Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rashin tsaro: Shin ko sojojin haya na iya sama wa Najeriya mafita?
Masana sha'anin tsaro na ganin cewa amfani da sojojin haya ba zai taɓa zama mafita ga taɓarɓarewar tsaron Najeriya ba.
Masu nazari kan harkokin tsaro irin su Bulama Bukarti, sun ce wannan mataki ba zai zama mafita ba bayan shawarwarin da wasu 'ƴan Najeriya ke bayarwa na amfani da sojojin haya domin magance matsalar tsaron da kasar ke ciki.
Mummunan kisan gillar da ake zargin ƙungiyar Boko Haram ta yi wa gomman manoma a jihar Borno, da ke arewa maso gabashin Najeriya ne ya janyo zazzafar muhawara kan ko dakarun sojin ƙasar da gaske za su iya murƙushe 'ƴan ta-da-ƙayar-bayan.
Cikin masu irin wannan tunani har da Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zullum, wanda ya lissafa waɗansu hanyoyi da yake ganin cewa matuƙar gwamnatin ƙasar ta bi su, to ba shakka za ta ci galaba kan Boko Haram cikin gaggawa.
Cikin hanyoyin kuwa har da ɗauko sojojin haya da za a yi jinga da su, kuma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, su zo su murƙushe Boko Haram, su wuce.
'Sojojin haya haɗari ne'
Sai dai Bulama Bukarti mai nazari kan matsalolin da suka shafi ta'addanci a nahiyar Afirka, ya ce hakan ba zai kawo sauki ko daƙile matsalolin tsaron Najeriya ba.
Ya ce akwai buƙatar ayi taka tsan-tsan da irin wadannan shawarwari, saboda sojojin haya ba na ƙasa ba ne dauko su ake daga waje.
Bukarti ya ce, a lokuta da dama suna tafka laifukan keta haƙƙin bil adama kamar yadda aka gani a galibin ƙasashen da suka yi amfani da irin wadannan sojoji.
"Sojojin haya asali mutanen ne da kamfani ke dauka ya horar a kuma ba su makamai, don haka da rikici da yaƙi suke cin abinci kuma duk inda suka je ba a jin daɗinsu."inji Bukarti.
'Ba su da gurbi a kundin tsarin Najeriya'
Sojojin haya ba su da gurbi a kundin tsarin mulkin Najeriya, sai dai idan za a fasalta kundin ne domin samun hurumin ɗauko su, in ji Bukarti
Ya ce: "Ana jita-jita an yi amfani da irin waɗannan sojoji a lokacin tsohon shugaba Goodluck Jonathan, to ni a nawa binciken bai nuna hakan ba, watakil an ɗauko su ne bisa saɓawar kundi".
Barrister Bulama ya ce duk da cewa sojojin haya na zuwa da kayayyakin aikinsu wani lokaci a kan ɗan basu wasu kayayyakin kuma a biya su.
Tsadar yaƙi
Barrister Bulama ya kuma shaida cewa amfani da sojojin haya na da matukar tsada a yaƙi, saboda ana ware maƙudan kuɗaɗe wajen ɗauko su,
A cewarsa mafita ita ce horar da ƴan ƙasa matasa da 'ƴan ƙato da gora dan kare ƙasa.
Barrister ya ce akwai dabaru da dama da za a iya amfani da su wajen murkushe ƴan ta'adda da kawo ƙarshen matsalar tsaron Najeriya ba lallai sai da sojojin haya ba.
Sai dai Bukarti ya yi gargaɗin cewa ko da za a horar da matasan ƙasa a basu makamai to a ɗauki masu ilimi.
Ya ce akwai illa ba wa matasa marassa ilimi makamai don su ma na iya amfani da wannan dama wajen sake jefa ƙasa cikin tasku.
Mafita
Mahukuntan Najeiya sun sha cewa sun murƙushe Boko Haram, kafin mayaƙanta su sake fitowa su tafka wata ƙazamar aika-aika.
A yanzu dai, mutane da dama na ganin lokaci ya yi da gwamnatin Najeriya za ta tunkari gaskiyar lamari game da yaƙi da Boko Haram, ko da za ta kai ƙasar ne ga ɗauko sojojin haya daga waje, don kawo ƙarshen wannan rikici da ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa.
Ko wa na bada shawarwarin mafita wanda yake ganin na iya samar da kwanciyar hankali a ƙasar.
Abin jira a gani shi ne ko gwamnati za ta amsa ta dauki shawarwari da ake bata ko kuma zata ɓullo da wasu dabarun murkushe masu tada ƙayar bayan.