Kano: An yi garkuwa da ɗiyar ɗan majalisa a jihar

Wasu masu garkuwa da mutane sun sace ƴar gidan ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Ɗambatta, Alhaji Murtala Musa Kore da tsakar daren Asabar.

Ƴan bindigar sun ɗauki Juwairiyya ne da misalin ƙarfe 3:00 na dare bayan sun yi yunƙurin yin garkuwa da mahaifinta amma sai suka tarar ba ya nan, kamar yadda ɗan uwanta Jamilu ya shaida wa BBC.

Jamilu ya ce mahaifinsu yana birnin Kano a lokacin da ƴan bindigar suka isa gidan nasu da ke ƙauyen Kore a Ƙaramar Hukumar Ɗambatta.

Juwairiyya Murtala Musa mai shekara 17, ɗaliba ce 'yar aji biyar a makarantar sakandare ta Government Secondary School Jogana kuma ita ce 'yar auta a wurin mahaifin nata.

"Mutum uku ne suka fara shigowa cikin gidan amma ba mu san yawan waɗanda suka tsaya a waje ba," in ji Jamilu.

"Sun ajiye motarsu nesa da gidan, saboda haka ba mu iya ganin inda suka yi ba."

Ya ƙara da cewa da farko sun kama yayan mahaifin nasu kuma suka ɗaure shi bisa zaton shi ne Honarabul Murtala.

Ana dai ci gaba da samun matsalar garkuwa da mutane a Najeriya musamman jihohin arewa maso yamma.

Duk da cewa ba a cika samun rahotannin garkuwa da mutane a jihar Kano ba kamar takwarorinta na sauran yankin, masana tsaro na ganin cewa idan ba a yi maganin abin ba bayan lokaci kaɗan wannan matsala kan iya mamaye ko ina.

Ko a kwanakin baya sai da 'yan bindiga suka sace matar wani ɗan majalisa a jihar Jigawa da ke makwaftaka da jihar Kano.