Ƙasashen duniya sun yi wa Rasha rubdugu kan amincewa da ƴancin kan wasu yankunan Ukraine

Rasha

Asalin hoton, Getty Images

Amurka ta jagoranci tofin Allah tsine a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan matakin da Rasha ta dauka na amincewa da 'yancin kan yankuna biyu na gabashin Ukraine.

Shugaba Vladmir Putin ya rattaba hannu kan wata doka da ta umarci sojojin Rasha su shiga Donetsk da Luhansk, wadanda ke karkashin ikon 'yan aware masu goyon bayan Rasha.

Wakilin BBC ya ce take yanke shugaba Joe Biden ya rattaba hannu kan wata dokar kakaba takunkumin kudi, kan jagororin wadannan yankuna biyu da Rasha ta amince da ikon cin gashin kansu.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield, ta ce shugaba Putin na daukar irin wannan mataki ne ne don ganin iya gudun ruwan kasashen duniya.

Wasu rahotanni da muke samu yanzu haka na nuna cewa ayarin motocin yaki masu sulke na Rasharr sun fara kutsawa yankunan.

A shekara ta 2014 ne kasashen Donetsk da Luhansk suka fara shelanta 'yancin kai jim kadan bayan da Rasha ta mamaye yankin kudancin Crimea na Ukraine.

Ukraine da kawayenta na Yamma sun sha zargin Rasha da tayar da tarzoma tare da aikewa da makamai da mayaka zuwa ga 'yan tawayen, wadanda a yanzu ke rike da yankuna da dama da ake kira Donbas.

Moscow ta sha musanta zargin.

Wakilin BBC a Ukraine ya ce matakin ya zuwa yanzu ba shi ne cikakken harin da mutane da yawa ke fargaba ba, amma ya nuna wani gagarumin ci gaba na rikicin da ke da hadari.