Yadda harin ƴan bindiga a Sokoto ya tayar da hankalin 'yan Najeriya

Sokoto

Asalin hoton, Other

Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan matsalar tsaro a arewa maso yammacin ƙasar musamman hare-haren ɓarayin daji da ke kashe mutane da satar mutane.

Yawanci ƴan Najeriyar na nuna fushi ne kan mutanen da ƴan 'yan bindiga suka ƙona a wata motar fasinja lokacin da suka yi musu kwanton-ɓauna a yankin jihar Sokoto.

Fasinjojin sun fito ne daga karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar domin yin ƙaura zuwa wasu yankunan Najeriya, saboda ta'azzarar hare-haren 'yan bindiga a yankin nasu.

Wannan ne ya sa ƙungiyar ci gaban al'ummar Gobirawan Najeriya ta rubuta wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari buɗaɗɗiyar wasiƙa tana neman ya kawo karshen kashe-kashen da ake yi a arewacin kasar wanda ya ƙara jan hankalin ƴan Najeriya.

Wasiƙar ta nuna damuwa kan kashe-kashen mutanen da ake yi ba tare da daukar mataki ba - musamman a kananan hukumomin Sabon Birni da Goronyo da Isa da kuma Shinkafi da ke jihohin Sokoto da Zamfara, inda suka ce ƴan bindiga sun zama tamkar wata gwamnti, ta yadda suke cire shugabannin al'umma su naɗa nasu.

Wannan al'amari ya tayar da hankalin ƴan Najeriya inda Sokoto ke cikin batutuwan da ƴan ƙasar suka fi tattaunawa a shafin Twitter har aka ambaci jihar sau fiye da dubu 14 a lokacin rubuta wannan labari a ranar Alhamis.

Twitter

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto, Sokoto na cikin batun da aka fi tattaunawa a Twitter a Najeriya a ranar Alhamis

Abin da ƴan Najeriya ke cewa

Yawancin ƴan Najeriya na bayyana alhini ne da kuma takaicin ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga duk da matakan da hukumomi ke iƙirarin suka ɗauka.

Yusuf Anka @ankaboy ɗan Najeriya da ke yankin Zamfara ya wallafa a shafinsa na Twitter hotunan lokacin da ake ƙoƙarin binnen gawarwakin mutanen da ƴan bindiga suka ƙona inda ya ce "fasinja 39 aka kone cikin motar bas a Gidan Bawa na jihar Sokoto."

"Duniya ya kamata ta gani, muna buƙatar agaji," in ji shi.

Twitter

Asalin hoton, Twitter

Amina Usman @Amna_alsharaf ta ce: "Abin da ya faru a Sokoto mummunan al'amari ne, ko yaushe wannan matsalar tsaron za ta kawo ƙarshe? Mun yi hasarar rayuka da dama."

Twitter

Asalin hoton, Twitter

A nata ra'ayin @ummeettahh_N ta yi wa mamatan addu'a tare da cewa "abin da ke faruwa a Najeriya ba daɗi ana kashe mutane kamar dabbobi kuma babu abin da ake yi."

Twitter

Asalin hoton, Twitter

@UsmanZannah ya ce: "An ƙona matafiya 42 da ransu a jihar Sokoto kan wata manufar da su suka sani, a jiya buƙatar neman kuɗin fansa ce, yau kuma ta koma ƙona mutane da ransu, wa ya san abin da zai faru ga mutanen da ba su ji ba su gani ba a gobe."

Twitter

Asalin hoton, Twitter

Haka ma batun na ci gaba da jan hankalin masu amfani da Facebook inda labarin harin Sokoto ya razana mutane da dama tare da yi wa mamatan addu'a da kuma neman Allah Ya kawo ƙarshen matsalar ƴan bindiga.

Facebook

Asalin hoton, Facebook