Pogba ya gana da limamin Masallacin Madina

Asalin hoton, Masjid Al Haram Makkah
Ɗan wasan kulob din Manchester United Paul Pogba ya gana da limamin masallacin Annabi (SAW) a birnin Madina, Sheikh Ali Bin Abdur Rahman Al Hudhaify, yayin da yake ci gaba da aikin Umara a kasar Saudiyya.
Sai dai ba a san abin da suka tattauna ba tukuna.
Pogba ya isa kasar ne a makon jiya don fara aikin Umarah a watan azumin Ramadan.
Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Instagram gabanin tafiyarsa Saudiyya, Pogba ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa birnin Makkah domin godewa Allah kan nasarar da suka samu a kakar bana.
Tun bayan isarsa Saudiyya ne hotunan dan wasan suka karade kafofin sadarwa a duniya, ciki har da wadanda ya dauka a gaban Harami da dai sauransu. Kuma sabanin yadda aka saba ganinsa, akwai alamun karin nutsuwa a tare da shi.
Rahotannin kafafen yada labarai sun ce Pogba, wanda dan kasar Faransa ne, yana yin ibadarsa ta addinin Musulunci.
Pogba ya koma United a bara daga Juventus a matsayin dan wasan da ya fi kowanne tsada a duniya.

Asalin hoton, Masjid Al Haram Makkah







