Ambaliyar ruwa ta shafi mutum 273,000 a Somalia

Sama da mutane 273,000 ne suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa a kasar Somalia, wasu dubbai da ke zaune a yankin Baladweeyne inda lamarin ya fi kamari na rayuwa karkashin bishiyoyi ko tantunan da aka kafa na wucin gadi bayan ruwa ya shafe gidajensu.
Hukumar 'yan gudun hijira ta Norway ta yi kiran a kawo wa mutanen daukin gaggawa, wadanda ke cikin tsananin bukatar taimako.
Victor Moses shi ne shugaban hukumar a kasar Somalia, ya shaidawa manema labarai cewa ambaliyar ruwan ta shanye sama da kashi uku na yankin Baladweeyne, tare da wasu kauyuka makofta.
Kuma yankunan su ne inda marasa galihu suka fi rayuwa a ciki, a halin da ake ciki babu wutar lantarki, babu ruwan sha mai tsafta.
Amfanin gona sun lalace, ya yin da ruwan ya yi awon gaba da dabbobin da al'umar yankunan suka dogara da su.
Moses ya kara da cewa akalla akwai iyalai 30,000 da suka rasa matsugunansu a garin Bardaale a kudancin Somalia.
Ita ma hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dikin Duniya ta tabbatar da adadin mutanen da ambaliyar ta shafa kamar yadda takwararta ta Norway ta tabbatar, kuma dukkan adadin na watan da ya gabata ne.
UNHCR ta ce a wannan shekarar kasar Somalia ta sha fama da bala'i iri-iri ciki har da mummunan Farin da ya afka wasu sansanonin, baya ga tashe-tashen hankulan da rikicin kabilanci ke haddasawa, dan haka suke bukatar matsuguni, kayan abinci, barguna, ruwan sha da gidan sauro da bandaki da kuma magani.
Masu hasashen yanayi dai sun ce cikin watannan za a ci gaba da tafka ruwa kamar da bakin kwarya, ya yin da kogin Shabelle da Juba ke ci gaba da tumbatsa.
A bangare guda kuma Puntland da Somaliland za su fuskaci mahaukaciyar guguwa nan da kwanaki uku masu zuwa.











