Sharaɗi 24 da aka shata wa Masallatan Abuja

Hukumomin Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya sun shata wa masallatai wasu sharuɗɗa da ake buƙatar su kiyaye kafin taruwar mutane domin ibada.

A ranar Litinin ne gwamnatin Najeriya ta ɗage haramcin tarukan ibada bayan rufe masallatai da coci-coci domin daƙile yaɗuwar cutar korona.

Sai dai duk da sanarwar buɗe wuraren ibada da gwamnatin ƙasar ta yi abubuwa ba su daidaita ba saboda sabbin matakan da hukumomi suka shata kafin buɗe wuraren ibadar.

A babban masallacin kasa da ke Abuja hukumomi masallacin sun shaida wa BBC cewa sai nan gaba ne za a dowa da harkokin ibada. Haka ma a wasu masallatan da aka buɗe a birnin Abuja an shata wasu matakan kayyade taruwar mutane.

Daga cikin sharuɗɗan da aka shata sun haɗa da buɗe masallaci minti 20 kafin fara sallah sannan kuma a rufe bayan minti 20 da gudanar da sallah.

Amma a lokacin Magariba da Sallar Isha za a buɗe minti 10 kafin sallar Magariba sannan a rufe minti 10 bayan Sallar Isha'i. Kuma ana son a bayar da tazara ga mutanen da za su jira Sallar Isha'i bayan Magariba.

Sannan adadin lokacin da aka ƙayyade na gudanar da Sallar Juma'a da huɗuba duka kada ya wuce awa ɗaya. Haka kuma ba a yadda a gudanar da Salloli ba baya ga Salloli biyar na farilla da Sallar Juma'a.

Haka kuma akwai rukunin waɗanda aka haramta wa zuwa masallaci da suka haɗa da waɗanda shekarunsu suka haura 65 da kuma masu fama da cututtuka kamar tarin fuka da cutar SIDA ko HIV da kuma cuwon suga.

Sauran sharuɗɗan sun haɗa da:

  • Amfani da takunkumi ga duk wanda zai shiga masallaci
  • Tsabtace masallaci kafin gudanar da ko wace Sallah musamman amfani da sinadari domin goge kafet
  • An buƙaci masallatai su samar da na'urar da ke auna zafin jiki da kuma samar da abin wanke hannu kafin shiga masallaci da kuma makewayi ga dukkanin masallata da kuma dukkanin masu kula da masallaci
  • Lokacin kiran Sallah da Iƙama kada ya wuce minti 10
  • Ana son a bude ƙofa da tagogi a duk lokacin gudanar da Salloli biyar na farilla da kuma Sallar Juma'a
  • Ana kuma son duk wanda zai zo masallaci ya zo tare da dardumarsa ta Sallah. Sannan ana son a bayar da tazara akalla mita biyu tsakani a sahu
  • Yawan masu Sallah kada ya wuce kashi ɗaya bisa uku na yawan adadin mutanen da Masallacin ke ɗauka
  • Ba a son mutane su riƙa gaisawa da juna. Haka kuma ana son a dinga rubuta sunayen duk waɗanda suka shiga masallaci domin gudanar da salloli biyar na farilla
  • Makarantun Islamiyya za su ci gaba da kasancewa a rufe.