Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matashin da ke wayar da kan jama'a kan sauyin yanayi a kan keke
Yunusa matashi ne da ya ɗauki nauyin wayar da kan mutane a kan sauyin yanayi.
Yana yin hakan ne ta hanyar tafiye-tafiye zuwa garuruwan da ke arewacin Najeriya a kan keke, inda yake yi wa mutane bayani kan illar sare dazuzzuka da ambaliyar ruwa da fari da sauran su.
Yunusa ya daura aniyar yin wannan gagarumin aiki ne bayan da ya ga illar kwararar hamada ta yi wa ƙauyensa na Ingawa da ke jihar Katsina a Najeriya.