Zan cire wa 'yan Bauchi kitse daga wuta - Kauran Bauchi

Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya lashi takobin yin aiki tukuru domin tabbatar da muradin wadanda suka zabe shi a matsayin gwamna.

Gwamnan ya shaida wa BBC hakan ne a wata hira a ranar Litinin bayan da Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya samu nasara a zaben gwamnan jihar da ya gabata.

Hakan ya faru ne bayan karar da daya daga cikin 'yan takarar da suka shiga zaben wato Muhammad Abdullahi Abubakar, tsohon gwamnan jihar ya shigar yana zargin tafka magudi.

Sai dai dukkanin alkalan sun yi watsi da karar, tare da tabbatar da Kauran Bauchi Bala Muhammad.

Da yake magana da BBC jim kadan bayan kammala shari'ar, Gwamna Bala ya ce wannan nasara ce ta al'ummar Bauchi ba wai tasa shi kadai ba.

'''Zan tabbatar da cewa na cika wa mutanen Bauchi muradinsu, zan cire musu kitse daga wuta'', in ji gwamnan.

A kan zaben gwamnan Filato ma dai Kotun Kolin ta yi hukunci, inda ta tabbatar da zaben da aka yi wa Gwamna Simon Bako Lalon na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

Dan takarar jam'iyyar PDP Jeremiah Useni ne ya shigar da karar, shi ma yana zargin cewa an yi magudi a zaben, sai dai hujjojin da ya gabatar wa kotun sun gaza gamsar da ita akan ikirarin nasa.

A hirarsa da BBC jim kadan bayan bayan bayyana shi a matsayin wanda ya samu nasara, gwamnan ya bukaci dukkanin abokan hamayyarsa da hukuncin bai musu dadi ba, su zo a hada hannu a yi tafiya tare domin ciyar da jihar gaba.