Sace-sace a Kano: Mazauna jihar na kokawa kan satar allunan maƙabartu

Ana zargin masu sana'ar gwan-gwan ko tsince tsincen ƙarafa da cire allunan
Bayanan hoto, Ana zargin masu sana'ar gwan-gwan ko tsince tsincen ƙarafa da cire allunan

Masu kula da wata maƙabarta da ke Gwale a jihar Kano a arewacin Najeriya na ci gaba da kokawa kan irin yadda suka ce ana samun ƙaruwar sace allunan alamomi na kaburbura.

Masu kula da makabartar sun shaidawa BBC cewa tun kusan watanni uku baya ne suka lura ana yi wa shaidar da ake sakawa ƙaburbura ɗauki ɗai-ɗai.

Yayin da wasu kuma allunnan suke ganinsu a lanƙwashe idan gari ya waye lamarin dake nuni da cewa an yi ƙoƙarin cirewa ne amma hakan ta gagara.Wakilin BBC a Kano Khalifa Shehu Dokaji wanda ya je maƙabartar ƙafa da ƙafa, ya ce ya ga kaburbura da dama da aka cire allunansu aka tafi da su, wasu kuma a allunan alamarsu lauye.

Ɗanjuma Labaran na daga cikin masu haƙar kabari a wannan makabarta ta Dandolo, ya kuma bayyanawa BBC cewa tun da farko sun fara samun koke ne daga wajen jama'a dangane da ɓatan allunan da suka sanya a kabuburan ƴan uwansu da aka binne a wannan maƙabarta.

''Muna zargin ƴan gwan-gwan ne ke zuwa su kwashe su, don sune suke yawo a nan wajen, sukan zo su wuce, kuma akwai gefen makabarta da suke irin waɗannan ayyukan'' in ji Malam Ɗanjuma.

Sai dai wasu masu sana'ar ta tsince-tsincen kayan ƙarafan wato gwangwan a wannan yankin, sun musanta wannan zargi da ake yi musu.

Hotuna : Yadda aka cire wasu allunan

Wasu ƙaburbura da aka cire alluansu kenan
Bayanan hoto, Kamar yadda kuke iya gani a wannan hoto, babu wata alama a kan waɗannan kaburbura koh ? to a zahiri a baya da akwai, cirewa aka yi aka yi awon gaba da su
Ana zargin masu sana'ar gwan-gwan ko tsince tsincen ƙarafa da cire allunan
Bayanan hoto, Ana zargin masu sana'ar gwan-gwan ko tsince tsincen ƙarafa da cire allunan
Wani kabari da aka so cire alamarsa
Bayanan hoto, Ga kuma allon alamar wani kabari da shi kuma aka so tunɓukewa da ƙarfin tuwo amma hakan ta gagara, saboda ya kafu sosai, kamar yadda kuke iya gani ga shi nan an tafi an bar shi a lanƙwashe
Yadda wasu suka fara kewaye kaburburan an uwansu da ginin kankare kenan domin gujewa yin alamar da za a iya cirewa
Bayanan hoto, Nan kuma yadda wasu suka fara kewaye kaburburan ƴan uwansu da ginin kankare kenan domin gujewa yin alamar da za a iya cirewa a tafi da ita

Jihar Kano dai na da tarin maƙabartu da dama da babu hasken wutar lantarki, abin da wasu ke ganin cewa kan taimaka wajen bada mafaka ga masu zuwa su aikata miyagun laifuka a ciinsu.

A wasu lokuta a baya, an sha samun waɗanda ke shiga maƙabartu a jihar da tsakar dare don tone gawarwaki, su ciri wasu sassan jikinsu da wata mummunar manufa.

Jihar Kano na da mai bawa gwamna shawara na musamman kan lamuran da suka shafi maƙabartu, amma duk da haka wasu ƴan jihar na kokawa kan yadda ake samun matsaloli irin waɗannan