'Yan Najeriyan da suka makale a filin jirgin saman Thailand na iya komawa gida

Asalin hoton, Special Affairs and Public Relations Suvarnabhumi
Mahukuntan kasar Thailand sun ce wasu 'yan Najeriya uku da suka kwashe tsawon wata biyu a filin jirgin saman Suvarnabhumi a babban birnin kasar, Bangkok, za su koma gida nan ba da jimawa ba.
Tun daga ƙarshen watan Maris aka killace mutanen a can saboda dokar hana zirga-zirga da aka kafa domin dakatar da yaɗuwar cutar korona.
Ofishin jakadancin Najeriya da ke Bangkok ya rika sa ido kan halin da mutanen ke ciki, in ji jaridar The Nigerian in Diaspora Bureau.
Ofishin jakadancin ya tura wani sako na godiya ga wani dan kasar Biritaniya da ke zaune a Thailand bayan da ya nuna damuwarsa kan halin da mutanen biyu ke ciki a shafinsa na Twitter, sakon da ya ja hankalin duniya.
Richard Barrow ya kuma yabawa jami'an da ke kula da filin jirgin saman na Thailand saboda yadda suka rika ba ciyar da mutanen, suka kuma ba su ruwan sha da wasu kayan masarufi yayin da suk killace a cikin filin jirgin saman.
Guda biyu daga cikin mutanen sun kasance kan hanyarsu ta zuwa Laos da matafiyi na uku shi kuma mai niyyar zuwa Myanmar - amma ba ɗayansu da ya isa inda ya nufa saboda an kulle iyakokin waɗannan ƙasashen.
Mutanen sun sami kansu a cikin wani mawuyacin hali na yadda ba za su iya shiga Thailand ba saboda ba su da takardun izinin shiga kasar wato biza.
Sun kuma sun kasa komawa Najeriya saboda gwamnati a can ta rufe filayen saukar jiragen saman kasar tun karshen watan Maris.











