Harshen Kiswahili na kara samun daukaka

A kasar Tanzaniya, za a fara shirya jarabawa ta musamman kan yaren Kiswahili, wanda ake amfani da shi a sassan nahiyar Afirka masu yawa.

Jami'ar Dar es Salaam ce za ta rika shirya jarabawar, kuma ta ce za ta tsara ta ne kamar yadda ake gudanar da na harsunan turancin Ingilishi da Sfaniyanci da Larabci da sauran manyan harsunan duniya.

Masana sun amince cewa Tanzaniya ce kasar da aka fi amfani da harshen a matakin da ya kamata a fadin Afirka.

Idan ka ziyarci wuraren shakatawa ko kasuwanni a yankin Afirka ta gabas, akwai wani yaren da tabbas za ka yi kicibis da shi mai suna Kiswahili.

Za ka kuma taras da masu amfani da shi a tsakiyar Afirka har ma da kudancin ta, tun daga Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo zuwa Mozambique, daga kuma Zambia zuwa Rwanda.

Ya kasance harshe na biyu ga yawancin masu amfani da shi, inda ga wasu kuma, shi ne harshe daya tilo da suka sani.

Shirya wannan jarabawa alama ce da ke nuna yawan farin jini da habakar da harshen ke yi a nahiyar Afirka -- kuma wata hanya ce ta inganta shi da kare shi daga gurbacewa.

Kungiyar raya kasashen kudancin Afirka ta bayyana yaren na Swahili a matsayin na hudu a jerin harsunan da za a rika amfani da su a hukumance.

Kuma kasar Afirka ta Kudu na daf da fara koyar da Kiswahili a makarantun kasar daga shekara mai zuwa.