Coronavirus: Najeriya ta haramta wa jami'anta tafiye-tafiye

Covid-19

Asalin hoton, Twitter/NCDC

Lokacin karatu: Minti 2

Yayin da aka samu mutum na uku da ya kamu da cutar numfashi ta coronavirus a Najeriya, gwamnatin kasar ta ce ta dauki wasu matakai na hana bazuwar cutar a kasar.

A ranar Talata ne hukumomin Najeriya suka sanar da samun mace ta farko da ta kamu da cutar tun bayan bullarta kasar ranar 28 ga watan Fabrairun 2020.

Gwamnatin ta ce ta dauki matakan ne bayan zaman farko da kwamitin yaki da cutar COVID-19 da kasar ta kafa, a wani matakin riga-kafi da nufin dakile bazuwar cutar da hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana ta a matsayin annoba ta duniya.

Sakataren gwamnatin kasar Boss Mustapha ne ya sanar da matakan jim kadan bayan kammala zaman kwamitin.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Ya ce matakin farko da kwamitin ya yanke shawarar dauka shi ne haramta wa jami'ai da ma'aikatan gwamnati tafiye-tafiye zuwa wasu kasashen waje.

"An kuma soke duk wasu tafiye-tafiye da aka tsara yin su a baya," in ji sakataren gwamnatin.

A cewarsa, bayan yin duba na tsanaki kan yadda cutar take bazuwa, kwamitin ya ba da shawarar tsaurara matakan gaggawa domin yaki da cutar.

"A yanzu muna da mutum uku da suka kamu - sakamakon gwajin da aka yi wa daya daga cikinsu ya nuna ba ya dauke da cutar daga bisani,"

"Ya zama wajibi a shawarci jami'an da ke aiki a ma'aikatu da hukumomin gwamnati kan matakin haramta duk wasu tafiye-tafiye ko don halartar taruka ko tattaunawa da bukukuwa," in ji shi.

"Wannan haramci zai ci gaba da aiki har sai baba-ta-gani," kamar yadda sakataren gwamnatin ya fada.

Ya kuma shawarci jama'a su soke tafiye-tafiyen kasuwanci ko na zuwa hutu idan ba ya zama dole ba domin kare kawunansu musamman zuwa kasashen da cutar ta covid-19 ta fi kamari.

Sannan ya bukaci matafiyan da suka shiga kasar daga ketare su killace kansu na tsawon kwana 14 a gidajensu.

"Hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasar ta fitar da jerin wasu ka'idojin kebe kai" wanda ya ce za a yada su don wayar da kan jama'a game da yadda za su killace kawunansu.

Boss Mustapha ya kuma ce hukumomin lafiya za su rika sa ido kan mutanen da suka shiga kasar daga kasashen da ke da yawan mutane masu fama da cutar har tsawon mako biyu.

Ya kuma ce Najeriya ta goyi bayan matakan da wasu kasashen suka dauka na hana tafiye-tafiye.

Sakataren gwamnatin ya kuma yi kira ga 'yan kasar su mayar da hankali kan tsaftar jiki da ta muhallansu kamar yadda hukumomin lafiya ke ba da shawara.

Ya ce akwai bukatar mutane su rika yin nesa-nesa da juna don kare kansu daga yiwuwar daukar cutar.