Kotun Tanzania ta hana aurar da kananan mata

A baya ana aurar da kafin su kai shekara 15

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kotun ta zartar da hukuncin aurar da 'yan mata idan suka kai shekara 18

Babbar kotu a kasar Tanzania ta haramtawa iyaye aurar da 'yan mata 'yan kasa da shekara 15.

Kotun koli ce ta sake nazari kan hukuncin da wata kotu ta yanke da ya baiwa iyaye damar da aurar da kananan mata yara.

Kotun kolin ta ce aurar da 'yan matan kasa da shekara 15 na yin tarnaki da take hakkinsu sannan ya ci karo da kundin tsarin mulkin Tanzania da ya haramta hakan.

Babban mai shigar da kara na gwamnati ne ya sauya hukuncin da aka yanke a shekarar 2017, wanda wani banagre na dokokin aure ya aminta da aikata hakan.

A yanzu kotun kolin ta zartar da hukuncin dole iyaye su jira har sai yarinya ta kai shekara 18 kafin a aurar da ita.

Haka zalika su ma maza sai sun kai wadannan shekarun. Wannan hukunci dai gagarumar nasara ce ga masu rajin kare hakkin 'yan mata a Tanzania.

Wani bincike da susun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar, ya gano kashi 31 cikin 100 na 'ya'ya mata a Tanzania ana aurar da su kafin su kai shekara 18, yayin da kashi 5 cikin 100 kuma ake aurar da su kafin su kai shekara 15 a duniya.