Masu zanga-zanga a Mali sun sake komawa kan tituna

An sake yin wata zanga-zangar adawa da gwamnati a Bamako babban birnin kasar Mali.

Dubunnan mutane ne suka yi zanga-zangar suna kira ga Shugaba Ibrahim Boubakar Keita, da ya sauka daga karagar mulki.

Suna nuna fushi ne da yadda hare-haren masu ikirarin jihadi ke ci gaba karuwa, baya ga matsalar cin hanci da rashawa da suke zargin ta addabi kasar.

Shugaban masu zanga-zangar, dan ra'ayin mazan jiya Mahmud Dicko, ya fada wa taron cewa za su yi nasarar dawo da martabar kasar.

Ya ce zai sake yin kokarin tursasawa shugaban ya sauka.

Yunkurin sulhu da shugabannin yankin Afrika suka yi bai kai ga gaci ba, bayan da masu zanga-zangar suka yi shuri da kiran kafa gwamnatin gamin gambiza

Me ya sa mutane ke zanga-zanga?

Wannan zanga-zanga ita ce ta uku tun cikin watan Yuni.

Zanga-zanga ta fara ne bayan ƙawancen 'yan adawa sun yi watsi da sassaucin da Shugaba Keita ya ɓullo da shi don kawo ƙarshen rikita-rikitar siyasa kan dambarwar zaɓen 'yan majalisar dokoki a watan Maris.

A makon nan 'yan adawa sun ce tafiyarsu ta jingine buƙatarta ta neman Shugaba Ibrahim Boubakar Keita ya sauka. Sai dai har yanzu ta buƙaci gudanar da zanga-zanga saboda tana neman ƙarin sauye-sauye.

Keita ya hau mulki wa'adi na biyu tsawon shekara biyar ne a 2018 sai dai yana fuskantar ƙarin adawa game da bazuwar tarzomar masu iƙirarin jihadi da kuma matsalar tattalin arziƙi.

Al'ummar Mali dai na fatan cewa masu iƙirarin jihadi, waɗanda su ne da hannu wajen ƙaruwar rikici a yankin arewa da tsakiyar ƙasar, ba za su yi amfani da wannan turka-turka da ta taso ba.