Minista ya nemi a halarta cinikin tabar wiwi

Lokacin karatu: Minti 1

Ministan Kudi na Afirka ta Kudu Tito Mboweni, ya yi kira da a halarta cinikayyar tabar wiwi domin samun kudaden shiga a kasar.

Ya yi wannan kira ne a shafinsa na Twitter inda ya bayyana cewa zai kai wannan kudurin gaban majalisa.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bayyana cewa jama'a na son a yi hakan, sai dai kuma ya yi shagube ga likitoci inda bai fito fili ya bayyana ra'ayin likitocin ba amma da alamu ba lallai su yi na'am da batun halartar tabar ba.

Ya kuma wallafa wasu jerin hotuna na yadda aka shuka tabar wiwin har ta fara girma.

A 2019, Kotun Afirka ta Kudu ta yi sassauci wajen hukunci ga wadanda ake samu da laifin mallakar tabar ko amfani da ita da kuma noma ta.

Duk da sassaucin, cinikin wiwi a kasar haramun ne.

Akwai wasu kasashe da suke da sassauci kan tabar wiwi musamman wajen amfani da ita wajen magani, wasu kasashen kuma sun haramta amfani da ita ko ta wace hanya.

Akwai kuma wasu kasashe da ke da tsatsauran hukunci kan tabar wiwi wanda hukuncin kan iya kai wa ga kisa ko kuma daurin shekaru masu yawa ga mai laifi.