Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An sace matar dan majalisa a Jigawa
Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da matar dan majalisa mai wakiltar Miga a jihar Jigawa Haruna Aliyu a gidansa da ke jihar.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda reshen jihar ta Jigawa DSP Abdu Jingiri ya shaida wa BBC cewa wasu 'yan bindiga uku ne suka shiga gidan dan majalisar suka yi garkuwa da matarsa mai suna Zahra'u Aliyu.
Ya shaida cewa 'yan bindigar sun shiga gidan ne da asubahin ranar Asabar misalin karfe 5:00.
Ya kuma ce 'yan bindigan ba su karbi kudi ba yayin da suka shiga gidan.
Matsalar garkuwa da mutane a jihar Jigawa na kara karuwa inda a 'yan kwanakin nan ake garkuwa da iyalen manyan jami'an gwamnati.
Ko a kwanakin baya sai da aka sace mahaifiyar wani dan kasuwa da kuma mahaifiyar wani tsohon dan majalisar jiha wadanda duka sun samu kansu bayan an biya makudan kudade.
Haka zalika an taba sace wani ma'aikacin hanya farar fata a jihar ta Jigawa.
Matsalar garkuwa da mutane dai ta fi kamari ne a jihohin arewa maso yammacin kasar musamman Katsina da Kaduna da jihar Zamfara.
Ko a wannan makon sai da rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da sace wasu dalibai hudu na Kwalejin addinin Kirista ta Good Shepherd Major Seminary School da ke garin Kakau da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
A jihar Katsina kuwa, a ranar Laraba ne 'yan bindiga suka yi garkuwa da wasu jami'an kwastam guda biyu a wani shinge da ke kauyen Dan-bedi a yankin karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina mai iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Kwanaki kadan kafin afkuwar lamarin na Jibiya, masu garkuwa da mutanen sun yi awon gaba da fasinjoji kimanin 30 a karamar hukumar Batsari a jihar ta Katsina.
Haka zalika suka kashe wani malamin jami'a a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.