EndSARS: Fatawar Shiekh Dahiru Bauchi kan zanga-zangar Najeriya

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya Shiekh Dahiru Bauchi ya yi kira da a kai zuciya nesa kan zanga-zangar EndSARS a ƙasar.

A hira da BBC, shehun malamin ya ce zanga-zangar barazana ce ga zaman lafiya a Najeriya da ke fama da matsalolin Boko Haram da ƴan bindiga masu fashin daji da satar mutane.

An shafe fiye da mako biyu ƴan Najeriya - yawanci matasa na zanga-zangar ƙyamar rundunar ƴan sanda da ke yaƙi da fashi da makami da ake kira SARS.

Gwamnati ta rusa rundunar ta SARS domin biyan buƙatun masu zanga-zangar, amma kuma yanzu zanga-zangar ta rikiɗe ta koma tashin hankali a Najeriya.

Jihohin Legas da Abia da Ekiti da Filato da Imo da Osun an sanya dokar hana fita ta tsawon sa'oi 24.

Amma matakin a Legas ya haifar da tashin hankali inda akai ta yaɗa hotunan bidiyo a kafofin sadarwa na intanet da ke nuna yadda sojoji suka buɗe wa masu zanga-zanga wuta a Lekki. Ko da yake sojojin Najeriya sun ƙaryata.

Shiekh Dahiru Bauchi ya ce ba a kashe wuta da wuta - da ruwa ake kashe wuta. "Muna kira ga gwamnati ta sasanta da masu zanga-zanga, sasantawa ta zaman lafiya ba ta ƙarfi ba," in ji Shiekh Dahiru Bauchi.

Ya ce akwai buƙatar gwamnati ta dinga lura da haƙƙin ƴan kasa da take mallaka ta biya buƙatunsu.

Sannan ya yi kira ga masu zanga-zanga da su dakatar da zanga-zangar domin duk abin da suke nema ba za su samu ba ta hanyar zanga-zanga sai dai ƙara lalacewar abubuwa.

Shehin Malamin ya ce abin da aka raina na zaman lafiya a Najeriya za a iya a rasa shi.

Ya ƙara da cewa yadda abubuwa ke tafiya ba zai haifar da ɗa mai ido ba a Najeriya, ya kamata gwamnati ta kiyaye.

"Gwamnati tana da kunne da ido - kunnenta yana jin abin da ƴan kasa ke faɗa, idonta kuma yana kallon abin da mutane suke ciki na matsin rayuwa da rashin abinci da ayyukan yi da rashin kare rayukan mutane," a cewar Dahiru Bauchi.

Dahiru Bauchi ya saba magana kan matsalar tsaro

Shiekh Dahiru Bauchi, ya yi shuhura wajen gaya wa shugabannin Najeriya gaskiya.

Malamin ya taɓa kai ziyara fadar Shugaba Buhari kan matsalar tsaron da ta addabi yankin arewacin ƙasar.

Ya kuma taɓa fitowa ya soki gwamnati kan rikicin makiyaya da manoma, matsalar da ake ganin ta haifar da ƴan bindiga masu fashin daji a yankin arewa maso yammaci.

Ƙarin labarai da za ku so ku karanta