Rasha na kasaitaccen faretin tunawa da Yakin Duniya na Biyu

Red Square

Asalin hoton, Getty Images

Rasha na gudanar da wasu jerin fareti na sojojin kasar a yau Laraba - mako shida bayan da aka yi bikin zagayowar galabar da sojojin Soviet suka samu kan sojin Nazi na Jamus.

An jinkirta bikin zagayowar wannan ranar da aka fi sani da Victory Day ne saboda annobar korona, kuma ana gudanar da shi ne a yanzu duk da cewa Rasha na cikin kasashen da masu cutar suka fi yawa a duniya.

Sai dai ga Rashawa, wannan muhimmin biki ne saboda shi ne lokacin da suke tunawa da gagarumar sadaukar da rayukan da sojin kasar da fararen hula suka yi a yakin da suka lakaba wa sunan "Babban Yakin Kishin Kasa".

Dubban sojoji da tankokin yaki fiye da 250 ne za su yi wannan kasaitaccen faretin a dandalin Red Square domin tunawa da sadaukarwar da 'yan kasar suka yi - wanda shugaban kasar Vladmir Putin ya ayyana a matsayin mai tsarki.

Tsofaffin sojoji - wanda wasunsu na da shekaru 90 da wani abu - wadanda kuma aka killace su a wata cibiyar kula da masu cutar Covid-19 gabanin wannan bikin, za su yi maci tare da sauran sojin kasar domin tunawa da gagarumar hasarar rayuka na 'yan kasar ta Soviet suka yi kafin samun galaba kan sojin Nazi na Jamus.

Vintage T-34 tanks rehearsing in Moscow, 20 Jun 20

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Tsofaffin tankokin yaki samfurin T-34 a dandalin Red Square na Moscow

Amma Shugaban Rasha ya so ya gudanar da bikin da kasaitarsa ta zarce wannan.

Ya so ya gayyaci shugabannin kasashen duniya su halarci bikin a birnin Moscow ranar 9 ga watan Mayu, amma hakan bai samu ba saboda barkewar annobar korona.

Mako shida bayan ranar da aka shirya yin bikin, shugabannin kasashe kalilan ne za su halarci bikin.

Har yanzu ana samun dubban masu kamuwa da kwayar cutar korona a kowace rana, amma jami'an gwamnatin kasar na cewa an sha karfin annobar - wasu ma na cewa an gama da ita gaba daya.

Sai dai duk da wannan yawancin 'yan kasar za su kalli wannan faretin ne daga gida ta akwatin talabijin.