An bude masallacin Ƙudus bayan wata biyu

Asalin hoton, AFP
An sake bude masallacin Al Aqsa, wurin ibada na uku mafi tsarki ga musulmi da ke birnin Kudus bayan rufe shi tsawon wata biyu saboda annobar korona.
Daruruwa masu ibada ne suka rika ambaton 'Allahu akbar' yayin da babbar kofar koriya ta bude, lokacin da suke shiga harabar masallacin.
Daidai lokacin kuma sun rika sumbatar ginin. Musulmin na sanye da takunkumai kuma an bukaci su yi biyayya ga tsarin ba da rata.
Masallacin wanda ke yankin da Isra'ila ke iko da shi a gabashin Kudus, ya rufe kofofinsa a watan Maris a zaman wani bangare na matakan dakile yaduwar sabuwar cutar mai kisa.
Sake bude masallacin a Lahadin nan tamkar yayewar wani lokaci ne na kunci ga Musulman birnin Kudus, saboda a bana ba su iya yin ibada a lokacin watan azumin Ramadan ba, da kuma yin Idin Karamar Sallah ba tare da kai ziyarar da suka yi ba
Majalisar wakafi ta addinin Musulunci ta ba da ba hujjar kawo karshen sanya tarnaki ga masallata da kuma sake bude wurin ibadar sakamakon raguwar da aka samu ga adadin mutanen da ke kamuwa da annobar.
Kuma a kokarinta na ganin an takaita kasadar yada kwayar cutar, majalisar ta bullo da sabbin matakai, daidai lokacin da sabbin masu kamuwa da korona a Isra'ila ke kara hauhawa a 'yan kwanakin nan.
An dai bukaci masu ibada su rika zuwa masallacin da tabarminsu, matukar suna son yin sallah a cikin ginin ko kuma a farfajiyarsa..

Musulmai sun yi imani cewa daga wannan masallacin ne Annabi Muhammad (S.A.W) ya yi tafiyar nan mai cike da mu'ujiza ta Mi'iraji.
Haka nan kuma wuri ne mai tsarki ga al'ummar Yahudawa.
Karon farko tun tsakiyar watan Maris, da Musulman suka shaida kiran sallah a cikin masallacin kansa.
Annobar korona dai ta janyo tilasta manyan wuraren ibada na al'ummar Musulmi ciki har da Masallacin Ka'aba da takwaransa na Madina a Saudiyya.
Ma'aikatar Cikin Gidan Saudiyya ta ce za a buɗe dukkanin masallatai da ke wajen Makkah daga Lahadin nan 31 ga watan Mayu .
Lamarin ya zo ne sakamakon fara sassauta dokar kulle da Saudiyya ta ce za ta fara yi daga ranar 21 ga watan Yuni.
Sannan ta kuma sanar da cire dokar hana fita kwata-kwata a fadin kasar, bayan kusan wata biyu a yaƙin da take yi da annobar korona.
Sai dai sabon matakin na ɗage dokar a ko'ina bai shafi birnin Makkah ba.
Kasar ta shiga rana ta biyar da sanya dokar hana fita ta tsawon sa'a 24 domin hana bukukuwan Sallah.










