EndSars: Matsaya 11 da Majalisar Ƙoli ta Malaman Musulunci ta ɗauka kan rikicin

Majalisar Ƙoli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya ta yi kira ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta tashi haiƙan don daƙile masu yunƙurin yaɗa fitina da sunan zanga-zangar EndSARS.

Ta bayyana hakan ne yayin wani taro na manema labarai da ta gudanar a Abuja, inda ta cimma wasu shawarwari 11, da ta ce ya kamata a bi don kawo ƙarshen halin da ƙasar ke ciki a wannan lokaci.

Wakilin babban sakataren majalisar Sheikh Muhammad Bin Uthman, limamin Masallacin Juma'a na Sahaba da ke Kano, ya shaida wa BBC cewa dole ne gwamnati ta ɗauki gabarar hukunta duk wanda aka samu da hannu a tada yamutsin da ya biyo bayan zanga-zangar a wasu jihohin kasar.

Ya yi zargin cewa an kashe, tare da ƙona wuraren kasuwancin Musulmi da dama, amma babu wanda ya ce wani abu dangane da al'amarin.

Sannan ya yi kira ga ƙasashen duniya da ke ci gaba da martani dangane da zanga-zangar su guji yanke hukunci alhalin ba su ji daga kowanne ɓangare ba, domin hakan na iya haifar da rashin adalci.

''In yi laifi a ƙyale ni, shi ke miƙa goron gayyata ga wani, don haka a binciko waɗanda suka haifar da yamutsi a hukunta su, ko su wane ne,'' in ji Sheikh Bin Uthman.

Ga jerin matsayar majalisar

1. Ba za mu naɗe kafa muna kallo wasu na amfani da sunan zanga-zanga wajen kai wa jama'ar da ba ruwansu hari a sassan Najeriya ba.

2. Muna kira ga ƙungiyoyin ƙasashen waje su zo su ga irin ɓarnar da aka yi ta kisan jami'an tsaro da lalata ƙadarorin gwamnati da sunan zanga-zanga.

3. Muna jajanta wa iyalan 'yan sandan da suka rasa rayukansu a hannun waɗannan ''ɓata gari'', muna Allah wadai da irin kisan wulakancin da aka yi wa waɗannan jami'an tsaro ba tare da sun aikata laifin komai ba.

4. Dole ne gwamnati ta ɗauki mataki don kawo karshen abubuwan da ke faruwa, sannan a tabbatar da daukar mataki a kan masu haifar da wannan yamutsi, sannan ta tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

5. A tabbatar da an biya iyalan wadanda suka mutu diyya.

6. Gwamnati ta aiwatar da alkawarin da ta dauka na sauya tsarin aikin 'yan sanda, sannan ta amsa buƙatun da al'ummar Najeriya suka bijiro da su dangane da wannan al'amari.

7. Muna kara kira ga gwamnati ta fahimci nauyin da ke kanta kamar yadda yake kunshe a sashe na biyu na kundin tsarin mulkin Najeriya, da ya ɗora mata nauyin kare rayuka da dukiyoyin jama'a da kuma sama musu walwala. Musulmi sun fi kowa shan wahala a Najeriya, kama daga kan abin da ya shafi tsaro da da rashin aikin yi.

8. Muna kira ga kungiyoyin kasashen waje su kaucewa rashin adalci, su riƙi gaskiya musamman wajen daukar matsaya dangane da wannan batu.

9. Dole ne duk mu dawo hayyacinmu, mu koma ga Allah S W A, mu nemi yafiyarsa, daga dukkanin zunuban da muka aikata.

10. Muna kira ga masallatan Juma'a su yi addu'o'in zaman lafiya a ranar Juma'a, sannan a kaucewa rikici da saɓa doka da kuma tabbatar da zaman lafiya.

11. Daga karshe muna kira ga al'ummar Musulmi su tsananta addu'ar neman zaman lafiya, da hadin kai da aminci, sannan a fara alƙunutu da sauran addu'o'i musamman a salloli biyar, mu nemi Allah ya shiga lamarinmu.

Ƙarin labarai masu alaƙa

A samarwa matasa mafita

Majalisar ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya ta sama wa 'yan kasar musamman matasa mafita, ta yadda za su san ana damawa da su a tafiyar da harkokin gwamnati.

Sheikh Muhammad Bin Uthman ya ce babu abin da matasa ba za su iya yi ba, matsawar aka bar su cikin mawuyacin hali, ciki kuwa har da ta'addanci.

''Duk ƙasa idan ba ta samar da abubuwa biyar ba to ba gwamnati ba ce, samar da aikin yi, da samar da tsaro da samar da ilimi nagartacce, da samar da harkar kula da lafiya da kuma samar da kayan more rayuwa''.

Ya ce talauci ya kai in da ya kai a ƙasar nan, don haka wannan ne ke ƙara janyo duk matsalolin da aka tsinci kai a ciki.

Majalisar ta kuma bayyana damuwa dangane da yadda ake ƙin bayar da muhimmanci ga kisan jama'a da ake yi a yankin Arewa, tana bayar da misali da kisan mutum 20 a Zamfara yayin da ake tsaka da zanga-zangar, amma kuma babu wanda ya ji.

Majalisar malaman ta kuma koka kan yadda wasu jagororin addinin kirista suka dinga tunzura mabiyansu maimakon gargadinsu kan lamarin.

''Abin takaici ne yadda wasu malaman addinin kirista suka dinga yin kalaman da ka iya ƙara tunzura mabiyansu maimakon gargaɗinsu kan gujewa haddasa rikici.

''Mun yi amanna cewa irin waɗannan kalamai, da a wasu lokutan ake yi a kan mumbari kan rikiɗe su zama rikici addini da na ƙabilanci da muke gani a yau,'' in ji majalisar.

Abin da ya faru

Zanga-zangar ta EndSARS da aka yi ta yi a wasu jihohin Najeriya ta janyo asarori da dama, kama daga kan lalata gine-ginen gwamnati da na ɓangarori masu zaman kansu a wasu jihohi musamman Legas.

Hukumomi sun baza jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma domin shawo kan lamarin, sai dai tashin hankali ya ci gaba da ƙaruwa har zuwa ranar Laraba.

Lamarin ya ƙazanta daga bisani, bayan da jami'an tsaro suka buɗe wa wasu masu zanga-zanga wuta a Lekki da ke jihar Legas, abin da ya janyo mutuwa da jikkatar mutane masu yawa.

An bayar da rahotannin samun asarar rayuka da dukiyoyin jama'a, amma da yake gabatarwa al'ummar jihar jawabi, gwamnan Legas Sanwo Olu, ya ce ba wanda aka kashe, sannan ya ziyarci wadanda ke kwance a gadon asibiti don duba halin da suke ciki.