EFCC ta rufe jaridar The Sun saboda satar N7.65 biliyan

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta rufe gidan jaridar The Sun.

Kamfanin na daga cikin kadarorin tsohon gwamnan jihar Abia Sanata Orji Uzo Kalu da kotu ta yanke wa hukuncin daurin shekara 12 saboda zambar naira biliyan 7.65.

Kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren ya ce rufe gidan jaridar ya biyo bayan umurnin babbar kotun da ke zamanta a Legas, cewa a rufe dukkan kadarorin da tsohon gwamnan ya mallaka sannan a mika su ga gwamantin kasar.

A sanarwar da hukumar ta fitar, Wilson Uwujaren ya ce EFCC na sanya alama tare da rufe kadarorin tsohon gwamnan ne domin kauce wa karkatar da su.

Kamfanin Slok Nigeria Ltd na daga cikin kadarorin Orji Kalu da EFCC ta sanya wa alama ta kuma rufe.

A zaman kotun na ranar 5 ga watan Disamban nan da muke ciki, mai shari'a Muhammed Idris ya ce EFCC ta gamsar da kotun da kwararan hujjoji cewa wadanda ake karar sun aikata laifin.

Bayan tsohon gwamnan, sauran wadanda EFCC ta yi karar sun hada da kamfaninsa Slok Nigeria Ltd da kuma darektansa na kudi Udeh Udeogu bisa zarginsu da karkatar da naira biliyan 7.65.

Bayan yanke wa Orji Uzo Kalu hukuncin daurin shekara 12 a gidan kaso, kotun ta yanke wa Udeh daurin shekara 3.