Sojoji sun saki fursunonin siyasa a Guinea

Sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea ranar Lahadi sun saki aƙalla fursunonin siyasa 79 da gwamnatin da suka kifar ta tsare.

Yan siyasar na daga cikin kason farko na mutun 400 da tumɓukakken Shugaba Alpha Conde ya kama a lokacin zanga zangar da ta biyo bayan babban zaɓen da a ka yi bara.

Wannan na zuwa yayin da Shugabannin ƙungiyar raya tattalin arzikin yankin Afrika ta Yamma wato ECOWAS, ke shirin zama a yau Laraba don tattauna batun juyin mulkin a Guinea da kuma maido da mulkin farar hula a Mali.

Wakilin BBC ya ruwaito cewa tun a ranar Talata ne jerin motocin sojojin su ka isa gidajen yarin da fursunonin ke tsare inda suka kwaso kason farko.

Sakin fursunonin kan iya zama matakin farko na samar wa sabuwar gwamnatin sojin a ƙarƙashin Laftanar Kanar Mamady Doumbouya martaba ga idon jama'a.

Tun bayan juyin mulkin na ranar Lahadi Kanar Doumbouya ya yi alƙawarin samar da gwamnatin riƙo da za ta haɗa da sojoji da fararen hula, wadda kuma za ta samar da mulki nagari da kuma ci gaban tattalin arzikin Guinea.

Sai dai kuma bai faɗi lokacin da za su kafa gwamnatin ba, ballantana sadda za a sake sabon zaɓe.

Sojojin sun zargi Shugaba Alpha Conde mai shekaru 83 da cin hanci da rashawa, da son kai da kuma saɓa wa kundin tsarin mulki wanda a cewarsu hakan ya hana ƙasar ci gaba.

Sai dai ECOWAS ta yi barazanar saka wa sojojin takunkumi, kuma a yau Laraba ne Shugabannin ƙungiyar za su yi zama ta kafar intanet don tattauna rikicin siyasa da ke faruwa a ƙasashen Guinea da Mali.

A na sa ran tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan wanda shine mai shiga tsakani kan rikicin Mali zai yi wa ECOWAS bayani kan inda a ka kwana kan batun samar da mulkin farar hula a can.

Masana na hasashen cewa akwai yiyuwar ECOWAS za ta dakatar da Guinea kamar yadda ta yi wa Mali bayan juyin mulki.

Bugu da ƙari za su iya ƙaƙaba wa sojojin Guinea takunkumi.

Masu sharhin sun kuma bayyana cewa tsawon shekaru Ƙungiyar Tarayyar Afrika AU da kuma ECOWAS har ma da Majalisar Ɗinkin Duniya sun gaza ɗaukar mataki kan yadda Shugabanni a Afrika ke maguɗin zaɓe don ci gaba da mulki.

Kuma a cewarsu hakan ne ya dawo da guguwar juyin mulki da sauran rikice-rikicen siyasa a nahiyar.