Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Al Hassan Abdoul-Azizi: An gurfanar da tsohon shugaban Hizba na Mali a gaban kotun ICC
A safiyar Talata ne Kotun Hukunta Manyan Laifukan ta Duniya, ICC, ta soma shari'ar babban mai tayar da kayar baya wanda ake zargi da aikata laifukan yaki a kasar Mali.
Al hassan Ag abdoul-Aziz ya kasance shugaban Hizbah na masu tayar da kayar baya masu ikirarin kishin Islama a Timbuktu, lokacin da birnin na arewacin Mali ke karkashin ikon kungiyoyin Ansar Eddine da Al-Qaed shekaru takwas da suka gabata.
Mutumin, mai shekaru 43, shi ne mai tayar da kayar baya na biyu da ke fuskantar shari'a a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya da ke Hague, game da mummunan yakin da aka yi a kasar.
Tuhume-tuhumen da mai gabatar da kara ta kotun ta gabatar a kansa, sun shafi laifukan yaƙi da cin zalin bil-Adama da ake zargin an aikata a kan farar hula a lokacin tashin hankalin masu tayar da kayar baya daga 2012 zuwa 2013.
A matsayinsa na shugaban rundunara Hisbah ta kungiyar masu tayar da kayar baya ta Ansar Eddine, Al Hassan Abdoul-Azizi, na fuskantar zarge-zargen hannu a laifukan azabtarwa, da fyade da kuma ajiye sa-ɗaka.
An dai yi wa mata da 'yan mata da dama auren dole ga 'yan bindiga masu tayar da kayar baya, wadanda a lokacin su ke iko da birnin Tambutu mai dimbin tarihi.
Ana kuma zarginsa da bayar da umarnin rugurguza dimbin hubbarai ko kusheyi na tarihi da kuma gine-gine na addinin Islama ciki har da masallatai.
Hukumomin Mali ne suka miƙa Al hassan Aboul Azizi ga kotun ta ICC da ke Hague a 2018 bayan kotun ta bayar da sammacin kama shi.
Kafin fara shari'a ta Abdoul-Aziz a yau, mutum guda tilo da aka taba gurfanarwa a gaban kotun hukunta manyan laifukan ta duniya, game da yakin na kasar Mali, shi ne Ahmad al-Faqi al-Mahdi, wanda ya amsa laifin lalata wuraren tarihi guda tara da kuma wani masallaci a Tambuktu.
A muhimmiyar shari'ar da aka yi masa a 2016, an yanke masa hukuncin daurin shekaru tara a jarun, bayan da ya ce ya yi nadama.
Su dai masu tayar da kayar bayan a shekarun baya sun kwace wasu yankuna na Mali ciki har da birnin Tambuktu a yunkurinsu na kifar da gwamnati da kuma sanya irin nasu salo na Shari'ar musulunci, kafin daga bisani dakarun gwamnatin kasar da taimakon kasashen waje suka fatattake su kana suka sake kwato yankunan su koma karkashin ikon gwamnati, yayin da yakin ya yi sanadiyyar barnata dimbin kayayyaki da wuraren tarihi masu daraja da kuma janyo hasarar rayukan bil-Adama.
A 2017 ya barnatar da wasu kayayyaki da darajarsu takai ra fam miliyan uku.