Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ganduje ya sha alwashin mayar da almajirai Makarantar Boko
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya bayar da sanarwar hana almajirci da aka dauki lokaci ana yi a jihar.
Gwamnan ya ce yaran da aka tura su almajirci wasu jihohin da aka dawo da su jihar za a mayar da su Makarantar Boko.
Almajirai sama da 1,000 ne dai aka dawo da su Kano daga jihohin da ke makwabtaka da ita, sannan gwamnatin jihar ta mayar da almajirai 1,172.
Gwamantin ta Kano ta ce tuni ta sada yara almajirai 'yan asalin jihar su 723 da iyayensu, sannan akwai guda 28 da suka kamu da cutar korona, wadanda suna can a killace a wajen killace masu dauke da cutar da ke jihar.
Gwamnatin ta Kano dai ta ce ta dauki matakin hana almajiricin ne sakamakon fitowa da tsarin bayar da ilimi kyauta kuma tilas ga daukacin yaran jihar da ta yi, abin da ya zama wajibi almajiran su je makaranta.
Murtala Sule Garo shi ne kwamishin kananan hukumomi sannan shugaban kwamitin mayar da almajirai a Kano, ya kuma gwamnati ta kammala dukkan shirye-shiryen shihgatr da almajiran jihar na kai su Makarantun Bokon.
To ko yaya su malaman makarantun tsangaya suka ji da wannan mataki na gwamnan na Kano na hana almajirici jahar? Tambayar kenan da BBC ta yi wa shugaban kungiyar mahaddata Alkur'ani ta Najeriya da ke Kano, Dr. Lawi Gwani Danzarga, ya kuma ce "Ka san ita hukuma idan ta ce za ta yi abu to tana da karfi da ikon yi, amma ya kamata a yi adalci ga wadanda ake jagoranta.
"Sai dai mu ba a mana gatan da ake yi wa karatun boko.''
Tun gabanin wannan mataki na gwamnatin Kano na hana almajirici a Kano, gwamnatin jihar sai da ta killace almajirai 2,000 a garuruwan Gabasawa da Karaye da Kiru, kafin daga bisani ta mayar da su zuwa jihohinsu da kauyukansu.
A cikin watan Fabrairun shekarar da muke ciki ne gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da koyar da darasin lissafi da na Turanci a makarantun tsangayu a Kano, wanda ya ce hakan na cikin tsarin bayar da ilimi kyauta kuma tilas ga al'ummar jihar.