Matashiya a Kano ta kashe yayanta da wuka kan ya hana kida

'Yan sanda
Bayanan hoto, Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta mika batun ga 'yan sandan ciki domin bincike

Sa-in-sa ce dai ta kaure tsakanin matashiyar mai shekara 19 da yayanta mai shekara 30 ana cikin shagalin bikin wata 'yar uwar tasu daban.

Wata sanarwa da rundunar 'yan sandan jihar Kano ta fitar ta ce matashin ya nemi da a dakatar da kide-kiden da ake yi a wurin bikin ne, al'amarin da bai yi wa kanwar tasa dadi ba, inda ta dauko wuka ta daba masa a wuya.

Daga nan ne labari ya samu 'yan sandan suka kuma bazama zuwa wurin inda samu matashin kwance cikin jini male-male.

Daga nan kuma suka garzaya da shi zuwa asibiti, inda likitoci suka bayar da tabbacin mutuwarsa.

Yanzu haka dai Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Cp Ahmed Iliyasu ya bayar da umarnin kai batun zuwa hannun 'yan sandan ciki na CID a jihar.

A baya-bayan nan ana yawan samun karuwar matasan da ko dai su kashe wani ko kuma su kashe kansu, al'amarin da masana ke cewa ya kamata a yi wa tufkar hanci tun kafin lamarin ya ta'azzara.

Masu nazarin zamantakewar dan adam irin su Farfesa Sadiq Radda na Jami'ar Bayero ta Kano sun zayyana dalilai guda bakwai da suka ce su ne suke jefa matasa daukar irin wannan hukunci:

  • Shaye-shaye
  • Kuncin Rayuwa
  • Takurawar iyaye
  • Takurawar abokai
  • Takurarwar makwabta
  • Fina-finai
  • Kafofin sa da zumunta na zamani
  • Rashin hakurin matasa kan rayuwa