnin Ibadan na jihar Oyo, duk da cewa tun da farko an gudanar da taron ne cikin jayayya da iƙirarin umarnin kotu masu karo da juna tsakanin ƴaƴan jam'iyyar.
A ranar Juma'a, 30 ga watan Janairun 2026 kuma wata babbar kotun tarayya a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ta rusa shugabancin jam'iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki.
Kotun ta ce an gudanar da babbn taron PDP na Ibadan ne a bisa yi wa umarnin kotu karan tsaye, domin haka duk wata matsaya ko hukuncin da aka yanke a yayin taron ya saɓa doka kuma ba zai taɓa zama gaskiya.
Har ila yau, kotun ta amince da ɓangaren shugabancin riƙon ƙwarya na Mohammed Abdulrahman a matsayin shugaban jam'iyyar, har sai an gudanar da babban taron jam'iyyar.
A wata hira da BBC, ɗaya daga cikin masu magana da yawun hukumar INEC, Zainab Aminu ta ce hukumar ta ɗauki matakin ne saboda biyayya ga umarnin da kotun ta bayar game da dambarwar shugabancin PDP.
Ta ce ''Idan kotu ta byr da umarnin cewa ga abin da za a yi, to hukumar zaɓe hukuma ce mai biyayya ga umarni na kotu da dokoki na zabe da kuma dokoki na ƙasa.
Saboda haka wannan rikici da ke faruwa a cikin jam'iyyu na siyasa, hukumar zaɓe kanta abin yana damun ta. Ya kamata a ce jam'iyyun siyasa su haɗa kan mambobinsu domin su samu damar tallata ƴan takarar su ga mutane.''
Ta yi bayanin cewa jam'iyyun siyasa sun gaza wajen shawo kan dambarwar su ta cikin gida, saboda haka ne suke ƙoƙarin shigar da hukumar zaɓe cikin ayyukan da ba nata ba ne.
''Idan ana irin wannan rikici tsakanin mambobin jam'iyyu, daga ita hukumar zaɓen ake wahalarwa saboda dole ne ta yi biyayya ga duk wani umarni da kotu ta bayar,'' in ji Zainab Aminu.
Sabuwar taƙaddamar shugabancin PDP ta taso ne bayan ɓangaren Wike ya samu amincewar hukumar INEC saboda umarnin yin hakan da ya samo daga kotu, wanda kuma ɓangaren Tanimu Turaki ke cewa ba za ta saɓu ba.
Rikice-rikicen PDP
Jam'iyyar PDP ta daɗe tana fama da rikice-rikice, musamman tun bayan zaɓen fitar da ƴan takara da Atiku ya doke Wike, lamarin da ya sa Wike da wasu gwamnoni suka ware, suka yi tallata Atiku a babban zaɓen.
Amma wannan rikicin ya samo asali daga babban taron jam'iyyar da aka yi a watan NuwambaN 2025, inda babbar jam'iyyar ta zaɓi Kabiru Tanimu Turaki a matsayin sabon shugabanta, duk da irin jimirɗar da aka yi fama da ita gabanin zaɓen.
An samu umarnin kotu har guda uku da suka nemi jam'iyyar ka da ta gudanar da taron nata na ranar 15 ga watan Nuwamba a jihar Oyo.
Sai dai kuma wata kotun a jihar Oyo ta yanke nata hukuncin daban, inda ta ba kwamitin shirya babban taron umarnin ya gudanar da taronsa, lamarin da tsagin Wike ya ƙi amincewa da shi.