Tasirin annobar coronavirus kan shagalin sallah

    • Marubuci, Sani Aliyu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist

Sallar Eidi ita ce ibada ta farko da Musulmin duniya - su biliyan biyunsu kan gabatar a ranar Sallah, inda dubun dubatansu ke halartar sallar a masallatan da galibi a bayan gari suke.

Bayan wannan, Musulmi kan yi bukukuwan sallah na tsawon kwanaki biyu har zuwa mako guda a wasu sassa na duniya domin nuna farin cikinsu da wannan lokaci mai albarka da suka sami kansu a ciki.

A ƙarshen makon nan ne watan azumin Ramadan ya ƙare, kuma Musulmi a fadin duniya sun shiga bukukuwan sallar Eid ul Fitr.

Kamar yadda aka saba, Musulmi kan shirya yin shagulgulan sallah wandanda suka hada da cin abinci da ziyarar 'yan uwa da abokan arziki.

Sai dai a bana cutar korona ta saka ilahirin Musulmi cikin wani mawuyacin halin da basu taba samun kansu ciki ba.

Matakan da gwamnatoci suka dauka na hana fita da na samar da tazara a tsakanin jama'a za su ci karo da yadda addinin Musulunci ya bukaci mabiya su yi - musamman ziyarce-ziyarce domin sada zumunci da raba kyautuka da ma gudanar da wasanni na nishadi.

A wasu yankunan, Musulmi za su iya fita zuwa masallatai domin yin sallar Idin, amma a yawancin wurare, dokar hana fita ta tailasta musu yin sallar a gida tare da iyalansu.

Za a gudanar da bukukuwan sallah ta hanyoyin da suka sauwaka ne saboda wannan yanayin - iamma duk da haka, wasu za su dafa kayataccen abinci bayan sanya tufafin da suka dinka kamar yadda suka saba a shekarun da suka gabata.

Tasirin fasahar sadarwa ta zamani

Maimakon su fita yawon sallah, yawanci iyalai za su yi zamansu ne cikin gidajensu - amma za su yi amfani da hanyoyin sadarwa na zamani wajen sada zumunta da 'yan uwansu da kuma abokan arziki.

Yawanci za su yi amfani ne da manhajar WhatsApp da Facebook Messenger domin aikawa da sakonnin bidiyo da na sauti kai-tsaye ga wadanda suke son yin zumunci da su.

Akwai kuma wadanda za su kira 'yan uwan nasu ne ta waya domin sada zumuni.

Amma duk da halin da ake ciki, akwai wasu al'umomin da za su yi bikin sallah kamar yadda aka saba a da - domin hukumomin yankunan da suka sami kansu ba su aiwatar da dokar hana fita ba.

Wadannan mutanen a jihohi kamar Kogi da Cross River da ke tarayyar Najeriya da kuma wani yanki na jihar Yobe da Borno sun zama abin sha'awa ga sauran 'yan uwansu Musulmi saboda 'yancin walwalar da har yanzu suke da shi.

Amma ko wane hali Musulmi suka sami kansu, akwai abubuwa da ba za su sauya ba - wadanda suka hada da fitar da zakkar kono da raba abinci ga masu bukata, da yi wa juna addu'o'i na fatan alheri.

A wanna lokaci, Musulmi kan rika gaya wa 'yan uwansu "Barka da Sallah", ko "Eid Mubarak", ko kuma "Eid Sa'id", domin murnar zagayowar wanan rana.