Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar: Babu ranar da ba a kashe mutane a arewacin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Sarkin Musulmin Najeriya Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar na uku ya shawarci 'yan Najeriya da su hada kansu domin kawo karshen ta'addanci a kasar.
A lokacin da yake tsokaci kan matsalar tsaro a Najeriya a taron majalisar hadin kan addinai ta NIREC, Sultan Sa'ad Abubakar ya ce ba lokaci ba ne da mabiya addinai musamman Musulmi da Kirista za su rika zargin juna da yi wa juna barazana ba.
Sarkin Musulmin ya nuna damuwa kan yadda kashe-kashe da sace-sacen jam'a ke ci gaba da afkuwa, amma kuma Musulmi da Kirista sun bige da nuna wa juna yatsa da yi wa juna barazana.
" Dole ne mu daina zargin juna kuma mu hada kai matsawar muna son mu yaki makiyanmu. Idan na ce zan yi magana kan rashin tsaro a arewa babu lokacin da za mu bar dakin taron nan. In ji Sultan.
Ya kara da cewa , "yan kwanakin da suka wuce mun karanta a jaridu yadda aka kona matafiya a bas a Sokoto. Babu ranar da za ta zo ta wuce ba a kashe mutane a Arewa ba, musamman Arewa maso Yamma."
Bugu da kari Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar ya bukaci shugabanni da sauran hukumomin tsaro su hada kai su kuma fahimci girman matsalar tare da magance ta.
"Kar mu yaudari kanmu, abubuwa ba sa tafiya yadda yakamata a Najeriya. Na sha fada a lokuta da dama cewa abubuwa ba sa tafiya yadda ya kamata. Kuma idan dai kasan matsalarka, magance ta ba zai yi maka wahala ba. Saboda haka ya kamata mu san na yi kafin lokaci ya kure mana.
Sarkin ya yi kalaman ne a dai lokacin da 'yan Najeriya ke ci gaba da nuna damuwa, kan kona matafiya sama da 20 da 'yan bindiga suka yi a jihar Sokoto da suka hada da jariri.
Ko a ranar Alhamis rahotanni daga jihar Katsina a arewacin Najeriyar sun ce ƴan bindiga sun kashe wani kwamishina a gwamnatin jihar.
Sannan wasu kafafen yada labaran cikin gida sun ruwaito cewa 'ƴan bindigar sun kashe mutum 16 a lokacin da suke sallah, wasu gwammai kuma sun jikkata a wani hari da suka kai ƙauyen Ba'are na karamar hukumar Mashegu da ke jihar Neja a Arewa ta Tsakiyar kasar.
Shi ma a nasa bangaren Shugaban mabiya addinin kirista a Najeriyar Rabaran Samson Ayokunle ya ce yana mamakin yadda ake garkuwa da mutane a kan hanyoyin Najeriya amma kuma jami'an tsaro ba su iya gano inda aka yi da su.
"Yanzu tafiya daga wani wuri zuwa wani ta mota ta zama babbar kasada. Masu garkuwa sun game ko'ina kuma ba sace matafiya kawai suke yi ba har da kashe su. Saboda haka babu wanda ba zai iya fadawa hannunsu ba," a cewar Rabaran Samson Ayokunle.
A kan haka jagoran mabiya addinin Kiristan ya bukaci hukumomi da su tashi tsaye su yi aikinsu na samar da bayanan sirri, ya kuma bukaci suma al'umma su taimaka wa jami'an tsaron da bayanai.











