Abin da matakin da Birtaniya ta dauka kan kungiyar IPOB ke nufi

A ranar Juma'ar nan aka samu rahotannin da ke cewa Gwamnatin Birtaniya ta bi sahun Najeriya wajen ayyana ƙungiyar 'yan aware masu neman kafa ƙasar Biafra a kudancin Najeriyar a matsayin ta 'yan ta'adda.
Hakan na nufin Birtaniya ba za ta bai wa mambobin ƙungiyar mafaka ba kamar yadda ta yi niyya a baya.
Tun a 2017 ne gwamnatin Najeriya ta ayyana IPOB a matsayin ta 'yan ta'adda saboda kashe-kashen da hukumomi ke zarginta da aikatawa a jihohin kudu maso gabashin ƙasar da suka haɗa da Anambra, da Abia, da Ebonyi, da Imo, da Enugu.
Matakin na ƙunshe ne cikin kundin ayyukan hukumar harkokin cikin gida ta Birtaniya, inda ta ce ƙungiyar "yan ta'adda ce sakamakon ayyukan tashin hankali da take aikatawa".
Lamarin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin Najeriya ta ce IPOB ce ta kashe wasu sojojinta biyu mace da namiji da ke shirin yin aure a Jihar Imo da ke yankin na kudu maso gabas. Sai dai ƙungiyar ta musanta zargin.
To kan wannan batu ne BBC ta yi tuntubi Audu Bulama Bukarti, wani lauya da ke aiki a cibiyar Tony Blair Institute for Global Change da ke nazari kan tasirin tsattsauran ra'ayi da hanyoyin magance su.
Bulama Bukarti ya yi karin bayani, inda yake cewa Birtaniya ba ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin ta 'yan ta'dda ba.
'Birtaniya ba ta ayyana IPOB a matsayin kungiyar ta'addanci ba'
Audu Bulama Bukarti ya ce akwai kuskure kan yadda kafafen yada labarai a Najeriya ke cewa Birtaniya ta ayyana IPOB a matsayin kungiyar ta'addanci:
"Da farko dai akwai kuskure kan yadda jaridun Najeriya suka ruwaito wannan labarin, domin sun ruwaito cewa Birtaniya ta ayyana IPOB a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, amma ba haka lamarin ya faru ba. Abin da ya faru shi ne, Birtaniya tana da wata manufa kan wadanda take ba mafaka idan suka je can gudun hijira. To cikin wannan takardar da ta fitar ne ta ke bayyana irin mutanen da suka cancanci ta basu mafaka. A bara Birtaniya ta taba cewa 'yan IPOB za su iya samun mafaka idan suka yi gudun hijira daga gwamnatin Najeriya a Birtaniyar."
Sai dai Lauya Bukarti ya ce gwmanatin Birtaniya ta sauya manufofinta kan kungiyar ta IPOB:
"Amma a kwanaki uku da suka gabata, sai suka sauya wannan manufar tasu. Sai suka ce idan 'yan IPOB suka bukaci a ba su mafaka, za ta lura da wasu abubuwa. Daya daga cikin abubuwan shi ne za a rika la'akari da cewa gwamnatin Najeriya ta ayyana kungiyar da yake ciki a matsayin ta 'yan ta'adda. Kaga ke nan ba Birtaniya ba ce ta ayyana su a matsayin 'yan ta'adda, a'a, gwamnatin Birtaniya ta ce ne za ta lura da ayyanawa da gwamnatin Najeriya ta yi ne. Wannan kuma ya bambanta da cewa Birtaniya ta ayyana IPOB a matsayin 'yan ta'adda."
'Tasirin sauya manufar zai yi wa IPOB illa'
"Yanzu idan dan IPOB ya gudo Birtaniya, ko yayi gudun hijira, kuma ya zo ya nemi mafaka, to za a lura cewa a Najeriya kungiyar IPOB ta 'yan ta'adda ce, kuma za a lura ko shi wanda ya zo neman mafaka ko ya shiga cikin ayyukan zubar da jini da kungiyarsa ta ke yi, ko bai shiga ba. Idan ya shiga, sai a hana shi mafaka, idan kuma bai shiga ba sai a duba wasu sharuddan da idan ya cika su za a iya ba shi mafaka."
'Matakin babbar nasara ce ga Najeriya'
Bulama Bukarti ya bayyana dalilai uku da a ganinsa za su taimaki Najeriya kan wannan batu:
"To wannan matakin da gwamnatin Birtaniya ta dauka nasara ce ga Najeriya, domin a bara lokacin da Birtaniyar ta ce za ta rika ba 'yan IPOB mafaka domin karfafa mu su gwiwa, 'yan IPOB sun yi ta murna, kuma lallai wannan matakin ya karfafa musu, domin suna ganin idan suka aikata ta'addanci kana suka tsere zuwa Birtaniya, to za a basu mafaka. Kaga ke nan an sace musu taya da aka ce za a lura da ayyanawar da Najeriya ta yi musu a matsayin 'yan kungiyar ta'addanci."
Ga dalilinsa na biyu:
"Gwamnatin Najeriya ta fara yin nasara wajen gamsar da kasashen duniya su yarda cewa IPOB na ta'addanci a kudu maso gabashin kasar, to lallai 'yan IPOB ne ke yinsa. Domin ita gwamnatin Birtaniya cikin wannan manufar da ta fitar, ta ruwaito wasu cikin hare-haren da IPOB ta kai a cikin wannan shekara, kuma ta ce ya kamata a rika lura da irin wadannan abubuwan. Kaga kenan Najeriya ta fara samun kawayenta na kasa da kasa su amince da ita cewa IPOB kungiyar zubar da jini ce."
A karshe ya ce Najeriya na da damar amfana da matakin na Birtaniya:
"Na uku. Ya kamata gwamnatin Najeriya ta kara wayar wa kasashe kamar Birtaniya da Amurka da Majalisar Dinkin Duniya kai domin dukkansu su ayyana IPOB a matsayin kungiyar 'yan ta'adda. Ayyana sun zai taimaka wajen yakar su da toshe hanyoyin samun kudinsu da kuma toshe hanyoyinsu na gudu daga Najeriya, su je wasu kasashe suna neman mafaka, suna kuma ci gaba da ta'addancinsu a can."










