Yadda Canada ta zama cibiyar satar motoci ta duniya

Joshua Abush designed and installed driveway bollards for a client to protect their car. in Toronto. February 16, 2024. The bollards are heated, controlled by a remote fob, and raise (or lower) in about a 15 seconds.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda aka kafa turaku a gaban wata ƙaramar mota a birnin Toronto domin kareta daga ɓarayi
    • Marubuci, Nadine Yousif
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Toronto

Da safiyar wata rana cikin watan Oktoban 2022, Logan LaFreniere ya tashi daga barci bai ga motarsa ba.

Sabuwar motarsa samfurin Hulix ta ce ɗaukarni inda ka ajiyeni.

Kyamarar tsaro ta gidansa ta ɗauki hotu mutum biyu lokacn da suka ɓalla gidansa, suka yi awon gaba da ita.

Watanni bayan haka, sai motar ta bayya a wani shafin yanar gizo da ke tallata motocin sayarwa a tekun Ghana mai tazarar kilomita 8,500 daga gidansa.

“Wani abu da nake tuna motar da shi, shi ne a bayan kujerar direba na saka kwamfuta saboda ɗana, haka kuma akwai wata jaka da muke rufeta da ita,'' kamar yadda Mista LaFreniere ya shaida wa BBCC.

''Abin mamaki sai ga hoton kwamfutar a cikin abubuwan da aka lissafo cikin motar'', in ji shi.

“Tabbas babu shakka na gamsu a zuciyata cewar wannan motata ce.”

Ba Mista LaFreniere ba ne kaɗai mai irin wannan labarin ba. A shekarar 2022, fiye da mota 105, 000 aka sace a Canada, kusan a kowane minti biyar akan sace mota guda.

Cikin waɗanda lamarin ya shafa har da ministan shari'ar ƙasar, wanda ɓarayi suka sace wa mota- ƙirar Toyota Highlander XLE da gwamnati ta ba shi - har sau biyu.

A farkon wanan shekara ne, 'yan sandan ƙasa da ƙasa suka ayyana Canada cikin ƙasashe 10 da aka fi satar mota cikin ƙasashe 137 da ke cikin alƙaluman.

Bayanan bidiyo, Ɓarayin mota a Canada na sace wa mutum mota har sau biyu
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hukumomin ƙasar sun ce motocin da ake sacewa, akan yi amfani da su wajen aikata laifuka, ko a sayar a cikin ƙasar, ko kuma a fitar da su ƙasashen waje domin a sayar da su.

'Yan sandan ƙasa da ƙasa sun ce sun gano fiye da mota 1,500 a sassan duniya daban-daban, da suka ce an sace su daga Canada tun watan Fabairu, kuma a kowa mako ana gano kusan mota 200 da aka sata daga Canada, galibi a tasoshin jiragen ruwa.

Satar mota wani mummunan al'amari ne a Canada - wanda hukumar Inshorar ƙasar ta bayyana shi a matsayin mummunan bala'i na ƙasa.

Matsalar ta tilasta wa 'yan sandan ƙasar fitar da wasu dabarun yaƙi da al'amarin.

To sai dai wasu 'yan ƙasar sun riƙa samar wa kansu mafita, inda suka riƙa kafa na'urorin da ke nuna wurin da motocinsu suke.

Ga waɗanda ba su da zarafin yin hakan, sukan kafa turaku a gaban inda suka ajiye motocinsu - irin dai waɗanda ake gani a harabar bankuna da ofisodhin jakadanci - kare motocinsu daga sata.

Nauman Khan, wanda ke zaune a birnin Mississauga, ya fara sana'ar kafa turakun bayan da aka sace masa mota shi da ɗan'uwansa.

Mista Khan ya ce ɓarayin sun ɓalla ƙofar gidansa a lokacin da matarsa da ƙaramin ɗansa ke barci.

Ya ce ɓarayin sun riƙa neman makullin motarsa ƙirar Mercedes GLE dake ajiye a harabar gidansa, to amma daga baya ɓarayin sun gudu bayan da ya fusknace su.

Bayan firgici da tashin hankali da suka fuskanta, daga baya sun sayar da duka motocinsu, in ban da wasu guda biyu na da suka gada.

Ta hanyar, sabuwar sana'ar tasa, Mista Khan ya ce ya ji labarai da suka yi kma da nasa daga mutane a birin Toronta.

“Akwai wani da muka yi wa aiki da ya ce ankutsa gidaje da dama a layinsu, abin da ya sa ɗauki masu gadi da ke kwana a gidanda domin samun kariya''.

Yawan satar mota a Cadana abin mamaki ne idan aka yi la'akari da ƙanƙantar ƙasar idan aka kwatanta da Amurka da Birtaniya, da sauran ƙasashe da ake aikata laifuka, in ji Alexis Piquero, darakta hukumar ƙididdiga ta Aurka.

“[Canada] ba ta da tasoshin ruwa kamar na Amurka,” in ji Mista Piquero.

Yayain da ƙasashen Birtaniya da Amurka suka fuskanci ƙaruwar satar mota tun bayan annobar korona, Yawan na Canada ya zarce nasu, saboda a Canada cikin masu mota 100,000, ana sace wa mutum 262.5 tasu, lamarin da ya zarta na Ingila da Wales da ake sace wa mutum 220 mota cikin 100,000, kamar yadda alƙaluman da ƙasashen suka fitar ya nuna.

Yawan satar mota da ake yi a Canada ya kusan na Amurka inda ake sace motar mutum 300 cikin kowanne 100,000, kamar yadda alƙaluman 2022 suka nuna.

An samu ƙaruwar satar mota a shekarun baya-bayan nan ne sakamakon matsalar ƙarancin motcin da duniya ke fuskanta, lamarin da ya haifar da ƙaruwar buƙatr motocin.

haka kuma akwai ƙaruwar tsadar wasu nau'in motocin a kasuwanninsu, lamarin da ya sa ɓarayin motar kirar oto suka ƙara ƙaimi sakamakon ƙaruwar buƙatar motocin a kasuwannin duniya, in ji Elliott Silverstein wakilin gwamnati a ƙungiyar dillalan mota ta ƙasar.

To sai dai ya ce yadda akea hada-hada a tasocin ruwan Canada ya sa ɓarayin motar ke cin karensu babau babbaka fiye da sauran ƙasashe.

“Tasoshin ruwan ƙasar sun fi mayar da hankali kan abin da zai shigo ƙasar, saɓanin abin daza a fitar daga ƙasar'', in ji shi, yana mai cewa indai an sanya mota a cikin kwantina da nufin fitar da ita, to da wahala a yi zuzzurfan bincike a kanta.

Shipping containers at the Port of Montreal

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Akan fitar da motocin da ake sata Canada ta tasoshin ruwa kamar wannan da ke Montreal

'Yan sanda sun samau nasarar gano wasu motcin da aka sata.

A watan Oktoban shekarar bara, rundunar 'yan sandan Toronto ta ce cikin wata 11 da ta ɗauka tana binciketa gano mota 1.080 da aka sata, wanda kuɗinsu ya ka dala miliyan 60, inda aka samau ƙorafi fiye da 550.

Haka kuma daga tsakiyar watan Disamba zuwa ƙarshen watan Maris, 'yan sanda da ke kan iyakokin ƙasar, sun gano mota kusan 600 da aka sata a tashar ruwa ta Montreal bayan da aka binciki kontena 400 da ake yi niyyar fitar da su.

To sai irin wannan binciken ba lallai ya iya kakkaɓe matsalar ba, sboda yawan kontenonin da ake fitarwa ta tasoshin ruwan ƙasar, kamar yadda masana suka bayyana.

Kusan kontena miliyan 1.7 aka fitar ta tashar ruwan Montreal a 2023 kawai.

A wasu lokutan jami'an kula da tashar ruwan ba su da ikon duba kontenonin, sannan a wuraren da jami'an kwastam ke iko da su, jami'an da ke kan iyaka ne kawai ke da damar buɗe kontena ba tare da izini ba.

A daidai lokacin da hukumar kula da kan iyakokin ƙasar ta ce tyana fama daƙarancin ma'aikata cikin wani rahoto da ta aike wa gwamnati a watan Afrilu.

Haka kuma ga matsalar rashin amfani da sabbin fasahohi

A cikin watan Mayu, gwamnatin ƙasar ta ce za ta zuba jarin miliyoyin kuɗin don inganta wa hukumar binciken kan iyakoki ta ƙasar aikinta na samaun damar binciken kan iyakokin ƙasar.

Haka kuma gwamnatin ta ce ta za ta bai wa 'yansanda kuɗi domin magance matsalar satar mota a garuruwan ƙasar.

Amma kafin nan, masu mota irinsu Mista LaFreniere na ƙoƙarin yin abin da ya dace domin kare motocinsu daga sata.

Bayan da aka sace masa motarsa kirar Hilux, a yanzu ya samu zarafin maye gurbinta da Toyota Tundra, motar da ya bayyana a matsayin ''mafarkinsa''

A wannan karon ya saka mata matakan tsaro a injinta, ta yadda ɓarawo ba zai iya tayar da ita ba, haka kuma ya sanya mata na'urar bin sawu ko da za a samu ɓacin rana saceta, sannan ya saka ƙarfen maƙulli a sitiyarinsa duk dai a cikin matakan kariya.

Bayan wasu lokuta sai wasu ɓarayi biyu suka je gidansa da nufin sace sabuwar motar . To amma abin bai zo musu da sauki ba, domin sunkasa buɗe ƙofarta, lamarin da ya sa suka fasa gilas ɗin baya domin su shiga ta nan.

Ƙarar fasa gilashin ne ya tayar da Mista LaFreniere inda kuma nan take ya kira 'yan sanda ta amfani da lambar kiran gaggawa, cikin miti huɗu 'yan sandan suka iso gidan nasa, to sai dai ɓarayin sun gudu, ba tare da ɗaukar motar ba.

Ya biya kuɗi aka gyara masa indaɓarayin suka lalata, ya kuma ya sayar da ita.