Salihu Tanko Islamiyya: Wata guda da sace daliban makarantar Islamiyya a jihar Neja

Salihu Tanko Secondary School

Asalin hoton, Principal of Salihu Tanko Secondary School

A ranar Talata ne daliban makarantar Salihu Tanko Islamiyya da ke garin Teigna a jihar Neja suke cika wata guda a hannun yan bindigar da ke ci gaba da garkuwa da su.

Tun a ranar 30 ga watan Mayun da ya gabata ne wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka yi wa makarantar Islamiyya tsinke sannan suka yi awon gaba da dalibai da adadinsu ya kai 136, kamar yadda shugaban makarantar ya shaida wa BBC.

Har yanzu ba a kai ga ceto wadannan yara ba, ko da yake wasu daga cikin malaman da aka sace mutum uku sun kubuta.

A gefe guda kuma iyayensu na ci gaba da zaman zullumi, da kuma fatan dawowar 'ya'yansu gida.

Wasu daga cikin iyayen yaran sun shaida wa BBC cewa suna cikin damuwa da fargabar rashin sanin halin da 'ya'yansu ke ciki a hannun 'yan bindigar.

''Wannan kudi da suka ce dole sai an ba su sannan za su saki yaran nan, ba mu da kudi ban taba mallakar miliyan 5 ba bare kuma miliyan 100, muna mika lamarinmu ga Allah ya mana magani,"in ji mahaifin wasu daga cikin daliban.

Ita ma wata uwa da 'ya'yanta har uku ke hannun 'yan bindigar, ta ce ba ta san halin da yaran ke ciki ba sai dai fatan Allah ya kubutar da su.

Shugaban makarantar islamiyyar, Abubakar Alhassan, wanda kuma yake magana da yan bindigar daga bisani kuma ya sanar da iyayen yaran halin da ake ciki, ya ce su na ci gaba da tattaunawa da 'yan bindigar.

Ya kara da cewa cikin kudin da suka bukata miliyan 25 kadai suka tara yana mai cewa "'yan bindigar suna yi musu barazana."

A halin da ake ciki dai hankali ya karkata ne ga gwamnatin jihar domin ganin an kubutar da wadannan dalibai da suka cika wata guda a hannun yan bindigar cikin halin rashin tabbas.

BBC ta tuntubi sakataren gwamnatin jihar Naija Ahmad Matane, don jin halin da ake ciki game da kokarin ceto wadannan dalibai, inda ya ce gwamnati na bakin kokari domin ganin an kubutar da daliban.

Matsalar satar dalibai a Najeriya dai na ci gaba da janyo babbar barazanar ga bangaren ilimi a Najeriya, wanda dama rahotanni ke nuni da cewa yaro 1 cikin 2 ne ke zuwa makaranta a arewacin kasar, wato dai inda matsalar ta fi kamari.