Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shugaba Alpha Conde na son yin tazarce
'Yan adawa a Guinea na karawa da jami'an tsaro domin nuna rashin amincewarsu da yunkurin Shugaba Alpha Conde na tsawaita mulkinsa a karo na uku.
Ma'aikatan lafiya a Guinea sun ce an kashe a kalla mutum biyu yayin wata zanga-zanga da 'yan kasar ke yi domin nuna rashin amincewarsu da shirin Shugaban kasar Alpha Conde na neman tsawaita mulkinsa a karo na uku.
Wasu rahotanni kuma na cewa wasu mutanen sun sami raunuka.
Jami'an tsaron kasar ta Guinea sun yi amfani da harsasai na gaske da gurnati mai gigitawa da kumahayaki mai sa hawaye a kokarin da suke yi na kawar da masu zanga-zangar.
Sun dai kafa shingaye kuma sun rika kona tayoyi a yayin da suka rika jifan jami'an tsaro da duwatsu.
An kulle makarantu da kantuna a babban birnin kasar, kuma an ga wasu jami'an 'yan sanda sun zagaye gidajen wasu jagororin 'yan adawa.
An kuma sami rahotannin da suka tabbatar da ana tsare da wasu shugabannin 'yan adawa, wadanda tun gabanin zanga-zangar aka kama su.
Wa'adin mulkin Shugaba Alpha Conde na biyu kuma na karshe a karkashin tsarin mulkin kasar zai kare a shekara mai zuwa, amma da alama zai so ya yi tazarce.
Ya sha bayyana aniyarsa ta neman amincewar al'umomin kasar ta hanyar shirya zaben raba gardama. Kuma a watan jiya ya bukaci jami'an gwamnatinsa da su duba yiwuwar samar da wani sabon tsarin mulki domin ya cimma burinsa.