Covid-19: Yadda Janar 18 na sojin Najeriya suka kamu da cutar korona

Manyan jami'an sojin Najeriya

Asalin hoton, DHQNIGERIANARMY

Bayanan hoto, Bayanai sun nuna cewa Janar-Janar din na sojin Najeriya sun kamu da cutar korona ne a wurin taron manyan jami'an soji da aka yi a Abuja

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa manyan jami'anta 26 sun kamu da cutar korona.

Sanarwar da daraktan watsa labaran rundunar Kanar Sagir Musa ya fitar ta ce gwajin da aka yi musu ne ya nuna cewa sun kamu da cutar.

Amma wasu rahotanni sun nuna cewa a cikinsu har da janar-janar 18.

Sanarwar ta ƙara da cewa ɗaya daga cikinsu, Manjo Janar JO Irefin wanda shi ne kwamandan bataliya ta 6 da ke birnin Fatalwal, ya sanar da cewa yana fama da zazzabi da tari a ranar da aka yi taron ƙaddamar da sashen yaƙi da laifukan intanet na rundunar, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya halarta ta bidiyo a ranar 7 ga watan Disamban 2020.

A lokacin ne aka ɗauke shi zuwa asibitin soji rundunar sojin Najeriya da ke Fatakwal, daga bisani kuma a ranar Laraba 8 ga watan Disamba aka ɗauki samfurinsa domin yin gwajin cutar korona.

A dai wannan rana ce kuma sakamakon gwajin ya nuna cewa yana ɗauke da cutar ta korona, domin haka ne aka kai shi cibiyar killace wadanda suka kamu da ke Gwagwalada a Abuja babban birnin ƙasar.

Sanarwar rundunar ta ƙara da cewa bayan da sakamakon Janar din ya nuna cewa yana dauke da cutar korona, babban hafsan sojin kasa na Najeriya ya bayar da umarnin dakatar da taron, sannan dukkanin waɗanda ke halartar shi su kebe kansu, bisa ka'idar dokokin Najeriya na yaki da cutar korona.

Ta ƙara da cewa an yi wa manyan jami'an rundunar soji 417 daga cikin mahalarta taron gwaji zuwa yanzu, sannan sakamakon 26 daga cikinsu ya nuna cewa sun kamu da cutar korona cikinsu har da janar 18.

Ko hakan na iya shafar yaki da matsalar tsaro ?

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau

Asalin hoton, AFP

Wannan na zuwa ne yayin da Najeriya ke fama da matsalar tsaro, kama daga kan hare-haren ƴan Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar da na masu satar mutane a arewa maso yammaci.

Dakarun sojin Najeriya na kan gaba a yaƙi da dukkanin waɗannan matsaloli, amma kamar yadda aka sani tafiya ba ta yiwuwa ba tare da shugabanci ba.

A cewar wani masanin harkokin tsaro a Najeriyar Manjo Bashi Shuaibu Galma, "Babu wani abin damuwa, domin kamar sauran ma'aikatu, akwai mataimaka da za su iya ci gaba da gudanar da ayyukan da suke yi.

"Akwai Janar-Janar da ko ba su kai matsayinsu ba za su iya ci gaba da jan ragama, domin cike gibin da hakan ka iya haifarwa" in ji shi.

Sai dai Dakta Kabiru Adamu, wani masanin harkokin tsaro a shi ma Najeriya ya kalli batun ne ta wani ɓangaren, inda ya ce akwai sakaci daga jagororin rundunar da har suka shirya taron da ya zamo sanadin yaɗuwar cutar yayin da ake tsaka da fama ita.

"Akwai ƙa'idoji na yaki da annobar korona da aka shimfiɗa waɗanda ba shakka an take su a yayin taron", a cewarsa.